26

64 2 0
                                    

Kayan ta kawai ta gyara ta zuba su a muhallin da suka da ce, sannan ta fito domin ƙara ganin gidan, gidan yayi mata kyau sosai, ya kuma tafi da ita musamman da ta fito balcony tana iya hango cikin compound ɗin nasu da kuma wasu da suke nasu balcony ɗin. Ta shiga kitchen ɗin dake parlour wanda idan mutum na ciki na parlour zai iya ganin sa, sai dai idan ya sunkuya ba zai gan shi ba. Kitchen ɗin ya fi komai yi mata kyau a gidan, harda fridge da sauran kayan electronic na amfani. Harda ƴar Tvn su plasma ƙarama a parlourn nata da kuma receiver. Tana cikin haka akayi knocking mata ƙofa taje ta buɗe wannan matar ce ta jaraba.

"Ki zo mu je ana kiran mu".

Ɗan murmurshin yaƙe tayi irin toh ɗin nan.

"Lafiyar ki kuwa? Ko baki da lafiya?

"Alhamdulillah lafiya nake".

"To taho mu tafi za mu je a nuna mana companyn".

"Toh".

Ta faɗa tare da rufe ƙofar ta, bata jira ta kuma yin magana ba.

"Mutum sai surutu".

Ta faɗa tana ɗauko jakar ta maƙala face mask ɗin ta. Ashe babu nisa daga gidan su, a ƙafa suka zo tare ɗaya daga cikin ma'aikatan, sosai aka nuna musu ko ina a cikin Companyn ciki da wajen da har makarantar dake jikin companyn sai da aka nuna musu, ba ƙaramin haɗuwa suka ga yayi ba, ashe companyn su ba komai bane ba idan aka haɗa shi da wannan, sai da aka gama nuna musu ko ina sannan aka raba wa kowa wajen aikin sa. Matan su duka aka kai su building ɗin su, sauran kuma aka kai su sauran building ɗin, ita de haka kawai hankalin ta be kwanta ba anya ba da biyu ba kuwa aka yi wannan abun?

~~~~~

Yau ya kama Monday ranar da za'a koma kotu, an shirya iya shiryawa domin gabatar da shari'ar, duk yarda suka so samun nasara basu samu ba, saboda irin hujjojin da su Ƙaramin suka gabatar wanna karan ma sai da ya taimakawa Barrister Hadiza, sunyi namijin ƙoƙarin ganin cewa ba'a kuma ɗaga shari'ar ba saboda irin hazaƙar da sukayi dan har maganin da yayi shekaru na Maryama sai da aka kawo, aka gabatar aka kuma je aka buɗe asibitin aka ga irin nau'in maganin da allurai da suke ciki duk da sunyi expire amma irin su ne sak babu banbanci aka kuma kawo waccan shaidar ƙarar aka gwada aka ga ba iri ɗaya bane. Kotu ta gamsu iya gamsu, ta kuma aminta da irin shaidar su. Hakan yasa aka saki Daada bayan kotu ta wanke masa laifin da tas, su kuma aka ɗauri musu shekara shida na iya shekarun da Daada yayi, sannan kuma kotu ta bashi licenses ɗin sa na bude asibitinsa tare da kuɗaɗen da aka ci tarar sa aka kuma linka masa, sune za su bayar sannan aka rufe asibitin nasu.

Mutanen da basu san da zaman labarin ba sai a wannan Shari'ar ta biyu, sun taya shi murna ba sosai an kuma ya ɗaga a social media, haka kotun ta cika maƙil, kowa na so yaga Daada, Daada kukan da beyi ba shine a yanzu yake yi, sosai yake zubar da hawaye, haka ma Abba da Baba suna rungume junan su suna zabgar kayan su kamar wasu yara, sun bawa mutane da dama tausayi sun sa wasu zubar da hawayen da basu shirya ba.

~~~~~

Sajjad na dawowa gida yaga Inna a compound ga kuma kaya a gaban ta, hakan yasa shi zuwa zai wuce part ɗin sa.

Tace, "Sajad".

Ta faɗa da iya ƙarfin ta, dawowa yayi.

Yace, "Gani".

"Shiga ka kwaso mun kaya na, Bauchi zan tafi yanzun nan zancen maganar auren ka".

"Aure kuma  Inna?

"Ban sanar da kai ba? Ko kuma baka sani ba?

"Na sani".

Daga haka be ƙara cewa komai ba, ya shiga ya ɗauko mota jakar yasa mata a mota.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now