20

69 1 0
                                    

A hankali ya fara shafa bayan ta yayin da ita kuma ta cigaba da zuba masa zance yana jin ta, wani irin ratsattsan farin ciki ne yake ratsa shi na musamman wanda ya manta rabon da ya ji shi a duniyar nan, banda sakin murmurshi babu abinda yake yi. Jin tayi shiru alamar ta fara bacci yasa shi saurin kallan ta tare da kallan agogo yaga baya yi ya maida duban sa ga agogon hannun sa yaga shabiyu da mintuna, da sauri ya ajje tare da tattara kayan ya saɓe ta a kafaɗa sannan ya ɗauki kayan ya, yana sauka ya tarar da sojojin sa sun taso ƙofa suka buɗe masa yasa ta sannan suma suka shiga, tambayar su yayi inda suka san wannan uniform ɗin aka sami drivern ya sani amma be sani ba ko akwai wata mai irin uniform ɗin bayan wannan.

"Sir! Munzo".

Kallan makarantar yake yi dakyau, kamar gida aka mayar makaranta da alama bata masu ƙarfi bace ta masu dan wadata ce da rufin asiri ta ku ya ku bayi. Rasa yarda zai tashe ta yayi gashi  sam be gaji da jin ɗumin ta ba, amma ganin yara sun fara fitowa alamar an tashi yasa shi tashin ta akan dole badan ya so ba.

"Mammy kaɗan zan ƙaga".

"Tashi mana".

Ya faɗa yana zaunar ta. Tashi tayi tana janyo baki gaba tare da murza ido. Hijabin ta yasa mata tare da takalmi, zai goya mata jakar ta karɓa ta duba taga bounty ɗin da ta bashi.

Tace, "baka fa nayi kuma shine zaka samun?

"Yi haƙugi".

Turɓune fuska tayi zata sa masa kuka jin ya kwaikwayeta, yasa shi saurin janyo ta jikin sa ya hau rarrashi.

Tace, "Kuma Daddyn ma bazan ce ba".

"Yi haƙuri".

Bashi tayi bounty ɗin ya karɓa, ta ɗauko bankin ta ta bashi.

Tace, "Ka siyo min Baby mai kyau gobe ka kawo min sai na kaiwa Mammy take masa wanka".

Karɓa yayi yana juya gwangwanin a hannun sa, yana sakin murmurshi.

Yace, "Ba'a garin nan nake ba".

Nan take annurin dake fuskar ta ya ɓata ɓat tana kallan shi ganin haka yasa shi saurin cewa.

"Ina zuwa duk weekend, anan nake yi".

Murmurshi ta sakar masa sannan ya buɗe mata ta fita, yana kallan tana kalle -kalle, sai kuma yaga ta ruga da gudu har zuwa wurin wasu yara, ga dukkan alamu sune Sultan da Abie, yana daga inda yake zaune yake hango ta, tana ta zuba kamar de tana basu labari tunda gashi tana nuna musu motar sa, murmurshi sosai ne akan fuskar sa, ta buɗe jakar ta ta ciro musu abinda ta ajje suka sami waje suka zauna suka fara ci ita kuma tana ta zuba kamar kanya, basu jima sai ga Ruƙayya ta zo ɗaukan su suka tafi. A hankali ya zame ya kwanta yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa a hankali kafin ya lumshe idan sa yana mai ƙara damƙe abinda ta bashi a hannun sa. Tare da faɗawa duniyar tunani.

****

A lokacin da ya sa ta a cikin mota a lokacin ne ita kuma Nilah ta fito domin samun mafitar yadda zata yi da wannan flash ɗin gashi bata san sunan sa ba, yanke shawarar shiga office ɗin sa tayi  kawai tunda taji yanzu zasu shiga meeting ta bakin Faisal taji, rasa inda zata je tayi hakan yasa zuwa masallaci ganin shabiyu tayi. Zuwa tayi ta ɗan kwanta bata jima ba kuwa sai bacci ya ɗauke ta, kiran sallahr da aka fara ne ya tashe ta tare da zuwa da yin alwala. Abinci taje domin taci taga Faisal.

"Baku shiga meeting ɗin ba?

"Wanda za'ayi meeting ɗin domin shi baya nan".

"Waye shi?

Ta faɗa bayan sun karɓo abinci be bata amsa ba har sai da suka zauna.

Yace, "Ɗan Uwan su ne".

"Wai su haka suke da ƴan uwa?

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now