Shimfiɗa.

384 9 0
                                    

  

Malam Sani shine mahaifin su sun kasance su uku a wurin Iyayen su, Mahaifiyarsu kuma Khadijah wacce suke kira da Inna, su kaɗai suka haifa wanda suka rene su cikin so da kaunar ƴaƴan su gami da tarbiyya mai kyau , asalin su ƴan Bauchi ne daga baya suka tashi suka dawo cikin garin Kano bayan wani miƙami da aka bawa Ahmad dake soja yace yana so kuma Mahaifinsu ya barshi dan a shi a rayuwar sa babu takura duk abinda mutum yace yana so to shi zai yi muddin tarbiyyar sa da kuma halayyar baza su ɓaci ba, Mahaifiyar su ce de da ƙyar ta yarda, Kabir  shi kuma kasuwanci ya riƙe na Mahaifinsu  sai  Adam wanda shine ƙarami a cikin su yana karantar harkar lafiya. Daga baya suka kuma dawowa Kaduna inda aka maido da Ahmad aiki cikin  jaji suka koma da zama shi dai Baban su badan yana so ba yake wannan tashin sai dai babu yadda ya iya tunda basu kama iyali ba har yanzu kowa aikin sa yake ƴan uwan sa dake Bauchi sun yi da su suyi auren nan amma suki suka ce shine yake ɗaure musu wurin zama.
Adam koda ya gama karatun sa sai be fara aiki ba anan Yayan sa Ahmad ya bashi shawarar ƙaro karatu acan ƙasar Turai ya kuma yarda shine ya biya masa komai ya tafi, ya tafi ba jimawa yayun sa sukayi aure Ahmad da Kabir inda aka basu auren a ƴan uwan su basu wani yi ja ba suka amsa cikin ƙankanin lokaci  akayi komai aka gama ganin gidan su na jajin kamar zai yi musu yasa sukayi shawarar siyan fili kawai su fara gini gashi Iyayen su na fara zancen komawar su Bauchi yarda suka saba zaman nan a kusa da su komawar su kamar zai yi musu wahala, babban ƙatan fili suka siya dan a lokacin har ana cewa yayi daji da yawa amma dake babu wani fili mai babba da zai ishe su yarda suke so dole sai nan ɗin gidajen a wurin ƴan tsararu da su haka de suka siya suka tada gini dake kowa alhamdulillah da kuɗi haka shima Kabir ɗin ya bada  gudunmawa mai tsoka a wurin ginin gidan duk shi kasuwanci sa yawancin a Kano da Bauchin yafi yawa sai baya wani zuwa wurin su sosai. Har ta Adam da baya nan sai da suka yi masa masa apartment ɗin gida ne sosai na gani na faɗa a wancan lokacin suka gina kuma ishashshe zai isa kowa koda nan gaba idan wani ya tashi yin wani auren dake fili kawai ƙatan gaske dan zai yi kusan gandu uku idan be fi bama.

Dawowar su gidan babu jimawa Aisha ta haihu (Matar Ahmad) inda ta haifi namiji aka sa masa Isma'il sunan mahaifinta inda suke ce masa Babba  babu jimawa itama Asiya ( matar Kabir) itama ta haifi na namiji suka yi ba baban su takwara aka sa masa Sani suna ce masa ƙarami. A lokacin Kabir ya fara shawarar fara gina Company ganin cewa kuɗi yana samuwa ta ko ina domin yana da yara a ta ko ina s inda yake kuma alhamdulillah basa cutar sa bare kuma su ci amanar sa.    Adam be dawo ba sai da ya zama cikakken likita kuma babban likitan ƙashi wato physiotherapy sannan ya dawo lokacin da ya dawo ya tarar duk ƴan uwan shi sunyi aure ba ƙaramin murna yayi ba dake kawai waya suke ta landline( lokacin ita ake yayi)  shima sai sun kirashi shi baya samun su idan ya kira, ƴan uwan shi suka gina masa asibiti babba musamman nashi duk da ya samu aiki a asibiti daban daban amma haka suka yi masa nashi duk da haka amma yana zuwa kowanne asibiti kuma idan ta kama har asibitin sa za'a biyo shi . Haka suka kasance abinsu har shima Adam yayi aure sai dai kuma shi ƴar Kano ya aura Ƙauwar abokin kasuwanci Kabir daga zuwa duba shi ya gano ƙafar sa, dake yana yawan zuwa duban shi tunda Kabir ya haɗa su shikenan ya gano ta anan suka haɗu da ita mai suna Bilkisu.
  Haka  akayi auren sai dai itama da da tashi haihuwa sai ta haifi namiji , lokacin Aisha da Asiya  sun haifi yaran su duka maza, yayin da Aisha ta sake haihuwa itama kuma Asiya a lokacin bata haihu ba shine sa'an yaron da Bilkisu ta haifa, daga nan kuma Bilkisu bata kuma haihuwa ba tun ɗan da ta haifa Aliyu, koda suka sake haihuwa suma basu ƙara ba a lokacin kuma Bilkisu itama ta sami wani cikin wanda suka ɗauki san duniya suka ɗaurawa cikin da zummar cewa mace za'a haifa sai dai kuma kash ba macen bace namiji aka haifa.   Sai gidan ya kasance babu wata mace a gidan sai maza har ma shiyasa  a unguwar su ake kiran gidan da gidan Maza saboda babu mata idan ba iyayen su ba har ta suma yaran suna san suga ƴar macen nan a gidan su amma babu basu da magana sai idan nayi aure mace zan haifa dake duk sun tasa abin su musamman Babba da ƙarami wanda suke ce musu Yaya Babba da ya Yaya ƙarami.  Aisha matar  Ahmad tana da yara huɗu, Babba, Abdulmajid, Al-ameen sai Hafiz shine ƙarami. Kabir kuma nada uku, Ƙarami, Mustapha,  Yusuf,  Yayinda shi kuma Adam yake da yara biyu Aliyu, Ahmad yayan su kenan yaran suka sa masa Sajjad shine autan su gaba ɗaya wanda shima har addu'a suke yi Allah yasa mace ne sai aka haifo namaji suka sa masa Sajjad shima ya beye musu be musa musu ba yayin da suka ci faɗa a wurin Kakar su wacce suke ce mata Inna dake haka suka ji iyayen su na kiran sa yaran yasha gata sosai kasancewar shine auta  a cikin su daga shi  babu wacce ta ƙara haihuwa. Ahmad shine suke ce masa Abba, Kabir kuma Baba,  sai Adam suna kiran sa da Daada.

Haka yaran suka taso cikin so da ƙaunar junan su ga haɗin kai kamar kamar me babu wani wariyar da ake kusan kowa da sa'an sa a gidan Babba da Ƙarami, Abdulmajid da Mustapha, Al-ameen da Aliyu sai su Hafiz da  Yusuf da Sajjad ne kawai be da sa'a komai shi kaɗai ake yi masa abinsa musamman da ya kasance sunan Abba ne da shi sai shima ya fi san shi bama shi kaɗai ba,  kowa yafi san sa saboda shegen surutun sa ga rawar kai uwa uba shiga rai. Yarda suka kasance gidan maza ne hakan ya kasance aikin gidan ma sune suke yi hakan yasa basu je boarding school ba suma kuma basa da sha'awar barin gida duk wani nau'in aikin gida sune ke da wannan alhakin nayin shi, idan kuwa aka ce Abba  yana gari to fa zaka sami sojoji cike a gidan duk da kuwa masu gadin su da driver da masu aikin waje duk sojoji ne hakan kuma be hana suma asa su suyi aikin wajen ba musamman ga wanda yayi laifi. Haka a rayuwar su take tafiya cike da burgewa inda wasun su da dama daga cikin su a cikin Companyn da Baba ya gina suke aiki wasu kuma suke kula da wani Companyn da suke ginawa a Kano da kuma Bauchi sau tari yaran kan halarci wani taro da za'ayi bayan shi Baban ya wakilta su saboda duk wani abu sun ɗauke ragamar yi tunda dukan su de aikin suka raja'a akai   Ƙarami ne kawai ya karanci law ya kuma zama barrister  yayin da Sajjad yace shi ba wani aiki da zai yi shima soja zai zama babu wanda ya na shi ya tafi sai dai kuma dake gata yayi masa yawa yana zuwa ya kafa ya tsare daƙyar da suɗin goshi ya gudu Daada zai bayar shi Abba ya ce a,a sam be san zance ba tunda ya dawo ba ya so shikenan ya zaɓi me zai yi yace likita  shima zai yi ko zai zama irin Daadan sa haka aka yi kuwa Abba ne da yayi masa komai yayin da Daada kallan sa be yi ba daman wayan ci basa shiri idan ba da Anty ma wato Babar sa ita ce babu ruwan ta bata cika faɗa ba shi yasa kowa ya ɗebo shirgin sa da shirman sa ita ce, itace ta kasance tamkar musu Yaya mace shawara ita ce zance ita ce tun suna yara sukayi sabo da ita ita ma kuma tayi sabo da su gata da iya zama. Mama kuwa Aisha wayaga faɗa abu kaɗan kayi sai faɗa haka ma Ummi suma duk faɗa ne da su har gwara Ummi.  Sanda zai tafi karatu lokacin a kayi bikin ƴan uwan sa Yaya Babba da Yaya ƙarami kasancewar sune manya sai da aka gama bikin sannan ya tafi, yana can suka haihu sai dai maza suka haifa su dukan su haka yana can akayi bikin Abdulmajid da Mustapha hakan yasa ya marairaicewa Abba akan kada ayi bikin baya nan, gashi kuma Daada ya kafe akan cewa lalle bazai dawo ba idan ya dawo ma meye amfanin zuwan nasa. Daƙyar de aka samu aka ɗaga bikin ya zamana ranar da zai dawo za'a yi ɗaurin aure sai dai kuma kash hakan ma bata faru ba domin su wani babba a makarantar ta su ya rasu kuma musulmi ne hakan yasa aka ɗaga har sai da aka naɗa matar wanda ya rasun a matsayin gurbin sa tukunna wanda sai da aka ƙara wajen wata guda kenan yaji takaici ba kaɗan ba, babu wanda ya je masa sai Abba kuma be sanar da kowa ga inda zai je ba bare kuma ana shi amma ya riga shi dawowa ba tare suka dawo ba.

Labarin zai fara.......

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now