3

123 3 0
                                    

        

Yau kimamin watanni shidda  kenan Sajjad na garin Bauchi duk inda ya kamata ace yaje ganin ƴan uwa yaje da wanda ya sani da wanda be sani hatta ƙauyen Bauchi sai da yaje ya koyi yare da dama a ɗan zaman sa dake ance sa kai yafi bautawa ciwo  har noma ya iya ya kuma koyi abubuwa da dama na hannu daga ns mazan har na matan ya iya, tuni kowa ya san shi amma Maza idan kaga yana mu'amala da mace to tsohuwa ce ko irin su Mama ne ko kuma ƴar yarinya ce ƴar ƙarama da bazata wuce sa'ar su Samir ba, tun matan na masa magana har suka Dena gaida shi ma to shima hakan ya fi masa daman ba so ba yake ba. Sai dai kallo ɗaya zaka masa kasan  lalle ya rame domin yayi baƙi dan shi kaɗai yasan irin azabar da zuciyar sa ke masa saboda  kewan gida duk da kuwa irin kulawar da Mutanen ke bashi.

Dawowarsa da ga noma kenan ya shigo gidan yana wanke hannun sa yana rera wakar da tsohuwa ta koya masa  ɗago da kansa da zai yi yayi ido huɗu da Abba da wani irin gudu ya tafi ya ɗalle kan sa yana dariya.

"Abba ka dawo? Yaushe ka zo? Ina su Anty? Ina Mama? Ina Ummi? Ina su Sadiq ina Samir".

"Ikon Allah yau ni naga abu".

Tsohuwa ta faɗa ta fulatanci tana kallan sa.

Abba yace, "Duk suna lafiya yaro na, tashi ka dauko kayan ka mu tafi".

Da gudu ya shiga ya kwaso kayan sa ya ɗauko wayar sa da takalmi.

Yace, "Tsohuwa sauran kayan a bawa Abdul, kice masa kuma ya kula min da gonata zan dawo, Abba taso mu tafi".

Zatayi magana ya kuma cewa.

"Yauwa kice masa idan yaje Bauchi ya faɗa musu ni na tafi".

"Amma kaje ka musu sallama".

"Idan ya musu kamar nayi ne, Abba taso mana".

"Ohh ni Hafsatu Ina ganin ikon Allah".

Be jira Abba ba yayi gaba, ya wurga ido a can ya ga motar su guda daya  da'alama a jirgi ya zo wurin motar yayi ya shiga ya zauna yana jiran Abba.

Abba yace, "Umma zamu tafi Allah ya saka da Alkhairi".

"Amin, kuma Allah ya yayi muku albarka".

"Amin Umma, a gaida Mutanen gidan gashi tafiya babu shiri, ba yawa abubuwan dan Allah ka kai musu".

"In Sha Allah Umma, hakan ma an gode".

"Abba wai yaushe ka dawo?

"Jiya na dawo".

"Amma Abba baka sanar da ni ba zaka dawo fa".

"Ai bamuyi waya ba tun shekaran jiya".

"Aww haka ne".

Kafin magriba sai ga su Kaduna murna fal cikin sa Abba kawai kallan sa yake yana dan shi Abba Allah ya gani be wani irin so yake yiwa Sajjad san da ya kasa ɓoye shi sai da ya fallasa kowa ya san irin san da yake masa yana jin tsoron ace yau an wayi gari wani abu ya sami Sajjad yasan shima sai abin nan ya same shi.

"Antyyyyyyy".

Ya kwaɗa mata kira tun kafin ya shiga apartment ɗin ta be dena ba ya cigaba. Ta fito daga Kitchen kenan tagan shi bata yi aune be taji ya rungume ta.

"Sajjad ko da ka dawo daga makaranta bakayi wannan murnan ba haka".

"Inaga daga prison ya fito".

Hafiz da Yusuf suka faɗa.

"Allah ba zaku gane ba shi yasa da kune kuka je garin nan nasan bazaku iya zama ba".

Hafiz yace, "Allah ya sauwake sai kace wani kai..."

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now