DA AURENA page 63__64

734 36 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Godiya ga kainuwa writer's Associaton musamman Auntynmu Fauzah 👏🏻👏🏻👏🏻*

Page 63 64



Sosai da sosai komi ya cabema Baban Huwailat ga yawan mafarkanta yanayi akai akai cikin wani yanayi abunfa ya fara damunsa .
Gashi goronma yanzu bai ja komi ya zama da kyal ake samunsa a gidan.
Yau ya yanke shawaran zuwa gun Amadu yasamo koda 1k ce dan tun safe yake hakilo amma ba wani bayani.

Cikin tunanin yau kuma mizai faru ya isa gidan Amadu dan baida yanda zaiyi sannan yasan abun arzikin da yaima Amadu baici ya yadasaba .

Yaro ya aika yai masa sallama da mai gidan .

Ba'a jimaba yaron ya dawo ,,ance yana zuwa , yauwa na gode yaro.

Sai kau ga Amadu ya fito yana ganin Baban Huwailat ransa ya baci ya juya zai koma sai yaga yakamata yau ayita ta kare tsakaninsu da tsohon nan.
Ahankali yadawo

,,Bawan Allah ko nace Abdullahi saurareni kaji da kyau yau zan fadama gaskiyar abunda baka saniba .....tun daga cacar bakinsa sa Abokinsa zuwa yau ba abunda bai fada masaba .
Ya kwashe da dariya gaskiya karamai kwanya gareka sosaima sannan baka da tunani dan nibazan iyama Diyata abunda kaima takaba ahakan wai ita kadaice gareka mace ko ? Oh ashefa yanzu Usaina natasowa ko?
Allah yasa kada kaimata na yar uwarta inada tabbacin yanzu ta zama cikakkiyar karuwa duk inda take gaskiya na tayaka murna .
Magana ta karshe karka sake nuna kasanni nidakai kowa tasa ta fishshesa ya ja gidansa ya rufe garam.

Juwa juwa ya dinga gani kansa na sarawa hawaye na zuba daga idanuwansa fuskansa na hasko yanda yadinga yima diyar cikinsa da kansa akan bare Wanda bai hada komi dashiba yanzu dawane ido zai dubi yarinyar idan tadawo ?

Ganin tunani ba abunda zai masa yasa ya nufi gidan da kyal.

Tun daga nesa ya hango kofar gidan cike da mutane tamkar ana wani abu gidan.

Cikin dan sassarfa ya idasa kofar gidan sai dai ba dan an taresaba kadan ya hana ya zube kasa.

Abba ne kwance male male cikin jini ba alamar numfashi atare dashi mutane sun kewayesa sunata salati.

,,sai dai kai hakuri Alh taho mugama sukai da motar Dangode babban nan mai motar ko juyowa baiba ya wuce abunsa .

Wani dan Dattijo ke wannan labarin.
Cikin kaduwa Baba ya samu da kyal ya isa gun Abban ya tabasa yaji yana motsi ya sauke ajiyar zuciya ,,kutaimakamun nakaisa asibiti ,
Wani mai mota aka tsaida ya kwashesu zuwa jenaral hospital samaru .

Sai dai likitoci sun bukaci 20k dan masa aiki a cikinsa da kafarsa da kana ganin kashin ta fili .

Zufa ta wanke Baba duk yau baici komiba amma ake tambayar 20k ?

Alfarma ya nema gun likitocin zaije gida ya dawo.

Tafe yake yana nadamar abubuwa da dama dasuka faru a rayuwarsa .

Yana shiga ya iske Mamansu itama tanata kuka anfada mata abunda yafaru da Abban.
Cikin sanyin jiki ya nemi wuri ya zauna ya rabka tagumi yakasa fada mata komi.

,,shikenan shima na rasashi ko?

,,Allah kayafemun abunda na aikata dakake jarabtarmu ta ko ina,

,,kiyi hakuri bai mutu ba amma banda kudaden da suka nema can asibitin.

,,Alh. har nawa suke bukata ?

,, 20k

,,innalillahi mukam ina zamu samesu Alh.

,,ko zakaje gun Amadu ne nasan zai taimaka,
Wani matsiyacin kuka Baba yasaki.

,,Zahara'u Amadu ya cucemu yaci amanarmu .........tas yakwashe labarin da Amadu ya fada masa ya fadamata.

Abunda bai saniba ta jima da sumewa agun ba numfashi.

Sai da yaji shirun tayi yawa ya dago kansa ya ganta kanta ya langabe miyau na fita ta gefen bakinta.

Sosai Baba ya kidime ya rasa mima zai mata .

Malam ne ya shigo a rude anfada masa yayansa motar Dangote tabi ta kansa.

Kwalalo idanuwa yai ganin Baba na dafe da gefen zuciyarsa yana shirin zubewa .
Da gudu ya taresa ,, Baba miya sameka ina yah Abban yake ?
Da hannu Baba ya nuna masa Mamansa dake mawuyacin hali .
Shinfidar da Baban yai ya nufi gunta.

Mama miya sameki ?
Pls mama karki barmu .

Mama kam tayi nisa batasan duniyar datakeba .
Da gudu ya ciccibeta yanufi waje ya tsaida mai mota suka nufi hospital da ita.

Tunda yabarsa sukadan dudduba wajaje masu sauki suka barsa nan sai ankawo kudin da suka bukata .

Cikin hanzari aka bata gado akai yan gwaje gwaje Dr ya tabbatarma da Malam tasamu shanyewar rabin jiki .

Kasa kuka yai sai zafi da kuna da zuciyarsa ke masa kawai.

Kamar daga sama yaji wani Dr nafadan ankawo mutum a mawuyacin hali anbar masu to maza a fito dashi inba a kawo kudinba.
Daram gabansa ya fadi badai yah Abba ake magana kansaba😱
Cikin hanzari ya fice yabi bayan wadanda zasu fitarda mai jinyar dan ganin waye.

Cikin tashin hankali ya ruga gun  Dan'uwnsa
,,pls my brother karka tafi muna tare.

Wani dogon numfashi yaja ya bude idanunsa sai dai dole ya rufe dan kansa ke sarawa sosai.

Daki guda ya nemi alfarmai hadasu ya tafi gida ya dawo.













*ADAMAWA*

,,Yanzu nan Dannan bazakaje samarun Nagano halinda Auta yake cikiba ,
Da kanka kace kagansa a yanayi marai kyau anya kuwa ?
Wata kamulallai tsohuwa kenan data  saka Babban Danta kan maganar Autanta .

Nace yakamata Nagano mana suwaye ko🤷🏻‍♀

Ina dubawa naga Mahaifiyar Baban Huwailat da Yayansa.

,,kiyi hakuri Dada insha Allah komi zai dai daita tun randa mustapha yazo mana da labarinsa naduba naga Huwailat bata tare dasu hakan yasa nake dakon bayyanarta dan nayi mata kiranye tana dab da bayyana saimu je baki daya can gunsu.






Yau ba abunda zai hanasa zuwa sokoto dan sanin laifin da yaima pretty Sam ta toshe duk wata hanyar aduwarsu to zaije ya fasa kwan kowa yaji yagaji da azabtuwa da kaunarta .

Yaya kenan 🤷🏻‍♀

Wazai agazama su mama🤷🏻‍♀

Ina yah Suleiman🤷🏻‍♀

Ya fansar Huwailat kan uncle 🤷🏻‍♀

Daddy zai hakura kuwa🤷🏻‍♀

Muhadu page na gaba

Taku Haupha

Ngd

DA AURENAWhere stories live. Discover now