9

82 3 0
                                    

Duk iya ƙoƙarin ta na taga ta ya kice kan ta abin ya ci tura domin wani irin runguma yayi mata ya kanainaye ta, ganin kamar ya sami bacci yasa itama ta saduda ta rabu da shi ahaka bacci ya dauke ta, takan farka akai kai taga ko ya sake ta amma ina sai ma ƙara matse ta da yake har asuba tayi bata samu wani baccin kirki ba banda ciwon jiki da ya sa mata shi kuwa baccin sa yake hankali kwance be san tana yi ba, akan kunnen ta aka kira sallah har aka shiga aka idar tana ji amma babu halin tashi, aka da aka idar sannan ya ɗan motsa jin motsin sa ya sa ta saurin rufe ido yayin da gaban ta ya fara faɗuwa.

A hankali ya buɗe idon sa ya jima yana kallon wuri ɗaya ganin ɗakin da yake sa shi tuna komai, ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ɗan yunƙura ya tashi yaji shi a jikin abu, ganin ta da yayi yasa shi ƙara kallan ta dakyau, a hankali kuma abinda ya faru cikin daren ya faɗo masa kallo ɗaya yayi mata yasan ba bacci ba take maimakon ya tashi sai ya koma ya kwanta amma wannan karon be kanainaye ta ba illah kallan ta da ya tsaya yi, kayan bacci ne riga da wando wandon dogo ne rigar kuma mai ƙaramin hannu cotton sun yi kyau sosai hular dake kan tatl ta zame hakan ya bashi kallan kitson da dake kanta ƙanana, sai da ya gama ƙare mata kallo sannan ya kai bakin sa kan ta da wani saurin ta buɗe ido jin saban wani al'amari yadda ta buɗe idon ta wani zaro ido shine ya bashi dariya. Daƙyar ya tashi ya shiga bayi yana murmurshi, yayin da ita kuma bugun zuciyar ta ya ƙaro ta kasa tantance meye wannan ɗin? Ya jima sosai dan sai da yayi wanka daga shi sai towel ya fito ita kuma tana nan kwance ta kasa tashi. Kaya kawai ya sa ganin gari ya fara haske kan carpet yaje ya tada sallah ganin ya tada sallah kuma ba nan ce gabas ɗin ba yasa ta kallan sa bata masa magana ba har ta fito be idar daga bayi be idar ba sai da ta tada sallah sannan ya idar sanda ta idar ya kammala azkhar ɗin sa.

Juyowa yayi yaga inda take yaga ba nan take kallo da'alama de nan ce gabas ba inda ya kalla ba. 'Lalle yarinyar nan' tsaki ya ja sannan ta tashi ya gabatar da sallahr yana idarwa ya kwanta anan inda ta ajje pillow amma be yi bacci ba. Ita kuma ta tashi ta fita a ɗakin. Kitchen taje ta dubo taga ko akwai abinci amma babu kuma tasan matan gidan nan ba kawo ba zasuyi muddin ba Muftahu ko Baba Garko ne ya ce musu su kawo ba. Duk baƙin gidan kuma a jiya suka koma ganin ba wani baƙi ne aka yi ba daman ba wani nisa ne da su ba. Gashi ita yunwa take ji sosai.

Fitowa tayi tsakar gidan ganin fanfo na zuba yasa ta zuwa ta kashe sai wani tunanin ya zo mata, ta shiga kitchen ta ga kayan ruwa hakan yasa ta fito ta fara kaiwa sai da ta cika abinda ya kamata ace ta cika sannan ta shiga bayi shima ta kai ta cika duk kai kawon da take yana kallon ta dan shi ba bacci yayi ba. Tana gamawa ganin babu wani abu da zatayi yasa ta kwanciya a doguwar kujerar dake parlourn amma kuma ina yunwa ta hanata kwanciyar hakan yasa ta tashin ta fito wai ko zatayi wani abun amma ko tsintsiya babu a gidan haka ta ƙara komawa ta kwanta. Gajiya yayi da yin juyin ya sa shi tashi ya fito duk da wani irin zazzaɓi da yake ji gami da yunwa amma baya san kwanciya ashe daman duk abinda yake a gida isakanci ne ya sa shi yin hakan ganin da masu yi masa ne, yanzu da babu su yayi ma mana ya gani. Ganin tana juyi yasa shi fuskantar wataƙila iyaka yunwar take ji, be yi mata magana ba ya fita. Ta ƙofar baya inda suka shigo jiya ta nan ya fita, gidan su ya nufa ya tarar da Mahmud na wanki a ƙofar gidan.

"Da sassafen kake wanki?

"Angoooo".

"Kasha ƙamshi".

Mahmud ya faɗa yana dariya, banza yayi masa.

Yace, "Kaga ka taimake ni kamin allura sannan ƙafana ciwo take wallahi".

Kallan sa Mahmud ya tsayayi jin muryan sa tayi wani irin sanyi kamar ba Sajjad ɗin da ya sani ba.

"Ya dai?

"Bakomai, kawai gani nayi gaba ɗaya ka sauya min".

Murmurshi yayi yana wani lumshe ido alamar shi kadai yasan me yake ji.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now