5

81 0 0
                                    

Washegari da suka je asibiti babu laifi patients sun zo sai dai yana tausayin su ace wai sai sun je har Gassol sannan zasu sai magani wanda za'ayiwa scanning ma haka, shi yafi tausayin masu ciki ma. Dan da wata ta zo ƙiris ya rage be yi kuka ba da aka tura su asibitin Gassol ɗin.

"Idan ta haihu kuma a mota fa?

Habib yace, "Idan kace komai za kake magana akai ba zaka samu amsar sa ba. Nima haka nayi farkon zuwa na so zakayi ka bari".

Mahmud yace, "Abinne abin tausayi".

Murmurshi kawai yayi ya bar su ya cigaba da abin yake daman su ba duba patient ɗin suke ba, to me za suyi ? Zama kawai suke yi suna kallan yadda yake kula da su. Kiran Abba da ya shigo wayar sa ne ya sa shi tashi ya basu waje, magana sukayi sosai akan maganar taimakawa asibitin yayin da Cal. S. A abokin Abban yace kawai za'a sake musu sabo kawai dan be je wurin kowa na sai wajen Governor kuma ya bashi ragamar komai a hannun sa, sosai yayiwa Abba godiya akan taimakon da yayi daga bisani sukayi sallama. Washegari kuwa suna zuwa suka ga mutane ana bawa kowa hakkin sa inda ya kasance gonar su zata shiga hakkin su ake basu batare da acewar an zalunce su ba. Yayin da aka nema Sajjad wanda shine zai ke kula da harkan ginin ya kuma sa hannu a inda aka ce masa basu fara a aiki a ranar ba sai washegari da  suka dawo a ranar suka fara aiki yayin da Sajjad yake kula da aikin na su hakan yasa kwana biyu yaje busy baya komawa sai Yamma lis suke komawa.


******

Yana kwance yana chat yaga mutumin  nan ya turo masa da saƙo buɗewa yayi ya shiga, abinda ya gani ne yasa shi tashi zaune, yana zooming hotan babu shiri ya kira shi. 

"Wannan shine wanda ya min magana ranar da na fara zuwa".

"Shine yau ya zo wurin Mai gida".

"Baka ji me suka ce ba?

"Gaskiya ban ji ba".

"Abinda nake so da kai shine, idan sun sake zuwa ka naɗi komai ko ka ajje ƙaramar wayar ka idan kaje shara".

"Hakan ma ba shine solution ba za'a iya cewa haɗawa akayi irin yadda akayi wa wani a unguwar mu".

"Ya kenan za'ayi?

"Zan san yadda za'ayi kar ka damu".

"To Baba Nagode".

Yana kashewa ya kira Yaya Aliyu.

"Ya akayi?

"Wannan wanda ya min maganar nan Sagiru? Yaje wurin Daada".

"Me suka ce?

"Shine abinda bamu sani ba".

"Wai sai yaushe zaku dawo?

"Sai wani satin daga nan ma Dutse mukayi daga nan muyi Bauchi sannan mu dawo".

"Innalillahi".

"Idan mun dawo ɗin zan je gidan shi cleaner ɗin".

"To shikenan".

Ya faɗa a sanyaye, kafin ya kashe wayar ya tashi ya fito. Ya jima be haɗu da ita ba kwana kusan nawa kenan, addu'a kawai yake Allah yasa tana nan, yana zuwa ya gango ta yau ita da yara ne a wurin suna ɗebo mata ƙasa tana haɗa musu gida ɗankwalin kanta ta cire hakan yasa shi ganin yalwataccen gashin ta a tsakiyar kai duk ta shafa masa ƙasa, kamar kullum yadda ya saba sai da ya jima yana kallon ta batare da ya san me yake kallo ba.

"Yaya Nilah".

Ya maimaita a zuciyar sa jin wani yaro ya ambaci sunan yana meƙo mata ƙasa, yayin da ɗayar  yarinyar  kuma Adda Nilah.

"Assalamu alaikum".

Yayi ƙarfin halin faɗa yana ƙara sawa wajen su, yarinyar ce kawai ta amsa masa.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now