13

67 2 0
                                    

Duka abinda ya faru ne ya dawo mata a cikin mafarki yadda idan sa ke a kan ta itama haka idan ta ke kan sa, tana miƙo masa hannu ana janye ta a lokaci guda idan su ya rufe, a fargice ta farka gaban ta faɗuwa sosai, kafin ta nutsu ta share zufar dake zuba a jikin ta, tare da bin inda take kallo. Ɗaki ne sabo dal amma babu furnitures a cikin ga kuma wata ƙofa wacce take bata tabbacin toilet ne, sai windows maka maka da su guda biyu, ita kan ta a ƙasan tiles ɗin dake ɗakin aka shimfiɗe ta.

Turo ɗakin da akayi ne yasa ta kallan wanda ya shigo, da ledar shopping a hannun sa sai baƙar leda, wulla mata yayi.

Yace, "Haka aka ce na kawo miki ko zaki ke tunawa da mijin ki, domin ke da ki ƙara ganin sa sai a lahira idan kun haɗu".

Kallan sa take ba ko ƙiftawa idan nan a ƙyeƙyeshi ƙam ya tsaya kan sa, ba za kuma ka taɓa cewa ga abinda take ciki ba.

"Ke ni kike wa wanna kallan?

"Waya sa ku sace ni?

"Wannan ba damuwar ki bane".

Ya faɗa yana ficewa, bin sa tayi da kallo har ya fice, babu kuma alamar ya rufe ƙofar dan bata ji alamar rufewa ba. Kifa kan ta tayi a tsakanin cinyar ta, ta rushe da kuka, kuka ne take yi ba wai na kan ta ba, kukan tunanin wanne hali yake ciki? Shin yana raye ko ya mutu? Wannan tambayar guda biyu ita ce wacce tayiwa kan ta. Kafin ya rarrashi kan ta tayi shiru, ta janyo ledar da aka kawo mata taga harda abinci, abincin ta ci kaɗan ta ajje tasha ruwan shima kaɗan kafin ta tashi ta shiga toilet babu ruwa a ciki hakan yasa ta damar fitowa, kai tsaye buɗe ƙofar ɗakin tayi ta fito, babu kowa a parlourn sai abinci da ta gani an babbuɗe za'a fara ci. Ta kalli ƙofar shigowa taga a buɗe wanwar hakan yasa wani ya ɗarsu a zuciyar ta na ta gudu, har taje bakin ƙofa tagan su a wajen sai ta dawo ta tsaya. Ɗaga daga cikin su ne ya shigo ya ganta.

"Me kike anan?

Kai tsaye babu wani alamar tsoro.

Tace, "Ina so nayi sallah kuma ba ruwa".

"Ga ruwa can ɗauki".

"Ai kunsan ba ice kuka ajje ba, dole zan buƙaci ruwa da yawa".

"Ke..."

"Kar ka ƙara ce min ke".

Ta katse shi tana cigaba da tsare da ido. Zuciyar ta banda tafasa babu abinda take, ji take kamar ta watsa masa mari ko zata ji daɗi amma bata san me zasu mata ba, shi kuwa galala ya tsaya yana kallon ta, jin tsaurin idon da take masa, har take iya ja da shi.

"Ni kike faɗa wa wannan abu?

"Ko kana so na ƙara maka?

Yanzu kam ya yarda ba kowa ke jin tsoro ba. Jiki a sanyaye gudun kada ya ja da ita reni ya shiga tsakaninsu, ita kuma ta juya ta koma. Tana zaune sai ga su da ruwan an kawo mata jarga guda andire da buta. Da kallo ta bisu kafin ta tashi shiga bayin. Koda ta fito a ƙasa tayi sallahr ya yanke kan ta da veil ɗin abayar ta. Sallolin dake kan ta ta rama duka sannan tayi addu'a sosai. Kafin ta faɗa duniyar tunani.

Sai sa akayi la'asar lis, ta tashi ta buɗe ɗakin ta fito, basa nan sun fita ta leƙa bata ga kowa ba, ta fito a ɗari ta je bakin ƙofar taga ba'a kulle ba, kawai germing ƙofar akayi, tsabar sauri jikin ta har ɓari yake ta cire zata fita kenan, wani ya fito daga wani ɗan ɗaki.

"Ke! Ke!

Ya ƙwalla mata kira gami da rugowa a guje, sai dai ko juyowa batayi ba ta fice, kafin ya fito har ta sha kwanar gidan da ana fitowa sai wata kwana da ta yi cikin layi duk gidaje ne a wurin, da gudu ta shiga wani gida dake kusa da ita, a zauren su ta maƙale a bayan ƙofa, mutumin gidan ne ya fito ganin sa a ƙofar gidan.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now