50

151 0 0
                                    

A zaune ta same shi a wajen kujerun da aka ƙawata office ɗin sa su kamar parlour. Zama tayi a kujerar da ke opposite da shi, yana sauraron wayar da yake yi, har ya gama ya soma yi mata bayanin abinda Yusuf yace game da su. Shiru kawai tayi ta ka cewa komai dan ita kam sam bata san abinda ta faɗa ba a ranar zai kai su da jan irin wannan asarar, idan kuma ba su nasara ba fa? Haka kawai taji jikin ta yayi wani irin sanyi, yana mata bayani amma ita ta tafi wani abun na daban. Tun yana yi yana san jin ta amsa ba, sai yaga kuma kamar hankalin ta sam bama a kan shi yake ba. Hakan yasa shi a hankali ya tsugunna a gaban ya kama hannun ta duka biyu yana kallan cikin ta.

"Kin san zaku iya wannan abun?

Girgiza masa kai tayi alamar a'a.

Yace, "Zaku iya".

"Amma..."

"Kinsan mai companyn 'UMMU'?

Girgiza masa kai tayi alamar a'a

Yace, "Macece, haka zalika wacce take kula da 'FARM GARDEN' itama mace ce".

"Me yasa za'a ce ku ba zaku iya ba?

"Ba kuma mutum ɗaya ba, har ku biyu?

"Hauwa'u".

Karo na farko da ya taɓa kiran sunan ta, tunda sake dan ko Nilah be taɓa faɗa ba, sai ya sakaya da Yaya Nilah. Haka yasa ta ji gaban ta ya wani irin faɗuwa sosai.

"Babu wanda ya taɓa kai wani mataki a rayuwar sa a lokaci guda. Duk wanda kika ya ɗaukaka a kowanne fanni, to tabbas sai da faɗi. Ba daga yin sa na farko ne hakan take kasancewa ba. Misali shi kan sa Baba da ya gina wannan companyn ba haka kawai yake ruling komai ba, ya fuskanci  ƙalubale dayawa kafin ya cimma wannan burin nasa, kuma har yanzu akan fuskantar ƙalubalen yake".

"Abinda nake so dake shine, kada ku sare, kada ku karaya, ku jajirce ba wa kan ku kawai baz ga ahalin mu gaba ɗaya. Kinyi min alƙawarin zaki yi?

Ita de ta ji shi ne kawai batare da ta san me yake cewa ba, kawai bakin sa take kallo yana maganar sai a yanzu da ya gama, bata san ma me yace a ƙarshen ba, kawai kai ta ɗaga masa hawayen da ya taru fal a idan ta ne ya samu nasarar saukowa, hannu yasa ya goge mata yana  cigaba da ƙarfafa mata gwiwa, har ta ɗan sake jiki ba dan ta ta dena ji fargaba da tsoro ba.

*****

Bayan wata biyar.

A cikin watanni biyar ɗin nan abubu da yawa sun faru, cikin kuwa harda rasuwar Yahya saboda dan wata irin uƙuba da ake gana masa ce ta kwantar shi ciwo daga nan yayi jinyar kwana uku yace ga garin ku nan, bayan ya nemi yafiyar waɗanda yayi wa abubuwa, ta hanyar kiran ƴan jarida da akayi ya faɗi ko shi waye da yadda yake gudanar da kasuwancin sa da haramtacciyar hulɗar kasuwancin sa da komai sai da ya faɗa, daga ƙarshe ya nemi yafiyar ɗumbin jama'ar da yayi laifi. Mutane da yawa sun yafe masa dan abin tausayi ne duba ga yarda ya koma ya lalace da shi. A ranar kuwa, Muddansir kwana yayi yana kuka yana nemawa Mahaifin sa gafara, washegari aka ce ya rasu, har jana'izar sa sai da su Daada suka je, ba ƙaramin dauriya Muddansir yayi ba sosai ya bawa mutane tausayi, haka ma itama Mahaifiyar sa, dole taji ba daɗi har kuka sai da tayi itama, a ranar da ya rasu kuwa labarin mutuwar sa ya karaɗe ko ina abun ka da socail media, tsoron Allah ya ƙara shigar mutane masu imani, kowa ya ji mutuwar sa musamman da aka gama jin labarin sa da komai nasa. Abin a tausaya masa ne. A bangaren su Dr. Ismail suma haka abin yake, sun yi kuka sun yi nadama tun ba'aje ko ina ba. Sun rasa ina za su kan su da wannan abun kunyar da suka aikata, musamman da Dr. Ismail yaji wai ƴar sa anfasa auren ta a ranar ɗaurin auren nata, sai asibiti aka kai yarinyar tsabar yarda labarin ya dake zuciyar ta, kwanan ta ɗaya tal ta koma ga mahaliccin ta, wannan abun ya fi masa zafi sosai. Dr. Bilya kuwa ɓarayi ne suka shiga gidan sa suka cinnawa gidan wuta, daƙyar iyalan sa suka samu nasarar guduwa daga nan be ƙara jin ɗuriyar su, daman sun je sun same shi sun sanar da shi ba zai ƙara jin su ba har ya mutu. Shi ba rashin su bane damuwar sa, irin maƙudan kuɗin dake cikin gidan sa ne matsalar sa, gashi an ƙone gidan. Ya san kuma sun ƙone. Shine yake cin sa a rai. Mukhtar Abieyola kuwa an fito da shi bayan da Daada ya roƙi alfarmar zai biya masa kuɗin fansar sa, da sa hannun ƙaramin dan Barrister biris tayi da zancen da ya je ya same ta dashi, ko uhm bata da shi ba. Bare yasa ran za tayi wani abu, shi kuma Daada yayi haka ne dan Mahaifin Nilah ne, koba komai Nilah bata cancanci haka ba, a rayuwar ta, ya kamata ace a yanzu ta san daɗin Mahaifin. Haka shima Usman an sake shi bayan an kira Yayan sa ya zo ya tafi da shi wanda ya san da cewar ya kaɗe har ganyen sa.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now