DA AURENA page 95__96

1.6K 66 13
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452

*Kardai kugaji da mun addu'a masoyana still dai muran taki barina sosai ta kanainayeni ta hanani sukuni kuma shaidane dan duk yau baku ganni kojin motsinaba to addu'anku nake bara pls my friends 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻*

Page 95 96

Basu bata lokaci ba da zuwansu suka isa gidan kakanninsu Wanda mustapha yasa major binsa da kyal danshiba jikinsa nabasa ba banzaba Captain yai masa haka ba akanme zai yanke duk wata alaka ta tsakaninsu ?
Asaninsa baima Captain komiba koko dan ya gaza tsayawa ai neman princess din tasa yasakashi fushi ?
Idankau hakane uzuri yakamata yai masa dan nashi case din yaci uban nashi yasamu dama taya zai bari ta subuce masa ?

Yanata sakawa da kwancewa har suka kofar gidan .
Mustapha yai masa jagora suka shiga har dakin Kaka .

Kwance take tana duba wasu papers hankalinta gaba daya na Kansu .
Kallo daya bazaka iya gane Huwailat bace kai tsaye dan ta kile ta waye ta zama isasshiyar mace tamkar tazo ziyara daga wata kasa .

Tana sanye cikin riga da wando masu dan kauri kasancewar anfara sanyi rigar tana tare da hulaita dan haka itace kawai ta jawo ta rufe kanta da yasha kitso miri miri ya zubo har gadon bayanta agaban rigar an rubuta Beauty da manyan haruffa .

Wani mugun faduwa taji gabanta yayi wanda bata san akan me ya fadinba .

Shima Major gani nayi ya dan dafe kirjinsa da yai wata muguwar bugawa .

Nace to fa nawa idone 🤥

Yah mustapha da yashigo da shegantakar da yasabama Kaka yai suman tsaye 'yar maganai ta makale a bakinsa taki ida futowa .

Huwailat dake dafe da kirginta ta kyalla ido taga yah mustapha ai da gudu ta watsar da takardun ta ruga da nufin kalalkalesa .

Shikuma ya juya baki cike da murna ya nunama major ita dan haka tana fadawa sai tafada kan kirjin major wanda kejin bugun zuciyarsa ya kara hauhawa .

Kawai jiyayi wani tattausan jiki ya fada masa dagowar da zai yai arba da Hunar sa .

Wayyo soyayyah😍😍😍

Kara rumgumeta yayi sosai kamar zata kwace ta ruga .

Cikin kuka tace ,,yah mustapha inaka tafi ka manta dani nashiga wahala da kangi bayan tafiyarka yah mustapha kadan ya hana su Yah Abba da Baba harma da Mama su kasheni .
Yah mustapha naga tsantsar kiyayyai Ahalina yanda ko a labari bantaba ganin kojin wanda ya gantaba .

Kara rumgumesa tayi tana fitar da sautin kukanta da yakeji tamkar dalma ko yunbun wuta a zuciyarsa .

Baki hangame yah mustapha ke kallon major da hawaye keta zuba a idonsa tamkar fanfo ,lallai ya aminta major ba karamin so yakema Huwailat ba yau idan ana neman sheda to shine nafarko gun bada shedar .

Ganin sunyi lub a jikin juna sunata a jiyar zuciya shikuma major yadage sai shafa kanta yake da tuni fulan ta zame yah mustapha yai gyaran murya .

Ahankali ta dago dan ganin halinda yah mustapha yake .

Ido hudu tayi da Suleiman .

Runtse idonta tayi ta bude amma ba karya bane rungume take ale ale jikin mutumin data jima da tsana a rayuwarta .

DA AURENAWhere stories live. Discover now