34

53 1 0
                                    

Sajjad na zaune bayan fitar ta ta yayi tunanin wasu files da ta canzawa waje ya duba be gani ba gashi yanzu yake san yin amfani da shi ya kuma lura idan ta fita bata dawowa da wuri, tsaki yaja kawai ya bita a baya, yana sauƙa daga elevator ya hango ta, hakan yasa shi bin ta amma ganin tayi saurin laɓewa a jikin wani corridor yasa shi dakatawa daga saurin da yake ya koma tafiya a hankali yana kallan ta cike da mamaki, yayin da shi kuma ta inda yake baya ganin su. Dena tafiyar yayi ya tsaya, yaga wasu sun fito, ita kuma yaga ta fito da sauri tana binsu, yasa shi shima binta sai dai baya ɗaga ƙafa dan kada ya cimma mata. Yarda ba su gane suna bin ta ba, haka itama bata gane yana binta ba har suka fito daga wurin suka shiga tsohon companyn da ada shine companyn amma yanzu baya amfani dan da aka tashi new modern aka gina shi kuma aka bar shi ɗan fasalin sa kamar gida haka yake ƙatan parlour ne akayi sai kuma aka bi aka yi ɗakuna haka yake, wurin ba amfani ake da shi ba sai yanzu ne da Sajjad yaga ya dace a gyara.

Waje ta samu ta laɓe amma ba jin su ba take, hakan yasa ta bin gini tana yi tana sanɗa kar su kama ta, ganin takardun hannun ta za su bata cikas yasa ta tsayawa ta ɗaga skirt ɗin ta, ta soke su. Yana kallan ta duk abinda take yi amma shi daga ƙarshe be fara bin ginin ba. Ganin za tayi nisa ta barshi yasa shi saurin binta yana yin yarda tayi, ta cire takalmin ta ta ɗaura akan windown sannan ta dira ta juyo zata ɗauki takalmin ta, tagan shi yana ɗaura nashi takalmin. Wani irin waro ido tayi tana kallan shi baki a buɗe.

"Me ya kawo ka nan?

Ta faɗa tana tambayar sa. Be bata amsa ba, ya diro amma be diro a sa ba, dan akan ƙusa ya dira ƙafar, ƙara zai ƙwala tayi saurin rufe mata baki da hannun ta, tana zare masa ido, shi kuma riƙe hannun ta gam tsabar azabtar da yake ji ba zata barshi yayi magana ba.

"Motsin me nake ji?

"Nima naji".

Suka nufo wurin, Jan sa tayi zuwa wani ɗakin suka ɓoye tare da ɗan tura ƙofar yarda ko an turo ƙofar baza'a gan su ba,ta kuma ƙi sakin bakin sa ta riƙe shi gam.

"Bakomai fa".

"Inaga iska ce daman ba motsin mutum bane".

"Ehh ba".

Suka suka faɗa suna komawa amma duk da haka sai da suka ƙara dubawa abin ka marasa gaskiya, Allah yasa ba su lura da takalmin sa dake kan window ba, tunawa da hakan da tayi ne yasa ta sauri komawa ta ɗauko ta dawo.

"Me kake yi anan?

"Ke na biyo".

Dafe goshi tayi, murya can ƙasa.

"Baka da hankali ne? Dan kawai kaga na taho sai ka taho kai ma?

Shiru yayi mata kawai yana kallan ta.

"Na riga da na saba ɗaukan riski amma kai baka saba ba".

Ta faɗa tana zaunar da shi a ƙasan wurin, duk da ya so ya turje ƙin zaman, ganin irin dattin dake tattare da wurin, amma kallon da ta wurga masa yasa shi saduda ya zauna, tana masa irin kallan nan ya fake shi ta fin cike ƙunsar ƙarar zai yi tayi saurin denne masa baki da suka hannun ta ta kuma naɗe shi dukan ta akan sa. Kallan cikin idan sa take yayin da shima yake mata wani irin kallo mai wuyar sha'ani da ganewa cike da zallar ƙauna da soyayya gami da kewan da bazata faɗu ba. Itama ana ta idanun haka ne.

"Ka dena kallona haka kuma". Ta faɗa tana kumbura baki tare da maka masa harara.

"Sauka akai na tunda ba katifa kika samu ba".

Tura baki tayi gaba tana sauko cike da gunguni. Tana cire ɗan kwalinta tare da kama ƙafar ta fara ɗaura har ta ɗaure shi tas, yayin da shi kuma ya kafe sumar ta da ido. Ƙananan kitson da aka mata yake bi da kallo wanda aka mata two step na ƙasan har ka fadarta ya sauko...

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now