44

63 0 0
                                    

"An kulle ka ma ba zaka haƙura ba?

Barrister ta faɗa tana kallan Yahaya Sabo da hannun sa ke riƙe da handcuff yayi wani iri da shi ya rame kamar wanda yayi wata a gidan yarin. Dariya yayi ta irin baki san waye ni ba.

"Ai maciji kuka kashe baku sare kan ba".

Tace, "Allah ko?

Sai tayi dariya.

Tace, "Yanzu kuma idan mun sare kan fa?

"Ai ba zaku iya ba. Saboda idan kun shiga kotu mutumin a yanzun nawa ne".

"Haba?

"Kina so na tabbatar miki ne?

Girgiza kai tayi tana jan numfashi tare da ɗan kujerar ta baya. Bismillah.

Ta faɗa tana ɗaukan ruwan da aka ajje masa. Ba tantama ya ɗauka ya sha dan ya jima be sha ruwan gora ba. Sai da ya shanye tas, tana kallan shi.

Tace, "Ba kai ne kawai ka iya wasan ba. Kana da awa asharin huɗu da mintina goma sha biyu. Sune kawai suka rage maka a rayuwar ka".

"Ban gane ba?

"Zaka gane lokacin da ka rasa rayuwar ka".

Ƙarami da kawai a tsaye yake yana jin su be tanka ba sai yanzu ya matso.

Yace, "A cikin ruwan da kasha, akwai wata guba da aka sa a ciki tana aiki ne batare da mutum yasan meke damin shi, har mutu kuma babu wanda ya isa ya sani. Mun saka mata ita ne,  saboda ba za'a gane cewar ita ka ci ba. Bama za'a gane ba mutuwar Allah da Annabi bane".

Tashi tayi.

Tace, "Allah ya jiƙan musulmi".

"Ameen".

Ƙarami ya faɗa yana barin wajen, sororo kawai ya tsaya yana bin su da ido, daman zasu iya kashe shi? Ashe suma ba su da imani? Yanzu ina kuɗin da ya bayar dan ayi masa wannan abun? Kenan babu ? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.

Ya fara faɗa yana nanatawa, babu wanda zai masa wannan abun sai Mukhtar Abieyola hakan yasa ana zuwa ɗaukan su domin a maida shi ya shiga ɗakin sa ya shaƙe masa wuya kafin ya riga shi mutuwa shi bari ya kashe shi. Da sauri aka zo aka raba su sai sumbato yake yana sai ya kashe shi. Yayin da Mukhtar Abieyola ya riƙe wuyan sa yana murzawa tare da kakin amai idan sa yayi jajur alamar yaji ƙamshin mutuwa fa.

Yahaya Sabo kuwa banda sumbato babu abinda yake yi, ya rasa me yake masa daɗi komai aka kawo baya ci, kawai zancen mutuwa yake sai sun riga shi kafin ya mutu sai yaga sun tsiya ce sannan zai mutu ya tsane su, haka yayi ta soki burutson sa babu wanda ya kula shi, shi ba ga Sallah ba, shi ba ga Salati ba sai abin yayi masa fiye da tunanin sa. Haka ya wuni cur babu yana zankaɗe zancen shi kaɗai ya rasa meke masa daɗi a rayuwar sa. Yayin da ya kwana idan sa biyu yasan kuma lokacin sa ne yayi hakan yasa tashi kafin azahar lokacin mutuwar sa yayi kawai ya gudu ya je ya cinna musu wuta har shi kowa ma ya mutu, sune kaɗai mutanen da ya ƙwallafa rai a dukiyar su be samu ba sai asara da tayi zabgawa tunda daga farko, daga farko de kamar da nasara ashe zai ƙare babu nasara, yayin da daman biyu ce ta huɗu su kuma suna jin haushin Daada ne ya fi su,  tun suna makaranta su Dr. Ismail kenan, har girman su ko ina shike lashe komai, wannan hassada da baƙin ciki shine yayi tasiri a ran su, suka haɗa baki da Yahaya Sabo suka fara musu zagon kasa har Allah ya basu nasara a kulle Daada na farko. Wannan karam kuma sai suka faɗi wanwas suka ci ƙasa. Fitowa yayi kowa yana bacci duk da an fara kiran Sallahr asuba amma ahaka ya fito yana bin ko ina da kallo, babu kowa a wajen, daman rena musu hankali kenan ake babu wasu masu tsaron su, yana fita yaga babu kowa a wajen, da gudu kuwa ya ɗame ƙafa sai gashi a bakin gate sai dai me yana fita ya kiciɓus da sojoji sun yi layi kamar wanda suke jiran sa.....

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now