32

49 1 0
                                    

Cikin tuhuma da zargi yake kallan ta batare da ya ce da ita ƙala ba har ta shigo, yayin da ita kuma ta maze ta cukume fuskar ta har ta ƙara so ta sami waje ta zaune tana ƙara damƙe wayar a tsakanin cinyar ta dan ji take kamar zata tuna mata asiri ne.

"Ina kika je?

"Yunwa nake ji".

Ta faɗa cikin sanyi.

"Waya ce miki an damu da ki rayu? Mutuwa nake so kiyi mutuwa".

Shiru tayi bata ce komai ba.

"Sau ɗaya tal na yarda a baki abinci".

Ba ta kuma cewa komai yayi tsaki yaja ya fice. Sai da ya jima da sauka sannan ta tashi ta kulle tasa sakata a duka ƙofar guda biyu ta shiga can lungun gado ta ta ɓuye sannan ta fara sa numbern sa Allah ya so ta, ta haddace a lokacin yana tashen kiran su suyi ta zabga zancen su.

A lokacin yana zaune a tsakiyar gado ya kasa yin komai banda jakar ta da ya tasa a gaba ya zazzage komai a na ciki yana kallo ɗaya bayan ɗaya yana so ya fahimci wani abu amma kuma ya kasa yin haka, ga wani zazzaɓi dake nema ya rufe shi da ciwon kai mai tsanani, kuma yaƙi ya haƙura ya ajje yayi bacci, idan yayi-yayi sai yaje yayi Sallah ya kuma dawowa ya ci-gaba haka yayi tayi har lokaci ya ja. Jin wayar sa na vibrating yasa shi kallan wayar da mamakin waye zai kira shi, lokaci guda kuma yayi saurin ɗaukowa ko za'ayi dace ita ce. Har kiran ya katse da sauri ya bi kiran, ya a kunne be yi ba magana itama bata yi maganar ba.

Daga can shiru tayi jin ya ɗaga yasa sakin wani ajiyar zuciya tare da sakin wani irin siririn hawaye, kaf duniya shi kaɗai take yiwa kuka shi kadai ne zai mata abu tayi kuka, shi kaɗai ne zata yi kuka akan sa ta rasa wanne irin so ne take yiwa wannan bawan Allah.

Ajiyar zuciyar da yaji ta saki ne yasa shi ture kayan da ya baza ya kwanta yana mai ƙudundinewa a wuri ɗaya. Shashshekar kukan da ta fara ne yasa shi lumshe idan sa yana tuno rayuwar su. Ji yayi shi ɗin ma yana neman yayi kuka yasa shi tashi zaune sai dai inaaa ya makara tuno hawaye ya wanke masa fuska tas.

"Me yasa Yaya Nilah?

Yayi mata tambayar yana hawaye na zuba a idan sa,  ya manta da a'ina take ya manta da a wanne hali take bare ya gane cewar basu da lokaci fa. Yayin da Nilah ta ƙara fashe masa da wani saban kukan tana toshe bakin ta, jin kukan nawa yana echoing.

"Ban san inda nake ba".

Ta faɗa cikin matsananci kuka. Sai a lokacin ya tuna ashe fa sace ta akayi ko, da sauri ya diro daga kan gado har yana neman ya faɗi ya nufi ƙofa.

"Kar ki kashe".

A lokacin har ya fito compound ɗin gidan tsabar sauri. Da sauri Aliyu ya fito da yaji fitar sa dake beyi ba bacci saboda yana yin jikin sa, ya kuma san irin wahalar da yake sha idan baya da lafiya, sojojin sa ne suka taso suka tarye su beyi wata-wata ba ya ba su numbern cikin ƙaƙanin lokaci aka haɗa suka shiga mota suka tafi har Aliyu Al-ameen ne da yaji ƙarar tashin mota shima suka fito shida Matar sa, amma sai dai shi be bi su ba saboda halin da matar sa ke ciki kuma gashi cikin dare ba za'a barta ita kadai ba.

Suna tafiya a hanya Sajjad yayi lamo yana jin kukan ta, ya kuma kasa ce mata ta dena shima da zai samu mai lallashi sa sai yafi ta jin daɗi. Tsab aka shigo unguwar gudun kada a tsorata mutane yasa su bi a hankali cikin kuma sanɗa da taka tsantsan na wanda suka san aikin su, shi dai Sajjad burin sa kawai yayi arba da ita. Knocking suka yi bayan sun zagaye gidan tsab tare da nazarin komai cikin hikima da dabara.

"Waye?

"Mune har kayi bacci kuma bamu shigo ba".

"Ai nazaci kowa ya shigo, ku kam kun fiye yawo".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now