6

93 1 0
                                    

Yana kwance  shi kaɗai sai murmurshi yake yana juyi daga nan ya koma can daga can ya koma nan, Allah Allah yake ya bawa Aliyu wannan labari labari biyu kenan dana jiya dana yau, shima ashe zai iya.'ai kuwa ban zan bari ta rena ni ba' ya faɗa a zuciyar sa yana sake juyawa.

Mahmud ne ya shigo ɗakin yaga yadda yake wani juyi yana murmurshi.

Yace, "Da alama ka fara zaucewa".

Tashi zaune yayi yace, "Ka fiye sa ido dayawa ina ruwan ka da ni".

"Tunda ka dawo kake faman murmurshi". 

Be tanka masa ba ya fice masa a ɗakin ya bashi waje, wajen gidan su ya dawo kan baranda ya zauna, sai kuma wani tunanin ya zo masa kai da sauri ya ɗauki waya ya yayi kira be jima ya kashe, yana kashewa kiran Hafiz na shigo.

"Hafizu na Yusufu".

"Wallahi Sajjad bansan wanne irin reni ne a tsakanin mu ba da kai ka bi ka rena mu".

"Wata nawa kuka bani da zaku ce kun wani fini ai yanzu kan mu ɗaya".

"Wata talatin da shida muka baka".

"Uhmm".

Kawai yace.

Hafiz yace, "Yaushe zaka dawo ne?

"Mene ya faru?

"Kawai ka faɗa min mana".

"Nan ba da jimawa ba zan dawo".

"Kasan me?

"Sai ka faɗa".

"Da zaman ka kayi wallahi, tunda idan ka dawo babu abinda zakayi".

"Lalle ma! Kuma zuwa asibitin fa?

"Laa baka san Daada baya nan ba?

"Ina ya tafi".

"Ƙaro karatu".

"Shi yanzu Daada ina shi ina wani karatu fisabilihi? Maganar gaskiya fa kenan".

"Haka yake so. A shawarce kenan fa".

"Zan duba na gani idan nan ɗin ya min daɗi shikenan".

"Kai da kake da saurin sabo ma?

"Aikuwa har nayi aboki".

"Ka gani".

"Kuma nayi budurwa".

Wata uwar dariya Hafiz ya kwashe da ita.

Yace, "Sajjad bansan yaushe ka fara ƙarya ba? Kaine da budurwa?

"Shi yasa bana so na faɗa maka abu".

"Allah ya baka haƙuri".

Kashe wayar sa yayi ya fara mita yana ƙunƙuni shi kaɗai.

~~~~~

KADUNA.

Yusuf ne ya zo ya sami Hafiz yana murmurshi gama wayar sa da Sajjad kenan.

"Lafiya?

"Wai Sajjad ne yayi budurwa".

"Kai haba?

Shima ya faɗa yana murmurshin.

"Wallahi haka yace min, nasan kuma kawai ganin ta yayi, imma ya kasa magana ko kuma ya faɗa mata magana marar daɗi kasan halin gogan?

"Wallahi kuwa indai Sajjad zai yi abinda yafi haka ma".

Yusuf ya cigaba, "Ya maganar dawowar?

"Yace zai duba ya gani".

"Bana so ya dawo domin idan ya dawo ya tarar da sannu case ɗin to tabbas zai iya shafar sa".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now