47

50 0 0
                                    

Sai da akayi Sallahr la'asar sannan ta tashi, a lokacin dawowar shi daga masallaci kenan, yana zaune yana karatun Alqur'ani a waya. Bata masa magana ba har ya kai ayar da zai kai sannan ya ɗago ya kalle ta, tashi yayi ya koma kusa da ita yana ɗaura kan ta akan cinyar sa tare da ajje wayar a gefen su.

"Sannu".

Jinjina masa kai kawai tayi, kafin hawaye ya zubo daga idan ta, ya sauka akan cinyar sa. Tana kallan shi kamar yadda shima yake kallan ta.

"Shikenan? Na rasa baby na?

"Babyn da bakya so ba ai murna ya kamata kiyi".

Duka ta kai masa, yasa hannu ya tare yana murmurshi, sannan yasa hannu ya goge mata hawayen dake zubo mata.

Yace, "Kiyi addu'ar Allah yasa hakan shi ya fi Alkhairi. Sannan Allah ya bamu mai Albarka ko?

Shiru tayi mata amsa ba, amma a zuciyar ta kam, ta amsa wani irin san cikin take yi sosai, wanda itama bata san iya adadin san da take masa.

"Daman kasan ina da ciki?

Jinjina mata kai yayi.

Yace, "Shiyasa nake maki dariya a duk sanda na kalle ki".

Wani dukan ta kai masa tana samun sa a ƙirjin.

"Yo haƙuri. Na dena".

Ya faɗa yana dariya, sosai yayin da ta ɗauke kan ta daga kallan sa.

Yace, "yanzu nasan ina ƙara yi zan sa..."

Rufe idan ta tayi tana sakar masa ihu alamar ya isa.

"Tunda ke ɗin akwai ki da saurin..."

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wai dan Allah Ya Sajjad meke saka haka?

Sosai kai yayi yana kallan ta. Sanan ya sunkuya ya sakar mata light kiss.

"Kinsan wani abu?

Tana kallan cikin idan sa.

Yace, "Ina san ki".

Tsayawa tayi kawai tana kallan shi, tare da ƙifta idan ta, yayin da ya ƙara tabbatar mata da kalmar da ya kuma furtawa.

"Ke kallan kuma fa".

"Ni kuwa kaga bana san ka".

Murmurshin mai haɗe da dariya ne ya kusa ƙwace masa, yana daura kan ta a pillow ya tashi be ce komai ba, ya wuce toilet da ruwan zafin da ya dafa ya zo ya haɗa mata ruwan wanka, sannan ya dawo ya cire ya fara ƙoƙarin cire mata kaya.

Tace, "Haka nace maka ba zan iya ba?

"Wankan ma ni zan miki".

"Amm.."

"Yaya Nilah Pleaseeeee".

Ya faɗa yana haɗe hannun sa. Tsaf ya shirya ta yayi mata komai abin ta, ya zo ya haɗa mata ruwan shayi mai zafi tasha sannan ya zuba mata abincin yana bata. Turo ƙofar da aka yi ne yasa shi kallan ƙofar Abba ne ya shigo bayan sa Aliyu. Be ga sauran ba, ganin fuskar Abba da yayi yasa shi jan jinin jikin sa, ya dauke kan sa da sauri ya mayar ga abinda yake, ya ɗebo abincin ya bata, kasa amsa tayi saboda ganin Abba da tayi, hakan sa ta sunkuyar da kan ta ƙasa cike da kunya. Ganin haka yasa Sajjad ajje abincin ya miƙe tsaye lokacin Abba ya shigo bakin sa ɗauke da sallama dan sai da ya gama ƙare wa Sajjad wani irin kallan sa Sajjad ne kawai zai iya fassara shi.

"Sannu Yaya Nilah".

"Abba ina wuni".

"Alhamdulillah ya jikin naki".

"Alhamdulillah. Anyi taro lafiya?

"Alhamdulillah Dear. Ya kike jin jikin?

"Da sauƙi sosai".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now