17

65 1 0
                                    

A hankali ya ƙarasa kusa da ita sai anan yaga dalilin da yasa baccin be mata daɗi ba, kallan acn dake saman ta yayi kafin ya taka yaje inda ake ajje remote ya ɗau ya kunna mata, sannan ya dawo ta gaban desk ɗin ta ya ɗan bubbuga sau biyu. A hankali ta buɗe idan ta kafin ta tashi tana yatsine fuska, mutumin da Faisal ya nuna mata a matsayin Abdulmajid ɗaya daga cikin masu companyn yasa ta wartsakewa lokaci guda gaban ta wani irin faɗuwa harda su tashi tsaye tana gaida shi. Shi wallahi dariya ma ta bashi, kana kallon kaga yarinya kawai girma tayi dan bazata wuce sa'ar Bintu ba, dan itama Bintu kawai shekarun ne da girma amma inaa har yanzu ba hankalin, ita ɗin ma sai yagan ta kamar Bintun. Da yayi niyyan yi mata rashin mutunci amma ganin yanayin ta da tsoron da ya gani kwance saman fuskar ta sai ta bashi tausayi beside be san a  ina take ba, be kuma san a wanne yanayi ne take ciki ba, dan daga ganin shigar ta zaka san ba daga gida mai kuɗi ta fito ba.

"Ki zauna".

Zama tayi tana tsila ido, daƙyar ta haɗiye abinda ya tokare  mata maƙoshi lura da hakan da yayi ne yasa shi buɗe fridge dake  kusa da shi yaga babu komai, bece bakomai ba ya fice, yana mamakin wannan yarinyar haka.  Ajiyar zuciya ta sauke sosai kafin ta dafe kan ta, sai kuma wani sanyi da ya ratsa ta, hakan yasa ta kallan sama taga ac. Ohh ba san ba, yaushe rabon da ta zauna a ac irin haka? No wonder bacci ya kwashe ta. Ko ta ina acn ta kunno oho.

Abdulmajid kuwa na fita office ɗin Mustapha ya nufa ya same shi yana aiki.

"Yanzu nake shirin zuwa wurin ka".

Mustapha ya faɗa yana cigaba da  aikin sa.

"Naje duba sabbin ma'aikatan nan".

"To ya? Suna aikin nasu. Bana so a zo a sami matsala fa, irin wacce aka samu".

"Kaima kasan ba yanzu zamu gane hakan ba. Shi yasa muka dena yarda da kowa, komai muka sa ayi gwara mu duba da kan mu".

"Abin sai ya fi".

"Yanzu kaine zaka je Abuja, jiya naje Kaduna, ranar Alhamis Sajjad yace min zai je".

"Me zai yi acan?

"Share ɗin dake cikin companyn sa zai bayarwa kowa nasa, saboda Turawan nan".

"Gaskiya gwara ya mayar, kuma muma zamu karɓi wani abun".

"Hakan yayi".

"Kasan me nagani?

"Me ne?

Murmurshi yayi yace, "Ɗaya daga cikin ma'aikatan nan kawa na samu tana bacci?

Shima Mustapha abin sai ya bashi dariya.

Yace, "Bacci kuma?

"Bacci de".

Yace, "Ko wacce ta zo a ƙarshe ce jiya? Kasan su shida ne, kuma ita kaɗai ce mace, Jiya ma naganta".

"Ita ce de".

"Daman wannan nasan za'ayi shiririta kawai de dan naga bata da hali ne shiyasa, dan naga irin masu halin nan ce wallahi baza'a ɗauke ta ba".

"Nima abinda yasa banyi mata magana ba kenan wallahi. Kawai tausayi ta bani".

"Shikenan kasa ido akan ta".

"Musa ido akan ta zaka ce".

A tare suka saki murmurshi, kafin ya tashi ya koma office ɗin sa shima domin aikin sa.

Nilah kuwa aikin ta ta cigaba da yi ganin lokacin sallah yayi yasa ta rufe system ɗin ta tashi ta fito, tana fitowa suna haɗuwa da Faisal tare suka jera kamar ɗazu, amma batare suka dawo ba, dan sai da ta zauna ta kuma ɗan matsewa sannan ta fito ta tafi. Yanzu kam aiki ta fara yi baji ba gani tana yi tana saving, har ta ɗan yi da yawa, ganin ta kammala na wurin ta sai wanda aka kawo mata yasa ta bi tana dubawa ko tayi typing error a hankali take bi. SAJJAD AHMAD ADAM.  Taga sunan sa dam taji wani irin bugawar zuciyar sam da tana rubutawa bata ga wannan sunan ba, sai anan ta fara bin sunayen companyn ne ashe da za'a ziyarar ta wannan satin, date ta duba taga anje jiya, sosai gaban ta taji yana bugawa, kafin a hankali taga garin da yake Kaduna. Kuma shima a Kaduna yake, amma shi ai Doctor ne, kuma da Ahmad Adam kawai yake amfani me zai kawo sunan sa nan? Meye hadin sa da wannan mutanen?

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now