48

55 1 0
                                    

A kwance ya same ta, ta juya bayan ta, hakan yasa shi zuwa da leƙa fuskar ta, ganin tana bacci yasa shi zama a kusa da kan ta. Yana tashin ta. Buɗe idan ta tayi ta kalle shi.

"Ki tashi mu tafi gidan mu".

Ai bata san sanda ta wani ware idon ta tana kallan shi ba.

Tace, "Gida fa?

Yace, "Ehh".

"Ni ba zanje ba. Ba zan bika ba".

"To nikam Allah ya gani nagaji".

"Nikam ba inda zan je".

"Ki yi ta zama, ba zan ƙara ce maki ki taho mu tafi ba. Kuma na dena miki magana".

Tashi yayi ya zai fita, har ya je bakin ƙofa.

Tace, "Zanje gidan su Zainab, zan mayar mata ƴar ta".

Wani kallo yayi mata ya fice. Kaɗa kai tayi itama ta fito, ta shiga kitchen ta ci abinci kaɗan sai ga Bintu ta biyo mata ta zo su tafi, hakan yasa ta zuwa ta ɗauko Hijabi. Koda suka fito domin tafiya babu yaran da aka tambaya ina suke Barrister tace Sajjad ne ya tafi da su. Girgiza kai kawai Nilah tayi dan ta san abinda yasa yayi hakan. Ita kuwa bata shirya kwasar kunyar nan ta sa ba, ba zata iya ba, idan shi Iyayensa ne ita kuma fa? Abubuwan da za'a faɗa akan ta har tarihin ta sai ya bi. Gata bafulata, fulani kuwa da tsoron gudun magana uwa uba kuma kunya. Har su Bintun suka tafi ba su ba labarin su.

******

Muddansir yana zaune kamar kullum yau de kam ya samu ya fito, don har ya fara jin daɗin wajen, amma yau be je ko ina ba, shi kaɗai ne a ƙofar gidan na su. Wata budurwa ya gani tana waya  tana juyawa alamar de kwatance ake mata kuma bata san wajen ba. Ganin sa yasa ta duso inda yake, tunda ta taho yake kallan ta, tunanin inda yasan fuskar kawai yake yi, ya kuma rasa a'ina ne yasan fuskar nan, amma tabbas yasan ta.

"Assalamu alaikum, dan Allah ina neman wani gida".

"Wanne gida kenan?

"Gidan Maza".

"Gidan Maza?

Ya maimaita yana kallan ta, gyaɗa masa kai tayi alamar eh.

Yace, "Nidai gidan mazan dana sani gaskiya ba'a anan unguwanni yake ba".

"Nan ba Badarawa ba ne?

Kallan ta yayi dakyau.

Yace, "Nan fa Unguwar dosa ce".

Wani irin ƙwalalo ido tayi tana kallan sa cike da mamaki.

Tace, "Innalillahi".

Ajiyar zuciya ta sauke. Tana masa godiya ta ɗauki wayar ta dake ringing.

"Nilah ashe ba unguwar na zo ba".

Ta faɗa tana yin gaba, da sauri Muddansir ya jiyo jin sunan da ga ambata, kenan ƙawar nan ta tace? Tashi yayi da sauri ya nufi inda take tana tafiya tana wayar, gama wayar kenan.

Yace, "Naji kince Nilah".

"Ehh".

Ta tsaya da tafiyar tana kallan sa.

Yace, "Ina nufin, Nilah ta can Gassol? Gidan Baba Garko?

Da mamaki take kallan shi.

Tace, "Eh, ko kasan ta ne?

Yace, "Baki gane ni ba?

Girgiza kan ta tayi alama a,a.

"Amma ina ma kallan sani ne kawai. Amma ni bansan ka ba".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now