28

52 2 0
                                    

A hankali ya shiga ya buɗe idan sa yana kallon inda yake kallo, tare da bin ina ne yake, bayan ga gama sanin inda yake kuma ya shiga neman wani abu kamar wanda aka ce masa abun zai fito, idan ba gizo idan sa ke masa ba tabbas ya ga fuskar Nilah, har ya so taɓawa ko de daman mafarki yake yi ne? Amma kuma ai idan mafarki ne a yarinyar ta ya saba ganin ta, yanzu kuma a ƴar babbar ya ganta ta fi da cika, tayi ƙiba Masha Allah da ita. Yana nufin kenan tana cikin kwanciyar hankali da samun nutsuwa?

Zaune ya tashi tana shafa kan sa cike da tunani iri-iri ya rasa wanne ma zai yi kuma duk akan ita ɗin de, ya manta sam da abinda da ya faru ɗazu, ganin agogo yasa shi tashi ya shiga toilet ɗin dake office ɗin ya yayi alwala anan office ɗin yayi Sallah kafin ya fito ya shiga nasa ya sami kujera ya zauna. Jin TV a kunne yasa shi kallan Tvn tare da kallan yaran da ke zaune a ƙasan carpet ɗin sun kafe tvn da ido suna kallo animation. Babu tantama ƴaƴan sectary ɗin sa ne wannan dan babu wanda zai shigo nan da su, tunda shi yana office ɗin ta, hakan yasa shi girgiza kan sa ya cigaba da abinda yake, su kuma suka cigaba da kallan su. Sun kwashe wasu awowi a haka su suna kallan su, shi kuma yana sabgar sa be ƙara ɗagowa ya kalle su ba.

"Nima sai na yi igin gawag nan".

Yaji Jiddah ta faɗa, cak ya tsaya da abinda yake yi kafin ya kalle su.

Abie yace, "Nidai ba luwana idan Mammy ta zo, tace kal mu ɓata".

Duk yarda sune, kenan daman acan Mahaifiyar su take aiki? Sai kuma ya tuna ashe fa sun taɓa zuwa sun duba ta ma, dariyar farin ciki yayi ko ba komai za su saba da shi, be jira ƙara wani nazari ba kawai ya tashi ya nufe su, yana zuwa ya ɗaga Jiddah da ta tashi tsaye tana masifa ta fara juyawa ta a sama, itama ta rirriƙe shi ɗan ta tsorata sosai, rungume ta yayi yana sakin ajiyar zuciya.

"Laa Daddy?

Abie ya faɗa da farin ciki haɗe da mamaki kuma, jin haka yasa Jiddah dake kiciniyar sauka ta kalle shi sai kuma ta rungume tana dariya, bajewa yayi a ƙasa aka fara kallan da shi ana bashi labari kwatanta farin cikin da yake ma ɓata baki ne, domin kuwa fuskar sa kawai zaka kalla ka gane haka, su duka suna jikin sa a haka sukayi bacci idan ya kalli wannan sai ya kalli wannan yana sakin murmurshi shi kaɗai babu abinda ke burge shi da su irin san da suke yiwa junan su duk da cewar kuwa ana faɗa amma ya gane akwai Soyayyar mai ƙarfi a tsakanin su duk da kasancewar su yara.

"Kayi haƙuri sun...."

Nilah da ta zo yanzu ta samu kan ta da faɗin haka ba tare da ta yi ko sallama ba, sannan da sauri ta taho zata karɓe su, kallan da yayi mata ne yasa dakatawa ko ƙara so wurin carpet ɗin basu yi ba. Kan ta a ƙasa ta ƙaraso tare da sunkuyawa ta fara ɗaukan Jiddah ƙamshin turaren da tasa ne yasa shi ƙara kallan ta, wannan turaren ai cuta ne, baza'aji turare ba sai anzo daf da kai salan asa mutum a wani hali, ashe fa mace ce kuma, shi kaɗai yake tunanin sa a zuciyarsa, shi dai koma meye Allah zai sa ka masa ta cuceshi.

"Mtswwwww!

Ya ja tsaki.

"Magana kake?

"A'a bakomai".

Anan yaga ta ajje su, shi ta ajje shi akan kujera ita kuma a ƙasan carpet.

"Idan ya faɗo fa?

"Ya baya birgima ita ce mai yi".

Jinjina kai kawai yayi ya tashi, zuwa tayi tayi masa bayanin meeting ɗin da suka je da abubuwan da akayi ganin Sallahn la'asar ya yi ya sa shi cewa idan sun dawo ta ƙarasa masa.

Tana fitowa taji wani mutum na waya da yaren da tunda ta baro Taraba bata taɓa jin sa ba, hakan yasa gaban wani irin faɗuwa tare da ɗan waigoya taji waye? Bazaka ce abinda yake faɗa ba abinda tausayi bane saboda yarda yake sa maganar da tausayi da tausasawa nan kuwa wani shegen makirci ne yake haɗawa, Allah yasa ta tana ji da tuni an yi angama, bin mutumim tayi a baya tana lafewa har taga inda ya shiga kafin ta zagaya ta shiga ta window ganin windows a buɗe suke, kuma babu ƙarfe, kawai dirawa tayi, sai da ta shiga taga ashe warehouse ne, shagala tayi da kallo har mutumin ya ɓace mata, sai da ta dawo hayyacin ta sannan ta lura da abinda take, da sauri ta fara neman sa jin motsi, gani tayi yana buɗe wani wuri kamar drawer a tsaye tare da danna numbers amma be yi ba. Can taga ya ɗauki waya ya fara da yaren.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now