40

77 1 0
                                    

Yana zaune a office bayan tafiyar Aliyu ya kasa taɓuka komai, sai tunanin Anty da yake yi, kawai kifa kan sa yayi yana jin wasu irin zafafan hawaye na zubowa a idan sa, ga wani irin ƙuna da zuciyar sa ke masa, kiran wayar sa da Abba yayi ne yasa shi, goge hawayen tare da sassauta kan sa,  wanda har wayar ta katse be samu damar ɗagawa ba sai da ta katse wani kiran ya kuma shigowa sannan ya ɗaga.

"Lafiya kake?

Abba ya faɗa cike da kulawa.

"Ehh ".

Shima ya faɗa sai dai kuma muryar sa tayi wani irin sanyi. Ajiyar zuciya Abba ya sauke ba dan ya yarda ba.

Yace, "Yau za'a shiga kotu zaka zo ne?

"Ehh Abba. Amma Yaya ƙarami yace sai Barrister ta zo".

"To ina  tunanin ta zo".

Daga haka ya kashe wayar sannan ya tashi ya kwashi kayan sa yana fita suka shiga nufi kotun shida sojojin sa. Tunda shigo harabar kotun da yaganta yaji wani irin sanyi a ran sa, sai yake gani a idan sa kamar ta sauya, tayi wani irin hasken tashin hankali har wani yellow tayi, sosai yake ƙare mata kallo daga sama zuwa ƙasa kafin ya saki wani shegen murmurshi da shi kaɗai yasan ma'anar sa. Yana shafa kai, a lokacin aka buɗe masa ƙofar sa beje inda take ba ya nufi inda su Daada ke tsaye shima yaja ya tsaya akai-akai yana kallan ta, har lokacin shiga yayi kowa ya shiga ya zauna, ita de bata ga zuwan sa ba, sai da ta zauna taji mutum a kusan ta, juyowar da zatayi suka haɗa ido, murmurshi ne ya ƙwace mata da sam bata san da zuwan murmurshin ba, irin na bazata nan, shima mayar mata yayi, sannan ya ƙara matsawa kusa da ita. Babu wanda yayi magana a cikin su har aka fara shari'ar.

Sosai aka bada shaidu iri-iri kala da kala wanda tun kafin a gama Shari'ar Yahaya Sabo yasan da cewar tasa ta rigada ta ƙare shikam, haka ma su Mukhtar da Bashar duk tsumo tsumo sukayi ido ya raina fata, wanda lawyern su kasa yin komai yayi shida mai taimakon sa, abin ya fi ƙarfin su sun kasa yin komai. Sun kasa aiwatar da komai, idan sun faɗi magana sai Ƙarami Barrister su kawo evidence, be ƙara jin ta tsinke da lamarin ba sai da yaga Mukhtar Abieyola ya zo ya bada shaida akan sa da kuma cewar shine wanda ya aika aka kashe Anty sai da ya so ƙaryatawa. amma ganin mutumin da yayi kisan real ainun ya ƙara da cewa duka gida ya aike su da su kashe suka tarar da iya ita kaɗai ce a gidan yasa suka kashe ta. Daga ƙarshe ya amsa laifin sa da ehh yayi. Aka yanke masa hukuncin rai da rai bayan kuma ya biya su tarin dukiyar da sukayi asara domin gina companyn su, gaba ɗaya rabi da kwatar kuɗin sa aka bayar, su kuma su Bashari shekara goma a gidan yari haka ma suma aka haɗa musu da kuɗin su, su kam babu abinda aka rage sai ma bin su bashi da akayi wanda iyalan su za su biya, Baba yace sun yafe, wanda sam Aliyu be so hakan ba, shi da Al-ameen har wani kumbura baki meyasa Baba zai ce ya yafe?.
Yayin da aka dawo kan Mukhtar Abieyola shima akan abinda yayiwa ƴar cikin sa da ya haifa. Nilah sam bata san ya akayi abin ya fita har haka ba, bata san ma waye ne ya kawo wannan zancen nan ba, sai da taji ana shari'ar. Inda aka nemi da fita domin jin ta bakin ta, sai da ta kalli Sajjad sannan ya ɗaga mata kai alamar eh, duk dauriya irin ta Nilah sai da ta zubar da hawaye a wannan gaɓar, a hankali ta tashi tana tafiya, hawaye na zubowa a idan ta. Taje ta tsaya.

"Kin yarda da cewar Mahaifin ki ne ya sace ki a karo na farko?

Alƙali ya tambaye ta.

Ɗaga kai tayi kawai, dan bata jin zata iya magana.

"Kina da hujjar da yasa kika ce haka?

Shiru tayi tana kallan shi kafin ta ɗaga kai.
Daƙyar ta samu ta tsaida hawayen ta sannan faɗi inda taji da yarda akayi, kowa a kotu tsit akayi ana jajanta al'amarin, wai uba ne zai sace ƴar sa, saboda kawai baya san auren da tayi wanne irin uba ne wannan? Wanne irin son zuciya wannan ɗin da har uban da haifi ƴar sa zai yi haka? Shida be san cin ta ba? Be san shan ta ba, hasalima babu ruwan sa da ita, be san ya tayi rayuwar ta ba sai da auren ta ya zo sannan zai ɗauke ta? To ta kai ta ina da Allah be sa ta gudu ba?

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now