DA AURENA page 67__68

761 34 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452


Page 67 68


Sosai yah mustapha yai bankwana da dangin mahaifinsa da tabbacin yana dawowa zasu dunguma gida samaru Baki daya.




Tunda safe ya shirya tsab yana jiran sabbin sojojin da zasu zo suyi handle over dasu .

Takwas dai dai motor Army tai parking a kofar Barrack  dinsu .
Ya jima kwarai kafin ya fito daga cikin office dinsa har suka fara kulewa karma mustapha yaji labari ya tsani wulakancin manyan nan nasu haka kawai yake jin bazasu shirya da major dinnanba .
Bama da yaji da yawan kana nan sojoji na Murna da tafiyarsa sai ya kara aminta bazasu taba shiryawaba.

Bai ankara ba yaji abokansa sun sara banda shi daya tafi duniyar tunanin rainin hankalin major da girman kansa da bakar ketarsa da ake fada .

Tunda ya fito eyes dinsa suka sauka kan fuskan mustapha ya gane yaron ya sanshi amma ya gaza gane Inda yasan yaron gashi fuskan yaron naima fizga data Wanda yasani amma ya gaza gane waye a inanema.

Ganin kallon da yakema mustapha na kusa dashi sukaimai inkiya daya bada hakuri amma mustapha saima ya nuna ko a jikinsa.
Duk abunda suke major na ankare sai yaji yaron ya birgesa kwarai yasan gwarzon namiji da baida tsoro ko kadan.

Cikin izza da nuna shifa babbane ya nuna mustapha da yatsa .

,, who are u ?

Cikin dakewa mustapha ya ce ,, mustapha A Zaria sir,

Koda yaji ace dan wajajensune yaron .

Kara hada fuska yai waye captain dinku ?

Still Mustapha yace ,,yes sir ,

Dan tsura masa eyes yai yace fallow me .

Yashige office dinsa   ,

Sai da friends dinsa suka damesa da magana ya bisa office din amma daka gansa kasan ransa bace yake .

Da kyal ya sarama Major din yaita cika yana batsewa ,

Shikam zai taida wannan yaron dan yanason yaga karshen bakar zuciyarsa.

Sai da ya gama duk wasu abubuwa nasa ya tashi ya fice yasake ce masa follow me .

Kamar zai mutu yaji amma baida yanda zai haka ya daure ya bisa a baya.

,,major kace nazo da wuri but nazo sai da najiraka inama na biya gun princess dita mun bankwana,

Cikin daurewar face yace ,, yanzuma kana iya zuwa ai ,

Kallon direban motor kawai yai ya fito waje yana sorry sir ,

Makullin ya ansa ya mikama mustapha yace ,,less go .

Bakaranin tankwafar zuciyarsa yaiba daya rike keys din motor bai bari ya fadi kasaba.

Saboda tsabar zafin kai na mustapha ya gaza tambayar ina zai kaisu ya kama tuka motar kawai saida sauran motocin sojojin suka tashi harma biyu suka shiga gabansa sannan yaci gaba da binsu har Airport San nan sukai parking .
Koda sukai parking shikam bai motsaba balle susaka ran zan bude masu marfin motar.

DA AURENAWhere stories live. Discover now