DA AURENA page 71__72

731 36 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452





'''Wannan page kyautane ko ince sadaukarwane gareki Diyata
Aisha Humaira Muhammad sirajo Alaramma Zaria
Allah ya raya mana ke bisa turbai gaskiya da Amanah'''

Page 71 72

Da gudu sojoji suka cika dakin dan ganin mike faruwa.
Mustapha da jikinsa ya gama sanyi kalau ya yarda da labarin da Huwailat ta bashi na asirin da Amadu yaima kaka da Suleiman din.

Cikin ruwan bala'i zalla yace ban labarin gaskiyar abunda ya faru .

Ahankali mustapha ya kai dubansa ga mutanen da suka cika dakin ya sadda kansa kasa bazai iya fadar sirrinsuba gaban mutane.

Wata uwar tsawa ya daka ,,ubanwa ya kiraku anan? Yabisu da idanuwansa da suka rine dan azabar bacin rai .
Sum sum suka bar dakin kafin ya sauke fushinsa kan mutum baiji bai ganiba .

,, Ina saurarenka ,

Ahankali mustapha yafara bashi labarin tun randa ya koma gida ya iske dukan da akema Huwailat da ita kanta Huwailat din labarin data bashi har zuwansu gidanta dashi yaima Amadu dukannan da yanda aka koresa saboda zugar Amadun .
Karshe yace .

Bayan dana tabbatar da idanna ki tafiya iyayena zasu tsinemu saina ba Huwailat ATM dina da full Address na Adamawa inda dangin mahaifinmu suke nafada mata wataran zai mata amfani .sai dai bayan dana bar garin nasamu hatsari Wanda nasan bacin raine danko gabana bana gani anan na rasa wayana Wanda ba karamin takaici nayiba danban rike number taba akainaba .sai dai yanzu a can Adamawa Yayan mahaifinmu yaban tabbacin Huwailat bata gida shine abunda yake damuna ina kanwata zataje bayan nasan wahala ko tsangwama bazasu taba sata ta guduba sai dai idan koraita sukai kamar yanda suka koreni .


,,ko shakka banayi naga Huwailat mustapha a sokoto sai dai ta nuna batama sanniba . yabashi labarin abunda yafaru gun siyen agogo .

,innalillahi wa inna ilaihirrajiun ,

Bamuda kowa a sokoto mizaikai Huwailat sokoto Sir?
Lallai sister na cikin gararanbar rayuwa .

Cikin tausan Kansu ya dafa kafadar Mustapha kai hakuri ai munkusa komawa muna komawa zamu dauki hutu mukoma gida mu tabbatar da gaskiyan lamari idan kuwa Amadu yasake Huna bata garin sai yazama abun kwatance kai makwabtansuma yaja masu dan ba abunda zaihanani cin ubansu.

Sosai mustapha yaji yasamu kwarin gwiwar tunkarai matsalai yar'uwarsa  ko shakka babu sai iyayensa dasu Yah Abba sun gane kurensu daya bayan daya .

Amadu kabani kaikam kowa Kaine target dinsa😱








Abban Huwailat ansamu gidan kuwa mai dan kyau ? Sonake a gyara matashi dan kaji abunda malam yace ta kusa bayyana sonake Huwai ta iske gidanta na kanta mallakinta hakan zai rage mata zafin koraita dasu Mama sukai .

,,Kwantar da hankalinki yaron yace ansamu gida mai kyau yanzu haka gyaransa akeyi ana gamawa zansa azuba mata kaya masu kyau da tsada fatana ta bayyana cikin koshin lafiya ,

,,Ameen amma Abban Huwailat inasan naje gida kodan naga tsarin da akaima gidan pls  ta marairaice fuska,

Karki damu kishirya sai muje tare . sosai tayi murna dan so take taje taga zaman Amadu da Hafsat tasan yanzu tafara girbai abunda ta shuka .

DA AURENAWhere stories live. Discover now