27

59 1 0
                                    

Sauke ajiyar zuciya tayi, sannan ta taka a hankali taja kujera ta zauna tana ƙara kalle office ɗin da kyau, idan ta ne ya sauka akan gwangwanin madarar da ke kan table ɗin hakan yasa ta tashi tare da zagayawa tana dubawa ga kuma kuɗi a ciki nan tana iya hangowa, ajjewa tayi da sauri jin ana alamar buɗe ƙofa ta dawo ta zauna harda kwanciya da kifa kai irin ace baccin tayi shiyasa ta kifa kan ta saboda kada aga idan ta na ƙiftawa. Dukan table ɗin yayi ne yasa ta tashi tana wani yatsine fuska irin baccin nan nake aka tashe ni, duk da ba'a ganin fuskar ta saboda face mask ɗin da ta saka, amma ya ga alamar kamar bacci take.

Beyi mata magana ba kamar yadda itama ba tayi masa ba, wayar ta kalla taga time, ashe lokaci ya ƙure haka. Tana nan zaune sai ga wani nan ya shigo da Mug da cookies kamar de kullum, ajiyawa yayi ya fice, wani ya kuma shigowa.

"Ka nuna mata Office ɗin ta".

"Yau Farida bata zo ba".

"Me ruwa na kuma?

"Da kace na je na same ta?

"Ohh! Yi haƙuri na manta".

Jinjina kai kawai yayi, daga nan babu wanda ya kuma magana. Sectary ɗin sa ne, wanda a yanzu ya koma ƙarƙashin Yusuf kasancewar Matar Hafiz ce sectary ɗin su, su duka biyun, yanzu kuma Nilah ce ta maye gurbin nasa. Binsa tayi aka nuna mata nata office ɗin, daban a gefen nasa amma nata be kai ko rabin girman nasa ba, sai dai yana da kyan shi sosai, sai wata ƙofa da ya nuna mata wacce zata shiga ta shiga ta office ɗin sa, sai kuma secrets abubuwa da ya nuna a office ɗin. Godiya tayi masa ta zauna ta fara dubawa sai dai babu system, Allah yasa ta taho da system ɗin companyn su, amma bata zo da ita ba yau. Cigaba da tayi da duba office ɗin tana duba ko wanne file dake gefe daban a cikin shell ɗin su, ta je maida wani file ɗin ya faɗi takardun suka watse ta tsugunna tana kwashewa ta ci karo da wani hoto, Jibrin ne da Sagiru suka ja hankalin ta hakan yasa ta ɗaukan hotan ta ware daban, ta ajje komai ta koma kan kujerar ta, tana nazarin hotan duka mutanen bata san su ba sai su Jibrin ɗin, sai kuma wasu mutane guda uku suma da'alama manyan mutane ne su ɗin. Wayar ta ta ɗauka ta kira Faisal ta sanar dashi abinda ta gani sannan ta tura masa hotan.

"Naji kuma suna cewa za su haɗu anan Abujan".

"Ko suna ɗaya daga cikin baƙin da za su zo?

"Ka sa ido akan su sosai dan Allah".

"In Sha Allah kar ki damu".

"Nagode".

Daga haka sukayi sallama, gashi ta baro system ɗin a gida, tana nan zaune sectary ɗin ya dawo ya fara mata bayanin aikin ta ya kuma faɗa mata duk wani schedules na su na yau ta fahimta iya fahimtar ta duk da ba duka ta gane ba amma ta gane wasu abun.

"Oga baya dan ɓata lokaci, baya jira, baya san magana da yawa duk naga ke ɗin kamar baki da hayaniya".

Ya ƙarashe da tsokana, ɗan murmurshi tayi masa duk da har yanzu tana ƙunshe da face mask.

"Nagode".

"Sunana Sadiq".

"Ni kuma Hauwa'u".

Har zai tafi sai kuma yaga ya dace ya sanar da ita. Hakan yasa shi ƙara zama yana fuskantar ta ganin haka ita kuma ta nutsu taji me zai ce.

"Hauwa'u".

Kallan sa tayi alamar inaji, shi kuma ya ɗan sunkuyar da kai, kafin ya ɗago ya kalle ta.

"Ki sani cewa duk abinda zakiyi kiyi gaskiya a ciki. Na sha samun hare-hare daga mutane da dama da kuma na zauna nayi tunani sai naga duk mutum ɗaya ne ke kawo min harin shiga hallaka ma'ana na ci amanar Sir. Sajjad".

Ɗan murmurshi takaici yayi.

Yace, "Sun sace min Mahaifiyata, saboda naƙi amincewa da ƙudirin su".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now