14

58 2 0
                                    

A yanzu babu wani ciwo da Sajjad yake ji banda rashin Nilah a kusa da shi, dan haka yau be sanar da kowa ba, dan ya lura Yaya Aliyu ƙara tsayar dashi yake, hakan yasa ya shirya sassafiya batare da kowa ya sani ba ya fice ba abinda ya ɗauka sai ATM ɗin Aliyu.

Baba Garko yau ba aiki yake ba, yana zaune yana cin abinci suna lissafi da Muftahu da zai yi tafiya kwana nan, kwatsam sai ganin mutum sukayi babu zato babu tsammani, a iya sallamar sa zaka gane ba ƙaramin sanyi muryan sa tayi ba, haka ma daga kallan sa sau ɗaya zaka tabbatar da hakan, dan yayi wani irin fari da shi ya kuma rame, ya sauya sosai daga yarda ada.

"Ahmad?

Suka faɗa a tare, cike da mamaki. Ƙara so wa yayi ya zauna cike da ladabi yana gaida su.

"Ya jikin naka? Abokin ka daya kawo  yake sanar dani abinda faru".

Kan sa a ƙasa ya jinjina musu kai alamar eh.

"Ita kuma Hauwa'u har yanzu ba'a ganta ba".

Da sauri ya ɗago da kan sa ya kalli Baba Garko yana yi masa kallan dagaske kake? Alamar irin be yarda ba ɗin nan, lokaci guda kuma gaban sa na wani irin faɗuwa.

"Bata nan?

Ya faɗa hawaye na zubowa a fuskar sa.

"Hauwa'u bata nan, bamu gan ta ba, mun rasa ta. Tun wannan abinda ya faru".

Kasa cewa komai yayi sai hawayen da yake zuba a fuskar sa, wanda zai iya cewa besan da zubar su ba sai da yaji danshin su, be damu daya goge ba, suka ci gaba da zuba masa.

"Zan iya ganin inda muka zauna?

Ya tambaya yana sa hannu ya share hawayen.

"Tashi ka ɗauko masa mukullin ka buɗe masa".

Jiki a sanyaye ya tashi, be shiga ta cikin gidan ba, sai ya zagaya ta baya yana tsaye yana kallan wuri ɗaya ya lula tunani har Muftahu ya zo ya buɗe be sani ba sai da ya taɓa shi sannan ya dawo hayyacin sa, shiga yayi yana kallon gidan tare da tuna duk wani moment ɗin su shi da ita. Wardrobe ya buɗe ya ciro jakar sa ƙarama bracelet ɗin ta ya fara cirowa yana gani kafin ya ɗauko wayar ta inda yayi mata kyakkyawar ajiyar yarda bazata iya gani ba. Be damu daya ɗauki kayan sa amma kayan ta kam ya ɗauka duk abinda ya ke so, ya zo musamman rigar baccin ta wacce tafi so sosai ita ya fara ɗauka. Yana cikin birkita kayan yaga wayar sa, sai a lokacin ya tuna da abinda ta ce masa ranar da zasu rabu. Ɗauka yayi itama ya sa a cikin jakar kafin ya fito da kayan abincin duka ya bawa Muftahu, sannan ya fito yace tafiya zai yi babu yarda ba'ayi dashi ba akan ya zauna, amma fafur yaƙi dole aka bar shi ya tafi, da wayar Muftahu ya kira Mahmud cewan ya zo kuma ya koma yayi haƙuri.

Sanda ya koma ana nema ayi la'asar ne dan haka yana zuwa kawai sallah yayi ya kuka ficewa direct prison ya je, babu ma'aikata duk sun wuce masallaci sai wani Christan daya gani, ya sanar dashi wanda yake nema ya buɗe masa inda aka kulle irin mutanen su daban suke kowa a cikin cell ɗin sa, mutum biyu biyu yana ta kallen su, har ya hango Daada dake kan darduma yana jan carbi. Shi kuma ɗayan yana sallah.  Ji yayi hawaye ya zubo masa yana cigaba da kallan Daada shi kawai tambayar da yake yiwa kan sa. "Wai Daada ne anan?" Juyowar da Daada zai yi ne yasa shi ganin ɗan sa, a tsaye yana zubar da hawaye, a iya sanin sa da Sajjad idan yana jinya ne kawai zai zubar da hawayen sa, ba kasafai ya fiye kuka ba, amma shine a yanzu dan ya gan shi a kulle yake kuka?

A hankali ya ɗaga ƙafar sa ya ƙarasa kusa dashi ganin haka yasa Daada ta sowa ya matso jikin ƙarfen, tare da kamo fuskar Sajjad ɗin yana goge masa hawayen.

"Daada meyasa? Daada meyasa?

"Kuyi haƙuri kaji ɗana?

Murmurshin takaici yayi yana ƙwace fuskar sa.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now