DA AURENA page 30__31

689 39 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452

Page 30 31

Cikin zubar hawaye nace Amadu kaji tsoron Allah ka guji haduwarka da Allah ka cuceni ka zalinceni da yawa saida ka rabani da kowa nawa sannan zaka sakeni .
To yanzu ina zan nufa gabanka iyayena sukace idan  kasakeni ba dai gidansuba.
Saboda tsabar mugunta kahanani zuwa kiran kakana yana cikin ciwo yazo ya mutu kahanani zuwa gaisuwa muna cikin gari daya yanzu idannaje mizan fada su yarda banda laifi ?

Sosai yasaka dariya wallahi farin ciki sosai nayi da mutuwar tsohonnan saboda naga shine kawai keban ciwon kai game da burina da ke Huwailat.

Barima kiji wani abu to randa ya aiko kiranki na hanaki zuwa ninaje na iske gidan cike da danginku .
Na marairaice sosai nakama share hawayen karya .
Sanin shi yasan koni wanene yasa ban nufi gunsaba saina zauna gun matansa da yaransa nace ,,kuyi hakuri ba laifina bane nayi nayi da Huwailat tazo kiran kaka ta kiya wai itama bata da isassar lafiya kowa yaji da nasa ciwon.
Kafin na ankara sun saka salati daman abunda mukeji iyayenta da yayyenta nafada gaskiyane ashe.
Amma duk rashin mutuncinta baikamata taima Alhajiba inji kishiyar kakarki Dan koda yaushe bakinsa nakanta ashe baici ta damu dashiba kodan yanda yake sonta da tattashinta ?

Nace kuma dai kungani bansan inda Huwailat tasamo wannan bakin haliba .
Karaf Kakarki tace sai dai can ga dangin ubanki sukam kowa yasan lafiya garesu.

Natakaita maki labari kullum sainaje da yan kayan dubiyata nabasu nakara basu hakuri kan halinki daga karshe sukebanma hakurin .

Kuka sosai nafasa kagama dani amma wata ran kaima zaka girbi abunda ka shuka time din bana kusa ko ina kusa batakai nakeba nabarka lafiya nida kai duk Wanda ya cuci wani Allah zai saka masa.

Daga hakan na shiga hada yan kayana na fara tattara manyan ya kece da dariya ,,kina nufin da wasu kaya zaki fita a nan gidan Huwailat ?

Ai idankinga kinga kin debi kayannan iyayenkine suka zoda kansu dansu suka bansu . su kuma yanzu ta haramai aurena suke Dan Tsohonki ya biyamun sadaki tsohuwarki taban kwasar adashenta nakara a lefe wadannan kuma nasa innnata taima dillaliya magana zata zo ta siyesu nakara kinsan ba wasu kudine daniba sosai .
Kollonsa kawai nake lallai Amadu wuyanka ya isa yanka malaminka ya iya aiki amma kasani nima kamar dan uwanah nake ( Mustapha) bana mantuwa bana yafiya zan jira ranai da zan dau fansar abunda kaimun .

,,Amma dai kin tabu ko ? To ATM din da yabaki nina daukesa danaga bai turo maki pin dinba nasaka shege masai .

,,Kinata kara batamun lokaci sabuwar jawara 😁

Cikin bacin rai na dauki yar jaka nasaka kaya kala biyar danba amfanin daukarsu .

Tashin hankalina banga takardunaba nai iyakar dubawata bangansuba na daure nakoma gun Amadu dake waya da Amaryaisa .
Dan Allah kokaga takarduna bangansuba ne .

Kallon ke kika sani yaimun yaci gaba da wayansa.

Kallon karshe naima gidan Amadu nafito nanufi hangar gidanmu gabana nafaduwa sosai bansan abunda zan iskeba .

To yakenan zasu kuwa ansheta hannu biyu koko koraita zasuyi🤷🏻‍♀
Tana iya zuwa gidan kaka kuwa 🤷🏻‍♀
Kubiyo Haupha danjin ya labarin Sulaiman da Mustapha ?

Godiya mai yawa gareku Kawayena na kusa da nesa

DA AURENAजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें