49

60 0 0
                                    

Kallan ta yake bako ƙiftawa  batare da ya saki fuskar ta ba, haka kawai yake ganin kamar mafarki yake yi, taya za'ayi ace ta zo gare shi? Ta za'ayi ace an ɗaura auren su ba tare da ya sani ba? Aikin waye wannan? 'Sajjad' zuciyar sa ta bashi amsa. Sajjad ne kawai zai iya wannan abun ba tare da kowa ya sani ba, saboda girman irin soyayyar da suke wa junan su. Shin da wanne irin abu zai sakawa Sajjad da shi? Wanne irin sacrifice ne wannan da zai yi domin ya faranta masa rai?

"Zainab?

Ya faɗa cikin sigar tambaya, kasa ɗaga masa kai tayi, dan wani irin kuka ne mai ƙara je san cin ƙarfin ta tana dannewa sai hawaye dake zubo mata, batare da tana sharewa ba. Rasa abin yi yayi kawai ya sata a cikin jikin sa ya rungume ta tsam a jikin sa, yana sakin wata irin ajiyar zuciya. Idan aka ce babu soyayya to tabbas wanda ya faɗa be san meye so ba. So wani irin abu ne mai mugun dafi, da idan ya same ka kai ɗaya kawai zaka ji ciwon da yake maka, ko ya kuwa ya kaje da faɗar zafin da yake maka. Sai a yanzu ne yake jin sa ya dawo cikakken mutum kamar kowa, amma a kullum a cikin kewar ta yake, a da yayi tunanin cewar memories will be enough for him to survive, amma a yanzu yayi realizing cewa, memories will not be enough for to him survive. Yana da buƙatar sake rayuwa da ita. Ya same ta a lokacin da ya yanke ƙauna daga gare ta. Sai dai kuma abinda yake kai kawo a zuciyar sa shine, shin Sajjad ya yafe mata ? Ko kuwa yayi hakan ne saboda farin cikin sa? Idan har yayi hakan ne saboda ya bashi farin ciki to be burgeshi ba har sai sun dawo yarda suke a da shi da Zainab, duk da cewar a lokacin da ya aure ta, ya tashi daga Sajjad ɗin da suka sani ya koma wani Sajjad ɗin na daban mai shiru shiru, dan haka bata san asalin waye ne Sajjad ba, yanzu kuma da ya dawo masa da ita a lokacin da ya dawo Sajjad ɗin sa ko zata iya sake sanin sa????? Wannan tambayar ce be sani ba.

Ƙara ƙanƙame ta yayi kamar ya tsagata gida biyu, tsabar yarda ya rungume ta babu sassauci. Yayin da ita kuma ta tsaya batare da tayi hugging back ba, sai kukan ta da yayi ƙarfi, wanda ya haɗa da ban haƙuri da kuma kewar sa da tayi. Tunda ta rabu da shi batayi farin ciki koda na second ɗaya ba ne, idan tace tayi dariya to da yarinyar ta ne tayi hakan. Tunda ta rabu da shi tayi bankwana da wannan farin cikin, kullum cikin kunci da damuwa take. Be san iya adadin lokacin da suka ja ba a haka, ita ce ta gaji dan matsar da yayi mata tayi yawa, hakan yasa ta fara motsi alamar zata ƙwace hakan yasa shi sauke a jiyar zuciya yana kallan ta cike da so da ƙauna.

*****

Wata irin rakiya aka yiwa Nilah da ba'a samu anyi mata ba, harda Sadiya da bata koma ba, dan hanata tayi haka ma Barrister daƙyar aka samu ta zauna, haka suka yi mata rakiya su dukan su matan familyn ɗin da yaran su, koda suka je gidan, gidan a wani irin hargitse yake pillows har waje ga takarda anbi an yaga ga ruwa ana wasa ana bawa flowers, tsayawa kawai suka yi suna ƙare musu kallo, har shi Sajjad ɗin da tiyo nan a hannun su suna wasa da shi sun jiƙa jikin su.

Mama ce ta fara faɗa, yasa su suka dena, haka ta tusa su a gaba tace sai sun gyara, Matar Yaya babba tace a,a ba'ayi haka ba tunda ga su nan, meye amfanin su, haka kuwa akayi, suka shiga gyaran gidan tsab da shi, Mama banda faɗa babu abinda take masa daga ƙarshe ta tusa ƙeyar sa ya fice a gidan shi da yaran. Aka gyara mata gidan tsaf aka kunna turaren wuta da suka zo mata da shi, sai dare suka bar gidan koda ya tashi dawowa shi ɗaya ya dawo be taho da su ba.

Yana zaman akan gadon wayar sa tayi ƙara yana dubawa yaga Aliyu murmurshi yayi sannan ya ɗaga kiran yana ficewa daga ɗakin ya koma parlour ya zauna.

"Kai ne ko?

Aliyu ya jefa masa tambayar ba tare da ya bari sun gaisa ba.

"Me nayi?

Shima yana tambayar sa irin be san me yayi ɗin nan ba.

"Koma me kayi nagode sosai".

"Yaya Aliyu kasan me?

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now