42

63 0 0
                                    

Gidan Yayar Anty suka je, wanda daman anan suke sauka duk zuwa, tunda ba su da iyaye a raye. Sosai aka tarbe su tarba ta mutunci da karamci. Da yamma suka je suka zagaya ƴan uwan tare da ɗan Umman wanda ya kasance sa'a ne ga Sajjad. Sai dare sosai suka dawo yaran tuni sun yi bacci. A parlour suka sami Umman.

"Sannun ku. Kun sha yawo".

Cike da kunya NilahBy G ta ƙara so ta zauna a ƙasa.

Sajjad ne daya ɗauko Jiddah Shi kuma Sabir ya ɗauko Hauwa Abie kuma ya riƙo hannun sa suka shigo.

Umma tace, "Ku wuce da su ɗakin su Saddiqa".

"Sannu Sajjad".

Ɗan murmurshi yayi.

Yace, "Ai mun jima bamu zo bane".

"Da ka dawo ai ka zo".

"Eh ba".

Sabir yace, "Kar ma wani na Allah".

Umma tace, "To da na meye?

"Nima Umma auren nan zan yi ko za'a ke min kallan mutunci. Duk inda muka je fa, sai ayi ta wani girmama shi irin gashi ya fimu ɗin nan".

Dariya abin ya basu, har Nilah suka dara.

Yace, "Dan Allah Anty Nilah dan Allah kimin budurwa nima kinji ko?

Umma tace, "Sabir a gaban nawa?

"To Umma bakin ƙi min ba".

Tashi tayi tana hamma.

Tace, "Nilah kuje ku kwanta sai sa safe".

Cike da kunya ta amsa. Tana neman shiga ɗakin su Saddiqa yayin da su Sajjad suka nufi ƙofar fita.

Umma tace, "Nilah, kibi mijin ki shine zaki bar shi ya kwana shi kaɗai? Ai kayan ki ma suna can".

Kasa motsawa tayi daga wurin tsabar kunya, bata taɓa tsintar kan ta a cikin matsananciyar kunya ba irin yau, bata je ko ina ba sai da taga Umma ta wuce sannan ta sauke ajiyar zuciya tana neman shiga ɗakin na su, taji ya riƙe hannun ta.

Yace, "Haba yarinya, ki gane mana".

"Wai kai baka jin kunya?

"Kunya kuma? A gidan namu?

Ƙasa-ƙasa tace, "Dan Allah ka sake ni kar wani ya gammu".

"To muje".

Ya faɗa yana sakin ta, yasa ta gaba suka wuce ɗakin su da aka tanadar musu.

Kwanciya yayi akan gadan ko takalmin be cire ba yana sakin ajiyar zuciya dan shi kam ya gaji sosai, ita kuwa ko magana bata masa ba, ta wuce ta ciro kayan ta na bacci ta wuce toilet. Sai da wankan ta sosai sannan ta fito ta feshe jikin ta da turare batare da ta shafa mai ba, kawa taje ta kwanta a gefen sa.

"Ka tashi ka je kayi wanka mana".

"Haka zan kwana".

"Nidai ba zan kwana da ƙazami ba. Ka wuni kana yawo kace ba zakayi wanka ba".

Yace, "Ina ruwan ki, jikin ki ko nawa?

"A'a jikin ka ne, ammar ka matso kusa dani".

Murmurshi yayi yana mirginawa kusa da ita gaba ɗaya ya hau kan ta.

Yace, "Maimaita abinda kika ce".

Tana nishi daƙyar tace, "Bance komai ba. Ka ɗaga ni dan Allah".

"Sai kin maimata".

Ya faɗa yana ƙara sakar mata nauyin sa.

"Bance komai ba. Kayi haƙuri dan Allah".

"Idan anƙi fa".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now