15

61 2 0
                                    

Meeting suke amma idan ka gan shi zaka ce sam baya daga cikin masu meeting ɗin, yana zaune ne yayin da yake juya biro a kan jotting book ɗin dake gaban sa, sam fuskar sa ba zaka ce ba ainahin abinda yake ciki ba,  sai dai kuma tsab yana sauraren bayanin kowa, yana kuma jin abinda kowa yake cewa. Ganin sun gama magana yasa shi kallan wanda yayi magana na ƙarshe akan share ɗin da mutane suka sa a companyn, akan cewa idan har ba'ayi abinda suke so ba, wanda suka sa share ɗin su masu yawa sunyi za su dawo su riƙe companyn, duk cikin su babu wanda yayi maganar amfaniin companyn nasu sai wata mata wacce dattijijuywa ce tana aiki da companyn ne tun sanda Baba yana nan ita kaɗai ce tayi maganar da ya gamsu da ita ɗari bisa ɗari.
   A hankali ya sauke kan sa a kan na kusa da shi batare da ya ce komai ba, haka ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ya dawo da kallan sa ga na ƙarshen wanda yake Bature ne.

"Share nawa kasa a companyn nan?

Tambayar ta zo masa a bazata, ɗago da kan sa yayi ya kalle shi, duk da cewan da Hausa yayi maganar kuma ya ji shi sarai, amma tambayar da kuma sanin inda yasan yana jin Hausa ne be sani ba.

"35%".

Murmurshin gefen baki yayi.

Yace, "Za'a biyaka, bama kai kaɗai ba, kowa da yake da share a cikin wannan companyn za'a bashi abin sa. Daga yau bama buƙatar share ɗin kowa".

Ya faɗa yana bin su da ido, ɗaya bayan ɗaya, ganin babu mai cewa wani abu yasa shi tashi a nutse ya fice. Da kallo suka bishi har ya fice daga cikin conference ɗin sannan masu magana suka fara yi a junun su. Yana fita elevator ya hau zuwa hawa na shida inda ya kasance anan ne office ɗin sa yake, sectary ɗin sa ne ya shigo ya fara masa magana yayin da shi kuma yake duba wasu files gefe kuma system ce ya buɗe, ba'a jima ba akayi knocking ƙofar ya bada izinin shigowa, wani ne sanye da kayan waiters hannun sa riƙe da tray ya ajje Mug ɗin da cookies sai cake ya fice. Sai da sectary ɗin sa ya gama masa bayani sannan ya ɗauki Mug ɗin ya fara sha a hankali kafin ya janyo system ɗin sa ya fara dubawa, sannan ya tashi yaje inda curtains suke yasa hannu ya janye glass ɗin dake wurin ya bayyana yasa hannu a aljihu ɗayan kuma yake shan coffee ɗin da shin. Yana kallan kowa dake harabar wurin, da kuma wasu building guda biyu amma basu kai nasa ba, ɗayan hawa huɗu ne ɗayan kuma plat ne, duka wanda zai shiga wurin yana kallo haka zai ga fitar sa wanda ba zai shiga nasa ne kawai bazai gani ba. Amma kuma a zahiri ake ganin haka amma a baɗini be san me ake yi ba, ya tafi duniyar tunanin da a kullum shi ya zame masa jiki, babban abinda yake ɗaga masa hankali shine, ko a ina take? Ko wanne hali take a yanzu? Ko tana cikin ƙoshin lafiya? Amma bu ɗaya yasa ni wanda be sam be yarda da shi ba shine yake kuma tsoron kawo ran sa, mutuwar ta. Baya son ya kawo tunanin cewan  ta mutu. A kullum burin sa be wuce ace yau ya ganta ba, be san wanne irin kalar farin ciki zai yi ba, musamman idan aka ce ya ganta wannan tunanin ne kaɗai idan yayi yake samun sauƙi da salama sai yaji kamar Baba Garko zai kira shi yace anganta.
   
    Besan wani kala a rayuwar sa na kewa ba sai da ta kasance bata kusa da shi, ya ɗauka sanda ya tafi karatu tsawon shekaru shida yayi kewan gida ashe ba haka bane idan aka kwatanta yarda yayi yarda yake ji a yanzu, gashi de tsawon wasu shekarun shida harda watanni amma  gaba ɗayan sa jin sa yake be cika ba, tunda rasa ta yasan cewan ita ce cikon farin cikin sa, ita ce ɗaya ɓarin sa, kusan zai iya cewa Matar sa rabin sa ce, ita mahaɗin rayuwar sa. Yasan kuma tana san son shi tun sanda yaga hotunan nasa a rayuwar ta, kuma ya godewa Allah da hakan ta kasance kaso a soka shine so, ba ka so aƙi maido maka da san ba.

    Ta wani ɓangaren kuma Yaya Aliyu shima, yayi auren ya so matar sa amma kuma me? Ya tabbatar da tana san sa da bata furta abinda yasa suka rabun ba, da ace tana san sa kwatankwacin yarda yake san ta da duk hakan be faru ba, amma sai dai kash, shi be yi sa'ar matar ba, dan a yanzu ta riga da tayi aure harda ƴar ta mace, bugu da ƙari a companyn sa matar take aiki, sanda ya ga sunan ta sai da yayi yarda yayi ya cire ta, amma besan wanne munafuki ne yaje ya faɗa wa Yaya Aliyu ba sai ganin ta yayi a sabbin ma'aikata abin yayi masa ciwo shi da ba shi aka faɗawa maganar ba amma baya jin zai taɓa barin kwanyar kan sa...

"Sajjad".

Muryar Aliyu ta katse masa tunanin sa. Juyowa yayi yaga har ya zo kusan shi, ɗaga mug ɗin yayi ya kai bakin sa da niyyan sipping sai yaji babu komai hakan yasa shi kallan Mug ɗin.

"Baka san ka shanye ba".

Murmurshi sukayi a tare, kafin ya ajje akan table suka yi cikin office inda ya kasance kujeru ne aka tsara su kamar parlour.

Aliyu yace, "Naji abinda kuka yi a meeting".

"Zan zo cikin wannan satin in Sha Allah".

"Yaushe?

"Zuwa Thursday".

"Why not Wednesday".

Shiru yayi be bada amsa ba yayi shiru.

"To shikenan, mu yanzu zamu wuce. Ka kula da Anty".

Tashi yayi suka fito suna tafiya.

Yace, "Kaje ka duba Daada".

Shiru yayi bece komai ba.

"Dakai nake magana".

"Toh".

Shima be ƙara cewa komai ba, har suka fito suna fitowa wajen building ɗin akwai steps kafin ka haura ka shiga, a bakin step ɗin farko yaga yarinyar da ba zata wuce shekaru huɗu ba, tana ƙoƙarin hawowa, kallan ta kawai yake har suka ƙara so, babu tsammani ya daka mata wata uwar tsawa, da sauri ta juyo harda faɗuwa, be damu da faɗuwar ta ya ƙara cewa mata.

"Me kike yi anan?

Ya faɗa a tsawa ce, yayin da Aliyu ya zuba masa ido yana mamakin sa, a sanin da yayiwa Sajjad yana da matuƙar san yara musamman idan mata ne, amma kuma shine zai ke yiwa wannan yarinyar tsawa haka? Wanne hali ne wannan ɗin da be san ɗan uwan sa na da shi ba har haka?  To wacece wannan ɗin?

Shikuwa Sajjad fuska a ɗaure ya nuna mata hanyar building ɗin da ya san Maman ta anan take, dan kada ma ya Yaya Aliyu yasan yarinyar wacece bare kuma har ya ji san yarinyar ya ɗar su a zuciyarsa, shiyasa yayi hakan, kuma daman can idan yaga yarinyar wani irin tafasa zuciyar sa ke yi, kawai baya san ta kamar yadda baya san uwar ta, farkon ganinsa da ita yaji ta burge shi saboda yarinyar bata da irin wannan surutun na yara sannan bata da ƙiwa takan fito tayi ta zagaye companyn tana wasan ta, yakan je yayi mata magana har ya taho mata da sweet amma tun daga sanda ya ga ashe ƴar matar da Aliyu ya aura ce wato Zainab yaji ya tsani yarinyar.

"Sajjad meye haka?

"Yaya Aliyu yarinyar ɓarna ne da ita shiyasa".

"Kuma sai kayi mata irin wannan tsawar? Yaushe ka canzawa yara?

Ɗauke kai yayi yana zuba duka hannun sa a aljihu, Aliyu be kuma cewa komai ba saboda ƙarasowar Al-ameen, yasa drivern sa ya kai su airport. Shi kuma ya dawo ciki.

*****

Anty ce a zaune bayan ta ansa mata pillow sannan an ɗaura wani pillown a cinyar an ɗauka bowl akai, ita kuma tana sa hannu fork tana cin fruit ɗin da aka yanka mata. Tsawon shekaru huɗu tana fama da ciwon zuciya sannan kuma da stroke sai dai ya zo da sauƙi domin hannun ta yana ɗaguwa sannan tana magana abinta kuma ana samun cigaba sosai. Turo ƙofar yayi da sallama ya shigo ya sami gefen ta ya zauna.

"Ka dawo?

"Eh".

Yayi yana kallon ta, kafin ya karɓi fork ɗin da niyyan bata, ta girgiza masa kai sai ma ɗaukowa da tayi ta sa masa a baki ya amsa yana kallon ta kamar yarda itama take kallan sa.

"Daada yana gaida ki".

Murmurshi tayi.

Tace, "Aliyu yace kaje?

"Ehh".

"Sai ance kaje ko?

"Yi haƙuri".

"Allah ya nuna min ranar da za'ace an wanke shi daga laifin sa, bana so duniya cigaba da ganin sa da laifi".

Shiru tayi haka shima.

Tace, "Bana so

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now