18

55 0 0
                                    

Sosai akayi taro na musamman wanda akayi aka watse yayin da aka tafi cin abinci da Sallah a zummar idan an dawo sai aci gaba. Shi dai Sajjad wannan abun beyi masa daɗi ba sam, amma kuma babu yarda ya iya haka suka tafi, sunje sunyi sallah za su shiga wurin cin abinci yaji zuciyar sa ta wani irin bugawa da sauri ya rufe idan sa yana jin zuciyar nasa na ƙara bugawa da duk wani taku da yake yi, Baba ne a gaba sannan shi wasu duk sun shiga sune kawai basu shiga ba.

Yayin da Nilah ke zaune ita kuma ta rasa me yake mata daɗi haka nan taji yau bata jin daɗi so take ma tayi kuka ko zata ji saussaucin abinda take ji, ganin abincin ya fice a kan ta yasa ta tashi domin ta fice a wurin ta zo fita kenan sukayi kiciɓus da Baba wayar hannun sa ta faɗi, da wani irin sauri gaban na faɗuwa sosai ta durƙusa tana me bashi bashi haƙuri tare da miƙo masa wayar banda rawa babu abinda jikin ta ke yi kalmar haƙuri kuwa ta yi ta, tafi cikin kwando. Yayin da Baba ya tsaya duban ta dakyau kafin ya sakar mata murmurshi yana girgiza mata kai alamar ba damuwa, kallan fuskar sa da tayi ne yasa bugun zuciyar ta ƙara ƙaruwa ga wani irin cikar kamala da kwarjini da fuskar sa tayi mata, a hankali ta sauke idan ta ƙasa tana bashi hanya ya wuce kan ta a ƙasa Sajjad ya zo ya wuce jin ƙarshen turare baya ga na Baba shine yasa ta sauke idan ta a bayan sa, ta kafe shi da ido gaban na mugun faɗuwa, jira kawai take ace ya juyo amma shi kuma kamar ya san me take jira yaƙi juyowa ya tsaya ƙiƙam baya gaba baya baya.

"Ina san wannan guy ɗin ya zo companyn nan saboda burgeni da yake yi wallahi".

"Allah yasa yau ya miki magana toh".

"Ke idan na ganshi zuciya ta har wani sanyi take yi na dabam. Ina ma a maidani aiki companyn shi".

Kallan matan dake magana tayi a kusa da ita, itama suna tsaye sun zuba mishi ido, kafin ta kalli inda suke kallo taga the same mutum da itama take kallo ne. Bata san shi ba, bata san waye ba, amma tabbas zuciyar ta, ta bashi tabbacin shine, sai dai bata da wannan courage na zuwa tace masa ai ita ce. To ita ce wa? Zuciyar ta taji har wani tururi take saboda maganar wannan matar lokaci guda taji tsanar ta, tsana mai tsanani kawai bata san ta. Hawayen da taji ya zubo mata yasa ta saurin barin wajen tana fita da sauri, tana juyawa shi kuma yana juyowa ya bi bayan ta da kallo, da wani irin hanzari ya fito domin ya cimma haka yayi ta binta har building ɗin su yana shigowa ya neme ta ya rasa gashi sai waya aka masa yaba rejecting.

"Sajjad lafiya?

Aliyu da yaga fitowar sa ya faɗa.

"Yaya Aliyu ita ce".

"Ita wa?

"Ita mana".

Sai hawaye sharr ya zubo masa ganin ya janyo hankalin mutane yasa Aliyu fita da shi, suna fitowa sojojin sa da suka biyo shi suka rufa masa baya. Office ɗin Mustapha suka nufa yana riƙe da shi.

"Yanzu faɗa min, wa ka gani?

"Ita ce".

Dafe goshin sa yayi cike da takaici yana kallan ka, ji yake kamar ya mangare shi amma ba halin yin haka. Yayin da shi kuma Sajjad yake cike da takaicin Yaya Aliyu da ya zo, da be zo yasan zai same ta.

"Wacece".

Kai tsaye yace yana goge hawayen sa.

Yace, "Matata".

Da wani mamaki Aliyu ya kalle shi kafin ya maimaita kalmar matar da ya ambata yayin da shi kuma ya jinjina masa kai alamar tabbatarwa.

"Nasha yin mafarki ta haifa min yara, ba ɗaya ba biyu ba. Wannan ya nuna min cewar tabbas tana raye ko kuma mun rabu da ciki a jikin ta. Ina san ta".

Sai hawaye ya zubo masa kamar wanda aka buɗe fanfo yaƙi tsayawa, kuka ne yake yi na wanda ya jima be yi ba. Yayin da Aliyu yake zaune a daskare saboda maganar ba ƙarami shigar sa tayi ba. Wai aure? Wai har yake tunanin ciki? To kenan ma komai ya wakana a tsakanin su.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now