DA AURENA page 87__88

710 29 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452






*Jaje da ban hakuri ga team din Amadu and Inna, nikaina banji dadin abunba mustapha yai ramuwar gayya da yawa hakora hudu babu 🥵🥵🥵*


Page 87 88




Hafsat ta yunkura da kyal ta tashi daga gun cikin matukar tsoro ta kalli yarinyar daketa numfashi sama sama tana neman dauki hannuwanta ta mika da nufin daukar yarinyar wani ihu ta saki ganin yanda hannunta ya koma na dama abun ba kyan gani .
,,oh ni Hafsat mizan gani haka kuma ?

Taita kukanta ita kadai bamai lallashi karshe ta samu da kyal ta dauki yarinyai ta nufi gudansu uwarta inta son 'yarta ta ansa kowa ta kansa yake gidan yanzu.

Hartaje sukai mata rashin mutunci  iyakar iyawarsu hardasu kashedin idan yarinyar ta mutu zasu kaita kotu .

Yau dai Hafsat ba masifa ba tujara dan haka baki alaikum ta fito ta nufi gidan malam Gardi dan yaga abunda yasameta .

Sai dai tana zuwa ta  iske shi matarsa zaune da mafeci tanata fiffita mai  kafafunsa zuwa kugunsa da sukai wani uban kumburi hatta da bagansa ya koma runtumeme sai ihu yake wai kuda nasha masa jini .
Cikin kuka Hafsat ta tsugunna ta tallafe hannunta da yaqara lakumewa tasaka kuka .

Matar ta dubeta ko shakka babu itace 'yar banzar da kullum saitaji ihunta da Gardi a shagonsa kilama ita ta goga masa wannan cuta .

Batare da gama tunanin abubuwan da suka faruba ta diraima Hafsat da duka sai da ta tabbatar da jikinta ko ina ya dauki service sannan ta hankadata waje .

Yara suka yayyabeta sunata ihu ihu


Uncle daya je gidansu Huwailat yaga Abun mamaki sosai .

Gidan ansakesa hardasu Get aka saka mai kyau dan madaidaici ga sabon fenti ya ce kilan Yah Abba ya gyara masu gidan dan haka ya kutsa kansa cikin matukar farin ciki ko banza pretty zata dawo ta iske gidansu ya sake .

Sallama biyu yai yaji muryai wata mace ta ansa dan haka ya gyara tsayuwarsa yana jiran ta fito .

Kallon kallo sukaima juna tabbas wannan kanin Amadune shege dan iska inji Zainab a ranta .

Wannan itace masifaffiyar kawai pretty ko dai ta dawo da gasken ?

Kallon hadarin kaji zainab tai masa ,,lafiya daiko ?
Yake yadanyi ,,dama gun masu gidan nazo .

Dariya zainab tayi sosai mai gidan dai ko ? Dan yanzu gidan mutum dayace dashi kunsan yanda kuka shiga kuka fita kuka korata duniya .

Tunda tafara magana kansa ya shiga duhu bayani yake bukata mai kyau .

Zainab ganin uncle na mata kallon rashin ganewa ta buga uban tsaki tace .

,,tsinannen Yayanka bai saurarama Huwailat da Ahalintaba sai da ya tabbatar yarabasu dakomi ciki harda gidannan , to da yake Allah yanasan kawata sai yabata ikon mallakai gidan batare datama saniba .

,,zainab bansan abunda yafaruba kinsan tunda Brother ya saki Huwailat tazo Babansu ya koreta taje gun kaka itama ta koreta na dauketa na kaita sokoto gun mahaifiyata , ya fayyace mata duk abunda ya faru .

DA AURENAजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें