7

78 4 0
                                    

Ganin ta tashi tsaye yasa shima Sajjad tashi yana kallan ta sannan ya kalli mutumim, ganin ya fara matsowa inda suke yasa ta ɓoya a bayan sa.

"lafiya?

Sajjad ya tambaya dan ganin yadda ta ɓoya sai tabbatar da cewa tsoron sa take.

"Ni kake lafiya? Ka taɓa min matar da zan aura gobe kuma sannan kake cewa lafiya?

'aure?

Ya maimaita a zuciyar sa, lokaci guda kuma abin ya faɗo masa sanda Muftahu na faɗa masa, rumtse idan sa yayi ƙarfi, lokaci guda kuma zuciyar sa na karyewa yana jin wani irin zazzaɓi a jikin sa da taɓa ji ba, kafin kuma ya buɗe idan a hankali, jin wasu irin kalamai da mutumin yake jifan sa da su, a halin da yake ciki ba zai iya buɗe baki ba bare kuma yayi faɗa daman kuma shi can ba mutum ne me faɗa ba shidai a barshi da taƙalar ƴan uwan sa da kuma abokin sa Mahmud shima dan yasan halin sa ne.

Sa kai yayi zai tafi, ya riƙe bayan rigar sa gam, hakan yasa shi kasa tafiyar.

"Daman ba yau na saba ganin ku da tare ba saboda shi nace a dena barin ki kina fitowa amma dake bakya jin magana shine kika fito ko?

Hausar kawai zai baka tabbacin bahaushe ne ko kuma de ya iya Hausa sosai domin baza'a taɓa kiran sa da yare ba.

"Wuce mu tafi gida".

Ya daka mata tsawa, maimakon ta sake shi, sai ta ƙara ƙanƙame shi sosai. Kallan ta Sajjad yayi yaga ta dena hawayen hasalima idan ta a rufe yake, jikin ta kuma ya dena karkarwa da ya ɗauka, a hankali ya juyo bayan ya cire hannun ta ta baya yana kallon ta har zai kai hannu ya taɓa ta sai kuma ya maida hannun sa ya ajje yana kallon ta, duk kallan da yake mata sai yau ne ya ƙare mata kallo, gashin dake lulluɓe da goshin ta shine zai tabbatar maka da cewan tana sa suma ga kuma gashin girar ta mai kyau gwanin ban sha'awa dashi bakin ta shape ɗin love ne da shi motse shin da tayi ne yasa shape ɗin fitowa sosai hancin ta ma ɗan sirit da shi mai kyau, babu abinda ya burge shi a fuskar ta irin girar ta, haka nan yaji yana so ya shafa amma yasan babu hali babu kuma dama babu ma rana, idan har ya sake ganin ta ma kenan.

Ya buɗe baki kenan da niyyar yin magana yaji an buga masa wani abu a kai ƙara ya saki tare da dafe kansa ya tsugunna a ƙasa yayin da ita kuma ta ƙwalla ƙara da ƙarfi ganin sun zagaye shi zasu dake shi yasa ta rugawa da gudu domin kiran wani a gidan su dawowar sa kenan daga tafiya yagan ta a firgice.

"Lafiyan ki kuwa?

"Ga...ga..ga..ga ..".

Ta kasa faɗa, sai nuna bayan ta take tana haki.

"Waye?

Ya faɗa yana kamota wai ko zata nutsu sai ƙacewa tayi.

Babar Garko ne ya fito dan yana sama yana kallon ta ta ɗakin sa, shine ya fito.

Yace, "Muftahu kuje da ita mana tunda ta kasa magana".

Ai kuwa bata jira cewar sa ba ta kama hannun sa, tana jan sa  kafin suje sun yi masa duka laga laga duk da basu bar shi a haka ba wani daga cikin su ne ya ɗaga gorar hannun sa zai maka masa a ciki Allah ya kawo su Muftahu ya ture shi ko sauraran sa be yi ba ya kama shi ya ɗaga shi. Banda kuka abin da Nilah take ita ce ta ɗauko masa wayar sa da ta faɗi ana daukan sa da takalmin sa suka tafi, duk inda suka wuce kallan su ake kasancewa magriba tana daf da yi mutane wasu na dawowa wasu kuma na fitowa hakan yasa ake kallan su, har suka zo gida.

Baba Garko na ƙofar gida yana safa da Marwa yana tunanin mene zai biyo baya kuma mene yake faruwa, duk abinda zai firgita ta yasan abu ne ba ƙarami ba. Yana haka sai ga su kuwa da saurin sa ya biyo shi.

"Subhanallahi waye, su waye suka masa wannan abu? Me ya faru?

Muftahu dake kame dashi yana tafiya.

Yace, "Baffa Likitan nan ne fa".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now