46

61 1 0
                                    

Hafiz da Yusuf suna zaune a gidan Hafiz haka ma Matan su, da yaran suna wasan su yau ba je wajen aiki ba, dan hutawa suke sunce sai ranar da Sajjad ya koma shima suma za su koma, Babba ne kawai yaje dake shi ne Babba kuma mai haƙuri. Hiran su suke ciki da raha suna kallo. Suka ji wani irin knocking ɗin tashin hankali ana yi babu sassauci dan sai da yaran suka firgita, Bintu ce ta ɗauke su tana rarrashin su. Yayin da suka tashi tsaye suna kallan juna alamar waye. Jin har yanzu ba'a dena ba ya sa zuwa da leƙawa ta hole amma basu ga kowa ba, kuma ba'a dena ba. Hafiz ne yayi ƙarfin halin zuwa da buɗewa ya leƙa ga kowa ba sai da ya fito duka yaga Sajjad, wani banza tsaki yaja.

Yace, "Wai daman kai ne?

Jin maganar Hafiz yasa su fitowa su dukan su, suna kallan Sajjad dake musu dariya.

Yusuf yace, "Amma Sajjad Allah ya shirya ka".

"Ameen".

Yace yana dariya.

"Gayu an razana".

Ya faɗa yana miƙa hannun yana karɓa yaran da sukayi shiru.

Yusuf yace, "Yaya Nilah shine ko ki hana shi?

Kafin tayi magana yace, "Sai aka ce maka ni mijin tace ne ko? Sai ta hanani abinda nake so".

Bintu tace, "Rai de".

"Ke ina wasa da ke?

Ya faɗa irin ba wasan nan.

Yusuf yace, "Kaga kada ka zo har gida ka ciwa mata ta mutunci. Nima bashi ne da ni ba".

"Matsoraci de".

Hafiza tace, "Sannu da zuwa shigo daga ciki. Kar ki biye su".

Ta faɗa tana kama hannun ta, ɗan murmurshi tayi tana binta a baya sannan suma suka rufa musu baya, a kusa da ita Sajjad ya zauna sosai har suna gogan juna, ɗan matsawa tayi kaɗan shima ya ƙara matsowa. Ganin ba haƙura zai yi ba yasa ta gaida su Yusuf suka amsa cike da fara'a suka gaisa da Bintu lokacin Hafiza ta zo ɗauke da tray a hannun ta. Ta janyo center table ta ɗaura komai a kai.

Sajjad yace, "Da baki sha wahala ba ai".

"Bakomai fa".

Ɗan jinjina kai kawai yayi.

"Me zaki ci?

"Na koshi".

Hafiz yace, "Daga tarewar taka shine zaka fara yawo?

Yusuf yace, "Kai ma ka faɗa".

Sajjad yace, "Kullum sai mun zo wallahi sai dai ku gaji da mu".

Hafiza tace, "Wanne gajiya kuma?

Yusuf yace, "Ina ne gidan? Wacce unguwar?

"Nan unguwar, nan layin ba nisa".

A tare suka kalli juna Hafiz da Yusuf alamar ko wannan gidan?

Yusuf yace, "Lalle Abba, wato de dole sai mun yi rayuwa da Sajjad".

"Ko kuna so ko bakwa so ba".

"Sajjad sai shiriya".

Suna nan a wajen har aka yi Sallah Azahar suka je suka yi sannan yace tafiya za su yi babu yadda ba'ayi da shi ya tsaya ya ci abinci ba yace a'a za su dafa idan sun je can.

~~~~~~

Muddansir na zaune ya naɗe hannun sa yana kallan Mahaifin sa dake zaune a gaban sa, babu wanda ya cewa da kowa komai duk, tun biyu saura yake zaune a nan yana kallan sa har ƙarfe uku ta gota suna a baka. Kowa sai kallan kowa yake, shi Muddansir be ce komai ba, shima Baban nasa be ce masa komai ba. Kawai kallan juna suke. Sai da aka zo aka ce musu lokacin ya ishe su haka, an basu minti biyu suyi sallama. Sai a lokacin Muddansir.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now