10

79 1 0
                                    

Sajjad yana nan a kwance ya ga fitowar ta yau kuma doguwar rigar atampa tasa tayi ɗaurin baya ta yafa mayafi a kafaɗar ta, taɓe baki yayi ya rasa uban wa take sa wa mayafi shidai ya san mijin ta ne sai ta tayi ta sa ka masa wani zubulale mayafi a gida ko da be zama mijin ba?

"Ina kwana?"

Ta gaida shi. Banza yayi mata ya tashi yaje ya ɗauko cups da tea spoon da kayan shayi ya ajje yaje ya zauna ya haɗa musu shayin ya tura mata nata kallan da ya mata ne yasa ta tashi ta sauko inda yake.

"Idan ba zaki ci ba ki tashi ki bani waje".

Ya faɗa batare da ya kalli inda take ba, da ace ba su kaɗai ba ne zatayi tunanin ba da ita yake ba, amma sanin su kaɗai yasa ta sanin da ita yake. Ji tayi idan ta na ciccikowa da ruwan hawaye batare da ta shirya yin haka ba sam bata san ma zata yi kukan ba, bata kuma yi aune ba sai jin zubar su tayi a kan hannun ta. Ba zata iya cigaba da wannan zaman ba daga jiya zuwa yau kawai? Ya sa ta kuka sau nawa? Anya kuwa?

"Me nayi? 

"Da kasan haka zaka min da baka aure ni ba".

Ta faɗa tana share hawayen ta.

"Kina jin ba daɗi?

Ya faɗa yana tsare ta da ido, itama kallan sa tayi da idan da yake ƙara fitowa da wasu hawaye.

"Tambaya na ma kake ?

Murmurshi yayi yana cigaba da cin abincin sa yayin da ta kafe shi da ido, sai da ya cinye lomar da yasa a baki ya kora da shayin sa.

Yace, "baki san babu daɗi ba? Sai da aka miki kika san ba daɗi?

Sunkuyar da kan ta ƙasa tayi, tana share hawayen ta.

"Be kamata ace kin ji ba daɗi ba tunda abinda kike yi ne aka miki".

Daga na be ƙara magana ba itama haka amma kuma kukan da ta yaƙi tsayawa banda share hawaye babu abinda take yi, har ya gama ya tashi ya shiga ɗaki ya bar ta anan tana kuka. Sosai yaji ba daɗi amma kuma yasan tunda ta fara magana da kanta zata gane rashin maganar ta ba dai-dai ne ba. Itama taji yarda ya ji.

Daƙyar ta rarrashi kan ta tayi shiru, ta jawo  shayin da ya haɗa mata rabin cup kamar nasa da ya haɗa haka ma abincin be wani ci dayawa ba duk da abincin daman na cin mutum biyu ne, kallan abincin tayi tana tunanin wanne irin abu ne wanna? Gashi de dankali take gani amma bata san da meye ya haɗa ba. Ɗan kaɗan ta ɗauka a fork ɗin da ya ci ta kai bakin ta, ta tauna daɗin da ta ji ne yasa ta ƙara janyo gaban ta, ta fara ci sai da ta ci ta ƙoshi ta kora da tea ɗin ta. Tashi tayi ta tattare wurin sannan ta kai kitchen taga yadda aka tsara komai  an ajje komai a muhallin da ya da ce. Fita tayi ta wanke kayan da suka ɓata sannan taga gidan a share tsab sai taji kunya ta kamata wai ace shine ya mata wannan abun? Ita kuma tana kwance tana bacci. Komawa tayi ɗaki domin ɗaukan wayar ta amma bata gani ba shi kuma yana zaune a kan gado ya ƙara yin wani  wankan banda wanda yayi ɗazu tana bacci yana ɗaure da towel ya buɗe wardrobe ya zuba mata ido daga inda yake zaune. Ɗan kallan sa tayi da sauri ta ɗauke idan ta domin har ga Allah ya bata tsoro yarda baya da kayan nan bata taɓa ganin namiji haka ba, saurin ja da baya tayi zata koma.

Yace, "Kaya na".

Kayan shafan sa yake nufi kuma sarai ya gan su akan mirror amma tsabar san neman magana irin nashi ne yasa shi tambayar ta. Daburcewa tayi ta fara inda inda daƙyar ta iya fito da kalman ga su can daga haka yayi waje. Tashi yayi ya nufi inda ta nuna masa yayi ƙwafa.

"Zakiyi biyani yau yau ɗin nan zai san kina sa min mayafi a gida".

Sai kuma yayi shiru yana shafa mai ya kalli kan sa madubi, yayi murmurshi.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now