22

65 1 0
                                    

Da daddare suna zaune a ƙofar ɗakun su, su duka sun rufo ƙofar saboda magani da aka sa, mutanen gidan kuma na zaune a wurin bishiya kamar de yarda aka saba, wasu kuma da mijin su ya dawo suna zaune a ɗaki wasu a wasu kamar de su. Yayin da kowa yake tasa irin hirar. A ɓangaren Nilah kuwa sam ba hirar take ji ba wanda Jiddah ce tunda suka dawo daga makaranta take basu labarin saban Daddyn da tayi suma kuma basu gaji da ji ba, yanzun ma shi take bawa Nilah amma sai dai hankalin ta baya jikin ta sam, yayi wani wajen, tunanin yarda zatayi da wannan al'amarin  take, kuma bata san zatayi da shi ba. Idan ta ce zata sanar da su halin da ake ciki to tabbas tasan ba za'a kama wanda suke waya da shi ba. Abu ɗaya take so tayi shine, wanda yake kira yana basu umarni shi take so ta fara sani. Amma kuma taya?  Kan ta taji yana wani irin sara mata, ga bacci ga rashin cin abinci ga damuwa ga rashin jin ƙarfin jiki. Jikin ta har wani zafi-zafi yake mata.

Ruƙayya tace, "Nilah lafiya kuwa?

Kallan ta tayi tare da ƙirƙiro murmurshi.

Tace, "Kaina ke ciwo".

"Gajiya ce, bari na ɗauko maki ki sha. Daman wannan aikin naku ni bazan iya ba. Kina ƙoƙari ma ai".

"Ki bari, akwai a ɗaki idan na tashi zan sha".

"Amma kamar wani abu na damun ki?

Shiru tayi kamar ba zatayi magana ba sai kuma.

Tace, "Bakomai yake damuna sai wani abu da ke ɗaure min kai".

"Meye shi?

Tsab ta basu labarin abinda taji da kuma yadda akayi ta ɗauke flash zuwa abinda taji yau.

Tace, "Ni bansan ya zan yi ba?

Abdallah dake sauransu.

Yace, "wannan abu da haɗari yake".

Ruƙayya tace, "Ai mutane da kike ganin su, kawai ki kalli kowa da ido kiyi sabgar ki".

Tace, "Da tunani sanar da Faisal nake".

Abdullah yace, "A'a kar ki sanar da shi, ki bari ki ƙara sanin halin shi, kada azo daga ƙarshe shima yana da manufa kuma abin ya racaɓe".

Shiru sukayi. Kafin yace.

"Abinda zakiyi da dama sai ki sa recorder wannan wanda zaki iya jin mutum duk sanda yake waya a system ɗin ki, ko kuma ki sami numbern da ki sa a taki ki haɗa ko da message ne zaki gani ya zo miki. Ko a haɗa duka biyun".

Yace, "Tunda ba lalle ne ba ce duk wata waya zai yi ta a office".

Jinjina kai tayi.

Yace, "Sannan kuma duk wani tsayuwar su kike ɗauka a waya da da hali har abinda suke ji".

"Amma taya hakan zai iyu kuwa?

Murmurshi sosai yayi alamar baki san dawa kike tare ba.

Yace, "kada ki damu. In Sha Allah komai zai tafi dai-dai".

Jinjina kai kawai tayi, dan ita gani take kawai hakan ba me iyuwa bane ba. Taya za'ace wani message ma kayi sai mutum ya gani.

Ruƙayya tace, "Ai ni na tabbatar ai wallahi kai ko?

Yana dariya yace, "Ni me nayi?

"Kafi kowa sani ai. Haka fa ya min, in faɗa miki ba dama nayi waya mutumin nan ashe yana ji? Duk wayar da zanyi a lokacin yana ji".

"Ai wannan saurayin naki".

Ya faɗa yana dariya sosai tare da tuno da rayuwar su.

Nilahn ɗan murmurshi tayi.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now