16

62 1 0
                                    

Yau ma de daga meeting ɗin ya fito, zai shiga wani ya wani haɗe fuska kana gani zaka san ran sa a mugun ɓace yake saboda yarda yake tafiyar ita kanta a zafafe, babu wanda ya saba ganin sa a irin wannan yanayin hakan yasa yake bashi hanya gudun faruwar wani abu, tare da binshi da kallo suna mamakin sa, yayin da sectary ɗin sa yake bin shi da sauri domin kafin ya jefa ƙafa daya Sajjad ya jefa huɗu saboda wani irin sauri da yake yi, shi kan sa conference ɗin da zai shiga a zuciye ya shiga batare da ya kalli kowa ba ya nemi kujerar sa ya zauna ya harɗe ƙafa ya jingina da kujera ya ɗaura hannun sa ɗaya akan table ɗayan kuma yana murza babban ɗan yatsan sa da manuniyar yatsan sa, yayin da ya tsaida idan sa a wuri ɗaya inda yake da tabbacin anan sectary ɗin sai zai ajje masa files dake hannun sa. Shi kuwa Sectary sai a lokacin ya ƙara so har wani haki yake ya ajje masa abinda zai ajje masa yaja kujera daga nan bayan sa ya zauna inda duka sectary ɗin su suka zauna.

Wani daga cikin baƙin da suka zo ne ya fara magana akan dalilin zuwan su da kuma haɗa hannun da zasuyi domin ci gaban su gaba ɗaya ganin cewan wannan companyn yana yin abinda suke yi, be yi magana ba har ya gama, kafin wani shima yayi, sai wata mata duka-duka baƙin su shida ne sai kuma Abdulmajid da yayi magana a ƙarshe, shi sam bema san zai zo ba sai da yaji maganar sa akan tallafin da suke nema saboda yanayin kasuwanci na can kuma bugu da ƙari shi sabon company ne, duk da cewan companyn nasu ne gaba ɗaya suna kuma da iko da shi, amma suke yin hakan, saboda su iya kasuwanci batare da an taimakawa kowa ba.

Abdulmajid da yayi magana a ƙarshe ya kalla.

Yace, "Wannan companyn zai sa share a companyn ka, shine kaɗai taimakon da zamu maka".

Daga haka ya kalli sauran suna ya basu amsar su, sannan ya kalli agogo.

Yace, "Mai magana ya riƙe maganar sa 30 minutes kuka nema kuma ta ƙare".

Daga haka ya tashi ya fice, zuwa meeting ɗin da za'ayi general gaba ɗaya duka ma'aikatan domin makarantar da za'a buɗe ta company. Makarantar a cikin companyn take sai dai idan aka shigo companyn kafin a compound ɗin daga gefe aka yi gate shi kuma sai ka ƙara tafiya zaka shigo gate ɗin companyn da zai da ka da buildings ɗin.

A tsaye yake ko zama be yi ba, tsabar yarda ya ƙagu ya faɗi abinda zai faɗa ya ƙara gaba, duk da yanzu ya ɗan sauko amma ba duka ba. Kallan wanda suke zuwa yanzu yake tsabar sun raina masa hankali tunda safe ya sanar amma sai yanzu wasu ma suka san da meeting ɗin, shiyasa companyn ƴan uwan sa suke burge shi basa ɗaukan renin hankalin nan na ma'aikatan su akwai dokar da suke shimfiɗawa duk wanda ya karya to imma aci tarar sa ko kuma ya kori kan sa da kan sa babu zagi babu cin mutunci tun Baba na musu magana har ya haƙura ganin kowa ya fi riƙe aikin sa da muhimmanci. Idan sa ne ya kai kan Zainab da yarinyar ta a kafaɗa, tsabar ta rena masa hankali ita sai yanzu take zuwa ganin jakar ta a hannu. Wani irin tsabar ta yaji ta sake rufe shi ta ko ina muddin zai ganta to sai ya tuna abinda ya faru a baya.

"Ke sai yanzu kike zuwa aiki?

Tasan da ita yake, saboda ita ce ta shigo yanzu, kuma bata san da zuwan ba sai da taga babu kowa shine tayi tunanin ƙila meeting ake.

"Yarinya ta ce bata da lafiya".

Wani wawan tsaki ya ja be ƙara magana ba, itama kan ta a ƙasa taje ta zauna don tasan irin tsanar da yayi mata, ta tabbatar idan da ace kisa ba laifi ne ba to tabbas tasan zai sa wuƙa ko bindiga ya halbe ta har lahira, kuma itama bata ga laifin sa tunda tasan tayi ta kuma aikata, amma abinda yake bata mamaki shine, shida ba shi aka yiwa laifin ba amma yafi wanda aka yiwa laifin jin haushi, tana jinjina wannan soyayyar dake tsakanin su.

Magana yayi musu sosai gami da makarantar da za'a buɗe ga wanda yake so yasa yaran sa saboda sauƙin ɗaukan su saboda wayan cin ma'aikatan suna tashi ne daga 12 zuwa 2 na break wasu su ɗauko yara a makaranta wasu suje su ci abinci da sauran su de, amma ba za su tashi ba sai 7 na dare maimakon 4 ko 6, hakan suka zaɓa shima kuma hakan yayi masa, yanzu da ya fito da wannan tsarin sai hakan ya yi musu daɗi sosai musamman masu makarantu da nisa daga nan kawai gida zasu kai yaran su kuma sannan ga araha babu tsada. Yana gamawa ya fice saboda wani meeting ɗin da ake jiran sa hallau.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now