8

76 2 0
                                    

A hankali ya rufe idan sa jin an basu chance ɗin tafiya, zuciyar sa bugawa take bugu ne irin wanda ya be taɓa ji ba yayin da wani sashe na zuciyar na tunasar da shi lalle idan ya ci wannan wasan ta zama tasa, tasa ta har abada babu wani shamaki da yake ganin zai raba shi da ita. Kowa na wurin yayi shiru yana kallan sa yayin da ya buɗe idan sa ya hango Mudassir yayi masa nesa yana gaf da fara hawa Dutsen nan da yake hangowa. Wani abu ya tuna sanda aka kai shi soja, sun yi tsayuwa a rana batare da takalmi ba na tsawon wuni guda, yayi gudun a cikin ranar batare da takalmin ba kilometers a cikin sakanni, ya hau gudu Dutse ya kwana akan sa sai wannan abun ace ba zai iya ba? Da sanyin safiya? Rana bata fito ba? Yayi targaɗe yayi gudu haka ya karye ya kuma yi gudu sai wannan ace ba zai yi ba?

Ƙara rufe idan sa yayi kafin ya ja da baya ya cire takalmin dake ƙafarsa kowa na wurin kallan sa yake, batare da sun san me zai yi ba domin kowa na wurin ya yanke cewan babu abinda zai iya amma ga mamakin su sai gani sukayi ya fanna da gudu, gudu ne kamar wanda yake tsare da zaki, to daman mana su da meye basu yi gudu ba? Yayi gudu da barewa a cikin daji bare kuma nan da ya rena.

Basu yi aune ba sai gani sukayi ya fara hawa Dutsen nan kamar wani biri a cikin lokacin da ba su wuce lokaci kaɗan ba ya hau saman Dutsen kowa na wurin sai da yayi mamaki shi kuwa Mahmud be ji mamaki ba domin ya san zai iya tunda yace sun yi, kuma tunda ya fara gudun yasan lalle ba ƙaramin so yake yiwa wannan yarinyar da be san da zancen ba ma sai yanzun nan. Sai da ya hau can sama sannan ya sauko shi kuwa Mudassir ko rabin hawa beyi ba bare ya sauko. Ta inda ya hau tanan ya sauko shi yasa saukowar babu wahala. 

Koda suka dawo aka nutsu bayan an gabatar da wanda za'a aura mata jira ake ƙarfe goma tayi a ɗaura mata a auren sai dai kuma babu ɗaya daga cikin su da zai koma ko ka ci ko baka ci ba, wanda ya cin kuma idan ya tafi sai dai a aura mata ɗayan, kuma shine zai bada sadaki.  Har lokacin auren yayi be san da wannan batu ba shidai yana zaune kawai yaƙi shan komai ya rasa me ke damun sa, har sai da aka zo ɗaurin auren sannan aka ce ya miƙo sadaki kallan Mahmud yayi wanda ya wakilta a matsayin wali ɗin sa domin baya da kowa sai shi ya kalle shi shima yayi masa alamar ko sisi be ɗauko ba dafe kan sa yayi cike da takaici.

"Idan baka shirya ba ayi da wanda ya shirya mana".

Yaji wani ya faɗa wanda suka zo daga cikin baƙi, sunkuyar da kan sa yayi idan sa ya faɗa kan zoben dake ƙaramin yatsar sa, Abba ne ya kawo masa wannan zoben tun yana secondary ya gwada sai sa shi yaji a UK yaji wasu irin kuɗi bana wasa bane ashe maƙale a yatsar sa be sani ba hakan yasa ya fasa saida shi, na finger ring ɗin shi kuma yasan yayi mata yawa.

"Malam ka yi magana ka miƙo sadakin nan ayi a wuce wurin".

Wani shegen kasalallen murmurshi kafin ya cire zoben ya miƙawa Mahmud karɓa yayi shima ya miƙa masa a matsayin sadaki, wanda aka miƙawa zoben tsabar zallan mamaki kasa magana yayi jin an fara cece ku ce yasa shi cewa na diamond ne hakan yasa kowa yin shiru aka daura aure kowa ya watse kowa kuma da abinda yake tofawa albarkacin bakin sa. Koda suka gida gidan Baba Garko suka nufa wani iri yake jin sa zazzaɓi yake ji sanyi yake ji zafi ne shima kan sa be sani ba amma de ya san yana jin jikin sa wani iri.

"Ahmad".

Baba Garko ya kira shi cikin muryan nutsuwa da kwantar da hankali.

"Na'am".

"Bansan ka ba, bansan daga ina kake ba amma gashi zuwan ka zaka koma da iyali".
Yarinya
Shiru yayi na wasu daƙiƙu.

"Na roƙe Ahmad ka riƙe wannan yarinyar amana, a yanzu duk wani hakki nata ya rataya a wuyan ka ne, kaine komai nata, nauyi ne wanda ya kamata ce ka sauke shi, a yanzu aljannar ta tana kasan kafarta ne, ka taimaka mata ta wuce, ka taimaka mata da inganta tarbiyyar ta, domin bawa ƴaƴan ku".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now