11

78 2 0
                                    

Sai da akayi azahar ya dawo ganin duhu yasa shi buɗe labulayen parlourn, ya shiga ɗaki, tana kwance akan carpet ɗin dake ɗakin ƙaramin Qur'ani a hannun ta tayi bacci da'alama karatun take yi tayi bacci, labulen ɗakin ya ɗage ya ƙara kusa da ita ya tsugunna ko hijabin dake jikin ta bata cire ba, a hankali ya sa hannun sa ya cire Qur'anin tare da cire mata  mata hijabin  da gyara mata kwanciyar  ta, yana ƙare mata kallo, har wani motsa baki take tana bacci, besan sanda yayi murmurshi ba ya ɗan shafi fuskar ta tare da kai bakin da kan goshin ta ya bata wani irin sassanyan peck ɗin da ya sata motsi, da sauri ya miƙe tsaye ganin motsin ta bame ƙarewa bane, can kuma sai yaga ta gyara kwanciyar ta, ta cigaba da baccin. Ajiyar zuciya ya sauƙe yaje ya rage kayan dake jikin sa yasa marasa nauyi har ya fara tattare kayan da ya cire, sai kuma ya wurga da su a tsakar ɗakin ya fita parlourn abincin da ya gani yasa shi zama dirshan ya kwashi gara ba laifi abinci ya masa daɗi duk be wani ci dayawa ba amma haka ya kashe rabi da kwatar abincin, abincin da zai ishe su har dare idan ma be musu yawa ba, amma haka ya kwashe ya fita dashi yaje ya bayar, ya bar mata ɗan kan ta. Yaje ya kwanta akan gadon.

Buɗe abincin tayi da niyyan ta ci kawai taga wani ɗan abinci da ya bar mata, wani irin takaici taji ya riƙe ta, wannan ɗan abincin? Ƙin ci tayi ta sami waje ta zauna sai kuka, kukan ta ne ya tada shi daga bacci ya ta so ya tsaya a ƙofar ɗakin.

Yace, "Malama kiyi kukan ki a hankali. Mutum yana bacci kin tashe shi".

Ƙara volume ɗin kukan ta tayi, yaja tsaki ya zo ya zauna ya ɗauki abinci ya fara ci, wani irin abu taji yana mata yawo a maƙoshi gashi de kukan take amma kamar ba yi bata take tsabar haushi da takaici, maƙoshin ta har wani ɗaci yake mata. Shi kuwa abincin ya cinye tas ya ɗauki ruwa ya sha ya miƙe akan kujera ya kulle idon sa, ɗan kan ta tayi shiru ta koma sauke ajiyar zuciya a haka wani bacci ya yi gaba da ita, jin shiru yasa shi buɗe idan sa ya kalle ta, ta kuma sanya hijabin, ƙwafa yayi a ran sa tare da kaɗa kai alamar zaki sani.

Haka ta kwana da yunwa ita bata yi wani abincin ba shima be yi ba, washegari shine ya kuma gyara musu gidan ya ɗebar musu ruwa ya siyo kayan cefene ya musu break fast duk da har yanzu ƙafar sa bata dena zafin ba sannan kuma be dena jin zazzaɓin ba amma haka ya kuma daurewa yayi komai, ruwan zafin da ya dafa jiya batayi amfani da shi ba, da shi yayi amfani yayi wanka sannan ya dafa wani ya kai mata ƙofar toilet dan wai ta gane cewan na tane fa, parlour ya dawo ya zauna yana fama jiran ta duk da ya wargaza ɗakin kamar yarda yayi jiya, yana nan ta fito fuskar nan ta kumbura alamar ta kuma cin wani kukan kenan.

"Ina kwana".

Ta faɗa ganin yadda ya tashi zaune.

"Lafiya".

Ta samu aka amsa mata, haka nan taji wani irin sanyi a ran ta, koba komai ya fara kulata ai. Kamar yadda jiya ya haɗa haka ma yau ya haɗa musu tea ya tura mata, yau dai anci sa'a tare suka ci amma kowa yayi shiru kowa da abinda yake saƙawa a ran sa ita farin ciki ne fal a ran ta amma iya ka kan ta take ganin ta sani, yayin da shi kuma ya san tun farkon amsa gaisuwar ta ga wani irin sauyi da tayi.

A haka suka kasance har tsawon sati guda, dake yanzu suna fita asibitin Gassol da wuri yake tashi ya kimtsa gidan yayi musu abinci ya ci nasa ya bar mata, ya fice duk tana bacci, magana kuwa watarana idan yaga daman ya amsa gaisuwar ta wata rana kuma ya yi biris da ita, kuma kullum da daddare indai ta kwanta a ƙasa shike ya ɗauko ta ya rungume abar sa su kwanta ya lura tana da nauyin bacci sai dai kana tashin ta zata tashi. Waya kuwa da ƴan gida yana kiran su da wayar Mahmud duk sanda suka je Gassol mantawa yake yi aiki ne yake shan kan su kuma basa tafiya da wani kuɗi sosai ga ATM ɗin sa manta shi yake duk sanda ya ce zai siya sai ya manta, kullum sai yayi waya da Yaya Aliyu amma be taɓa sanar da shi cewan yayi aure ba haka shima Yaya Aliyun be taɓa sanar da shi an kai Daada prison ba.

Yau ta kasance weekend ne a gare su hakan yasa shi, kwaso kayan su duka ya wanke tas bayan ya ɗaura sabuwar igiyar shanya a tsakar gidan, har inner wears ɗin ta ya wanke tare da na shi suma ya shanye su da ban. Ya  kwaso kayan wanke-wanke yana wanke wa, ta fito sanye da kayan baccin ta riga da wando masu laushi sai hular net da ta sawa kan ta bata ga hijabin ta ba hakan yasa ta fitowa dan tunanin ta ko ya fita ne, amma tana fitowa taga irin aikin da yayi, wata irin kunya ce ta rufe ta ganin  bras ɗin ta a shanye tare da pantie ɗin ta, panties ɗin da take wankewa kullum amma sai da ya kwaso harda wanda bata taɓa sawa ba, bata san sanda ta galla masa harara ba, shi kuwa yana ganin ta, sai ta bashi dariya kawai sai yaji murmurshi yana cigaba da wanke-wanken sa, sai ma fara waƙar sa.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now