37

61 1 0
                                    

Babu abinda ya ke sai safa da marwa a cikin ɗakin sa tun dawowar su daga asibiti bayan sallamo ɗan sa. Abin duniya gaba ɗaya ya haɗu yayi masa yawa, be taɓa tsammanin aikin su zai samu matsala ba a cikin ƙanƙanin lokaci ba sai a yanzu da komai yake nema ya cakuɓe masa. Ga rashin lafiyar ɗan sa da yake jin ta har cikin zuciyarsa, be san ya zai yi ba, be san cewar haka ake jin fargaba sai jiya da yaji labarin kama su Sagiru sa akayi shima Jibrin ne ya faɗa masa abun ba ƙaramin razana shi yayi ba, ko da aka kama su Dr. Ismail hakan be ɗaga masa hankali ba kamar yarda aka kama su Sagiru.

Samun waje yayi ya zauna kafin ya fara lissafin iya adadin dukiyar sa, ganin lissafin bame ƙarewa bane yasa shi tashi salin alin ya haɗa muhimman takardun sa tare da ɗaukan passport ɗin sa ya yi parlour, yana zuwa yaga matar sa da Ɗan nasa a parlour alamar ba su shiga ɗaki ba kenan.

"Ina zuwa haka?

Be je ga bata amsa ba aka yi knocking, zuwa tayi ta buɗe ƙofar batare da ta tambayi waye ba. Wasu irin murɗaɗan samudawan Sojoji ne, suke neman sa, ita kan ta, ta tsorata bare kuma shi kan sa da yayi laifin, bata je ga ja ba tace yana nan, ta basu hanya suka shigo, basu yi wata wata suka ɗaga shi sama shi dukan sa, babu tsayawa wani You are under arrest ko wani takarda ko wani abu, tsayawa magana wannan sai ɗan sanda abokin kowa amma banda soja aikin su kawai suke da cika umarni doka ɗaya ce idan ka karya ta shikenan hukunci za su dauka babu ruwan su. Yanzun ma haka ne, suna zuwa sukayi sama da shi dan kada ya ɓata musu lokaci. Haka iyalan sa da masu aikin sa  suna ji suna kallo aka sanƙa mashi a mota suka tafi.

Ko a mota idan sa yayi tsilli tsilli yana cilla idanu, shi kam yau yaga tashin hankali, mai suna tashin hankali to da shi waye ya kai shi? San kuɗi ko kuma me? Ba kowa ne ya je fasu a halin da ake ciki ba sai su Dr. Ismail acewar sa kenan. Ganin basu ɗauki hanyar airport ba yasa shi sanin lalle kashin sa ya gama bushewa shi yaushe raban sa da yayi tafiya mai tsayi irin wannan, jide Kaduna yarda ya mayar ta kamar me nan da nan yaje ya dawo, sauƙin sa ɗaya sun bar shi yayi bacci san ran shi har suka ƙara so Kaduna.


~~~~~~~

Yusuf da Hafiz kuwa ba su san cewar an kama kowa ba a companyn su, kuma an sallamo Anty, daman su washegari kasancewar Jummu'ah ce ba su ba za su aiki ba, shiryawa suka yi za su je Bauchi. Dan haka da asuba suka fita, suna yin Sallah suka ɗauki hanyar Bauchi, sun yi gudu sosai dan haka suka isa sa wuri, tara ma a can tayi musu daman su idan suka zo Jigawa kamar sun zo ne, kai tsaye gidan su Bintu suka nufa suka nemi a aurawa Yusuf ita dan ko ƙudurin Inna akan auren Sajjad da ita Bintun, baban Bintun be wani ja ba ya yarda dan Mahaifin Bintun mutum ne mai fahimta da  dattako. Suka siyo goro da alawa da kuma dabino, sai da suka jira aka yi sallar Jummu'ah sannan suka ɗaura auren, ba ƙaramin daɗin hakan yayi musu ba, daman da zulumin zai yarda ko kuwa ba zai yarda ba, sai da suka kamo hanya kuma ya fara zulumin ita kan ta Bintun nan ɗin ma Hafiz ne ya cigaba da ƙarfafa masa gwiwa.

Kasancewar a wannan tafiyar sun yi tsaye-tsaye tsayawa yin Sallah yasa ba su dawo da wuri ba ga kuma hold up, sai bayan Isha suka dawo, gida suka wuce domin su sanar da su Abba, sai dai abinda basu sani ba shine, suna tafiya Mahaifin Bintu ya kira ya sanar da shi komai. Suna zaune suka tarar da su a main parlourn na gidan kowa da kowa ƙwan su da kwarkwatar su kowa ya hallara an zo dubiyar Anty. Mata sun yi gefe abin su haka ma mazan a gefe a bin su yara ma haka.

Yusuf na shigowa suka fara ango kasha ƙamshi, tsayawa yayi kawai yana kallan su, kafin ya samu waje ya zauna.

Yace, "Yanzu waye ya faɗa musu wannan abun dan Allah?

"Kai a tunanin ka baza mu ji ba?

Al-ameen ya faɗa.

"Yaya Al-ameen yaushe kuka shigo garin?

"Wallahi bari kawai, Hajiyar su ce ta zo ta ɗauki Unaisa wai ta kusa haihuwa shine fa muka dawo muma".

"Kuma aikin fa?

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now