24

52 1 0
                                    

Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya iske wurare da dama cike da wajen Kano haka ma wurare da dama a garuruwa. Kowa sai ya jajanta wa lamarin. Sajjad wanda dawowar shi kenan daga wurin Anty, be taɓa jin haushi Inna irin yau ba, shi fa a yanzu babu abinda yayi masa zafi da ita, shiyasa ya dena shiga sabgar ta shima ta kan sa yake sannan kuma ga haushin  wannan yarinyar  yake ji. Allah ne kaɗai yasan haushin da ya ji yau. Ya fito daga wanka kenan yana shafa mai kada a yi magriba yaga kiran Hafiz.

"Ka tafi gida ne?

"Ehh".

"Mun wuce kano".

"Kano kuma? Jiya fa na dawo daga Kanon".

"Baka san ne ya faru ba ma kenan".

"Mene ya faru?

"Gobara ce ta kama a companyn, ɗazun nan".

"Hasbunallahu wani'imal wakil. Da fatan babu wanda ya rasa ran sa".

"Babu wanda ya rasa ran sa".

Ajiyar zuciya ya  sauke tare da neman gefen gado ya zauna.

Yace, "Nima gani nan zan taho".

"Mu mun tafi".

"Sai taho".

Daga haka sukayi sallama yana mamakin gami da jimamin wannan abun. 'Allah ya rufa asiri'  ya faɗa a zuciyar sa.

A gaggauce ya gama shiryawa ba wasu kaya ya sa ba shirt ce da wando  yasa sai kayan sa da ya janyo ya zuba a luggage ya ɗauki abinda yake so. Ya wuce masallaci bayan ya sanarwa da Sojojin sa,ana idarwa kuwa ya dawo cikin gida ya shiga yaji labarin har sunji.

Abba yace, "Idan ka tafi waye zai kula da nan ɗin?

Yace, "Da wai hutu zancw a bayar".

"To shikenan. Sai gobe mu zamu taho idan angama shari'ar nan ta Adam. Allah ya kiyye

"Shari'a kuma Abba? Wacce shari'ar?

Abba yace, "Baka san an  sake ɗaukaka ƙara ba?

"Bansani ba,waye ne ya sake shigar da ƙarar? Amma ba Yaya ƙarami ba ko?

Murmushi Baba yayi.

Yace, "Kai ma kasan ba shi bane ba. Wata mata ce ta sake shigar da ƙarar wacce ta san asibitin nasa".

"Allah ya bada sa'a".

Da ameen su ka amsa.  Inna dake zaune tana jin su ganin yana ƙoƙarin tashi.

Tace, "Banji kace masa komai ba".

Baba yace, "Inna me kuma zance masa? Bacin abinda ya faru. Inna a bari ba yau ba sai komai ya lafa".

Shidai Sajjad bece komai ba har ya fice, sallama ya shiga yayi wa su Ummi da Mama sannan Anty, suka tafi.

*****

A hankali ta shiga buɗe idan ta, tun tana kallan dishi-dishi har ta buɗe shi tarwai tana kallan ceiling ɗin ɗakin, kafin ta juyo da kan ta gefen ta taga mutane jere ta kuma juyo da kan ta ɗayan gefen taga mutane, kafin ta yunƙura ta tashi zaune tana sake kallon mutanen dake kwance. Sai kuma lokaci guda abinda ya faru ya faɗo mata. Ganin su Abdulmajid sun shigo yasa ta kallan ƙofar, ita kadai ce ta tashi dan ita babu abinda ya same ta, kawai tsoratar da tayi ne ta suma, wasu ne da dayawa hayaƙi yayi musu illah sai dai alhamdulillah babu wanda ya mutu daga cikin su.

"Ya jikin naki?

Sauke kan ta  ƙasa tayi.

"Alhamdulillah".

"An kira numbern da kika sa a jikin file ɗin bata shiga ba".

Faisal dake tare da su.

Yace, "Ta shiga da akayi ta gwadawa".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now