19

52 0 0
                                    

Koda ta koma gida babu abinda ta ci haka ta zauna tana tunani duk surutun da Jiddah take mata ba jinta take ba sai dai kawai tayi ɗan murmurshi alamar tana ji amma ba ji ba take, har dare ya tsala tana warwara tana ƙullawa ta rasa ya zatayi da wannan mutanen guda biyu, idan ta juya nan sai ta juya nan ganin ba yi mata zai yi ba yasa ta zuwa tayi alwala ta fara sallah raka'a biyu tayi, tayi addu'a sannan ta dawo ta kwanta, ko addu'a bata gama ba bacci ya ɗauke ta. Washegari kamar kullum suka shirya suka tafi amma yau Jiddah ta so rashin mutuncin ta wai ba zata je ba yau, sai da ta mata jan ido sannan ta fito suka tafi ita ce ta makarar da su amma da, da wuri zasu je, ta rasa wannan wani irin hali ne da Jiddah ta kwaso ita de ta san kwata-kwata batayi wannan abun ba, maybe shine yayi ko a ƴan uwan sa, ita ina taga ƴan uwan ma da zata yi musu wannan abun ko uwar da zatayiwa haka, komai da kaga mutum yana yi samun waje ne.

"Mammy dan Allah wannan satin   ki kaimu wajen wasa dan Allah".

Jiddah ta faɗa, yayin da Abie shima yace.

"Ehh! Mammy kullum sai Ameel ya bamu labali duk Fliday sai Abban su da Momyn su sun kai su".

"Waye Ameer?

"Kaiiii!

Jiddah ta faɗa irin mamakin nan na daban baki san shi ba.

Sultan yace, "Wani abokin Abie ne a Islamiyya yake basu labari".

"To zan duba na gani amma babu tabbas ɗin za muje".

"Dan Allah. Birthday fa zai yi".

Kallan Abie ɗin kawai take, shi da Abokai basu dame shi ba, amma shine yake maganar wani Ameer duk yadda akayi akwai alaƙa sosai a tsakanin su tunda har suka saba haka ya yarda yake bashi labari.

Abie yace, "Shine fa labalin da nace zan baki? Kuma kike ta tafiya aiki".

Ɗan murmurshi kawai tayi masa.

Yace, "Be jima da kawo shi ba, shine wani Pilifect ya dake shi, kuma daman ko? Kuka fa yake".

Suka saki dariya Shida Jiddah.

Jiddah tace, "Kuma kullum da kuka ake kawo shi, nice ma na faga gaggashin sa, tukunna ya ɗan yi shigu fagkon zuwan sa".

Haka sukayi ta bata labari har suka iso makarantar su, mai Napep ɗin kuwa jinjina kai yake yana mamakin wannan surutun na yara, ita kuma tana gane abun ta, dan shi ba kalmomin duka yake gane wa ba musanman na Jiddah da take mai da R, G sam bata da R ba kuma ranar da za tayi da alama. Itama sauke ta yayi a wurin nata aikin. Yau kam babu mutane da yawa ba kamar jiya ba, a hankali take takawa har ta iso build din su kallo ɗaya zaka mata ka gane bacci be ishe ta ba saboda yadda idan ta ya kumbura ga kuma kukan da ta sha jiya sai abun ya haɗe mata yayi mata yawa.

Jin tana jin yunwa yasa ta tana ajjewa jakar ta, ta fito domin zuwa cin abinci taga wannan sectary ɗin na jiya yana ta sauri ya nufi inda suka haɗu da wannan mutumin, da sauri itama ta bishi a baya ba tare da tana making sound ba, ganin zai juyo yasa ta ɓoyewa a bayan bishiya tare da sauya hanya ta nufa inda suka haɗu jiyan, aikuwa de shine, yana jiran sa yana zuwa taga ya miƙa masa flash ya juya ya tafi, shima fitowa yayi ya tafi, wanda aka bawa flash ɗin ta fara bi har taga sun zo building ɗin su  a kusan tare suka shiga da ita dan haka ta wuce shi, shi kuma yana gaisawa da mutane, tsaye tayi tana kallan sa kamar tana neman wani abu a office ɗin nata ta riƙe file tana ta duddubawa har ya zo ya wuce kafin ta bishi ganin inda ya shiga yasa ta dawowa ta zuba ta buɗe drawer ta ɗauko flash da yawa different colors ta zuba a jakarta  da file a hannun ta, ta nufi  corridorn su na individual office, nashi opposite ɗin na Faisal ne hakan yasa ta dai-dai ta kan ta, tare da aro wani murmurshin ta yafawa fuskar ta, ta yi knocking.

Izinin ya bada ta  shigo da sallama a bakin ta ya amsa, yana kallan ta tare da bata wurin zama, tana murmurshin sosai ta ƙara so ta gaida shi sannan ta miƙa masa file ɗin hannun ta, tana kallan flash ɗin da ya ajje shi kusa da shi ga kuma system a gaban sa da'alama sawa zai yi kuma ta shigo. 

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now