21

55 2 0
                                    

"Daa..."

Sai kuma yayi shiru Daada yake so yace amma ya kasa faɗa, saboda wani irin fargici da ya shige shi lokaci guda, kafin yasa hannun sa ya shafi fuskar sa, sannan ya mai da kallan sa ga Daada.

"Daada sai me kuma?

Abinda ya iya faɗa kenan.

"Bayan ya sace ta, bayan wani lokaci sai ya maida ta wurin sa, abinda be sani ba kuma shine, Mahaifin yaron da yake so ƴar ta sa ya aura yana da wani ƙuduri daman akan sa shiyasa suka harbi Sajjad, domin kada a gano su yasa suka tada bomabomai".

"Ita kuma yarinyar da aka sace ta sai ta gudu wanda ba'a san inda take ba kuma wanda suka sace ta suma suka kama gaban su gudun abinda zai je ya dawo".

"Dalilin da yasa Mahaifin ta ya yarda da auren a lokacin saboda diamond ring ɗin da yaga Sajjad ya bawa daga nan yasan lalle akwai wani abu a ƙasa".

"Wannan shine abinda na sani".

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Karamin ya sauke.

Yace, "Amma Daada kana nan wurin taya kasan wannan abubuwan?

"Wanda suka muke tare da shi, ai ɗan uwa ne ga Mukhtar Abieyola ɗin. Mahaifin su ɗaya da ya rasu shine kowa ya kama gaban sa, shi Mukhtar Abieyola Mahaifiyar sa ƴar can Taraba ce shi kuma wanda muke tare da shi, Sadisu Abieyola Mahaifiyar sa ƴan nan ce, duk wani abu da ƙanin sa yayi ana sanar da shi, haka ma dangantakar su da ita Hadiza".

"Daga jin sunan Sajjad kawai nasan lalle bakowa bane sai ɗana, na damu iya damuwa, musamman dana lura yana matuƙar san yarinyar, kaine mutum na farko dana faɗawa wannan abun, dan haka kada ka sanar da kowa, koda shi Sajjad ɗin ne".

"Daada wa yake zuwa yana sanar da shi wannan abubuwan?

"Ƙarami kenan ai shi nan da kake gani, babu labarin da bazaka samu ba, matuƙar kana so ka samu".

"Yanzu ta ina zamu fara neman ta?

"Shine bansani ba, da ace wanda suka kamata suna na kafini sanin yadda zakuyi aikin ku".

Jinjina kai yayi.

Yace, "Matsalar da bamu san sanda take ba".

"Idan ka san inda take babu abinda zaka iya yi akai. Idan hallau zaka kama Mahaifinta baka da hujja sannan shima wanda ya harbi Sajjad ɗin duka babu abinda zaka iya yi akai".

"Karo na biyu a rayuwata kenan da zan ƙara faɗuwa wanj case ɗin?

"Daman ba kullum ake samun nasara ba".

Shiru sukayi kafin Daada yace.

"So yanzu mun shirya?

Ɗagowa yayi yana wani tura baki gaba alamar a'a fa. Kafin kuma suka rungume juna cike da kulawa gami da soyayya.

~~~~

Koda suka shiga meeting kasa yin komai yayi kawai kallan mutanen yake, idan yace ga abinda ake cewa to yayi ƙarya, dan sam be san abinda ake faɗa ba, kawai tunanin sa yayi nisa a wurinta, tambayar da zuciyar sa ke masa ita ce. Wacece ita? Wannan tambayar ta tsaya masa a rai matuƙa. Tashi yayi domin ya fita jin wani irin sara masa da kan sa yake yi, zura hannunsa a aljihu kenan ya jiyo wani abu, a hankali ya zaro abun ya kalla da wani irin mamaki yake bin flash ɗin da kallo wannan shine flash ɗin da Baba ya bashi, ya akayi haka? Daman anan yasa? Amma ai ba wannan kayan jiya ya sa ba?

Kowa kallan sa yake ganin yana juya flash ɗin, kafin ya tsaida kallan sa ga sectary ɗin Abdulmajid yana kallon sa, shine mutumin da bawa jakar sa, shine kuma wanda zai tambaya. Meyasa sai yanzu zai yi wannan tunanin? Ganin haka yasa kowa ya fara kallan ɗan uwansa ganin kallo yaƙi ƙare wa gashi kuma a tsaye da Flash a hannun sa.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now