12

67 3 0
                                    

Cikin lokaci ƙanƙani ya haɗa mata light breakfast, a parlour ya  ajje mata yaje ya duba ko ya fito, ganin bata fito ba yasa shi komawa Kitchen yana kallon kayayyakin cefenen da ya siyo, ya rasa me zai haɗa, kafin idea ya faɗo masa ya fara haɗa pancake ganin akwai komai, yana yana leƙa ta ko ta fito, amma shiru bata fito ba sai da ya kusa gamawa sannan ya same ta har ta shirya ganin haka yasa shi komawa ya ƙara sa sai da ya gama tas, zai sa syrup ya tuna ashe basu da shi basu taɓa amfani da shi ba sai wannnan karon, shi kuma baya ci idan babu syrup.

Koda ya koma tana kwance ta sa doguwar rigar atampa ta wuce gwiwa kuma bata kai har ƙasa ba, sannan armless ce rigar da alama daman anyi ta ne don shan iska, murmurshi yayi mata yana ƙarasowa wurin ta, ya kama hannun ta suka fito. Sai da ya ɗauko pillow sannan ya zaunar da ita yana buɗe mata abincin.

"Duk kai kayi?

Murmurshi yayi mata kawai.

Yace, "Me zaki ci?

Maimakon ta bashi amsa, sai tace.

"Waya koya ma abinci haka?

Kallan da ya zuba mata yasa ta, sadda kan ta ƙasa bata kuma cewa komai ba, shima be kuma maganar ba ya zuba mata ta fara ci, pancake yana ɗaya daga cikin abinda da ta fito a abinci bata gajiya da shi gashi ta jima bata ci ba, hakan yasa ta ci dayawa sai da ta ƙoshi sannan ya haɗa mata magani ta sha kafin ya gama kwashe kayan har tayi bacci a zaune, zuwa yayi ya ɗauke ta ya shigar da ita ɗaki ya ɗauko saban bedsheet ya rufa mata. Bata tashi ba sai da akayi la'asar da wani sabon ciwon jikin ta tashi a lokacin baya nan haka ta tashi ta kuma yin wani wankan ta gasa jikin ta sannan tayi sallah a daddafe tayi sallar jin wani irin zazzaɓi na so ya rufe ta bata shirya masa ba, parlour ta fito taga kayan wankin su a jibge akan  kujera zaman tayi ta fara naɗewa cike da ƙarfin hali, sai ga shi nan ya shigo.

"Ke kika wanke min?

Ya faɗa yana ƙarasowa.

"Bansan sai yaushe zaka koyi sallama ba"!

Ta faɗa a hankali, kamata yayi yaji zafi jikin ta.

Yace, "Zazzaɓi?

Ya faɗa yana kallon ta, ɗaga masa kai kawai tayi shi kuma ya fice, bashi ya dawo ba sai da akayi Isha sannan ya dawo da nama da kuma Madarar shanu sai da ya dafa madarar sannan ya kawo mata tasha sosai ya bata naman shima ta ci kaɗan sannan yayi mata allurar sai da yaga tayi bacci kafin ya hau gadon yana kallon ta ya faɗa duniyar tunani. Kamata yayi ace yana cikin matsanancin farin ciki amma kuma wani sashen na zuciyar sa baya tare da shi, yana jin lalle  akwai wani abu da ƴan gidan su suke ɓoye masa amma sai dai koma meye yasan zai sani, sai ya basu masu mamaki babu wanda sai sanarwa da zuwan sa sai dai su ganshi, yayi niyyan siyan waya amma a yanzu ba sai siya ba kada ma wani daga cikin abokin sa ya kira shi kamar yarda ɗaya daga cikin abokinsa ne ya kira shi ya sanar da shi rasuwar Baffa babu wanda ya sanar masa daga gida, shiyasa a yanzu zai je gidan ya gaji da wannan ɓoye-ɓoyen da suke masa.

Juyin da tayi ne yasa shi kallan ta, yana jin wani irin tausayin ta gami da tsantsan so na ratsa shi, ko ja zai yi idan ya kai musu ita? Ko zasu karɓe ta? Ko za su sota kwatankwacin yarda suke san sa? Ko ya za su ji? Irin wannan tunanin yake har shima yayi bacci batare da yayi addu'a ba.

Washegari jikin nata yayi sauƙi sosai, koda ta tashi sai da tayi wanka sosai yau taji daɗin jikin ta, jikin nata ya sake jin ta take kamar ba ita ba, yana parlour yana naɗe kayan su ganin sa baya da walwala yasa ta itama tsuke fuskarta bata san wani abu da zai ƙara sawa su koma gidan jiya shiyasa take kaffa-kaffa dashi, haka suka wuni babu wani maganar arziƙin da ta haɗa su.

*****

Tana kallan sa daga kwancen da take yana shiryawa zai fita, a kwanakin nan  gaba ɗaya yayi wani iri da shi ya koma shiru-shiru kamar ba shi ba, ɗan neman faɗan ma da yake yi ya dena, haka duk wani gyaran gida da ya saba yi musu ya dena yin shi abinci kuwa sau ɗaya tak ya koma cikin sa, haka ma abu mai ƙara shiga tsakaninsu ba tun ranar nan. Tashi tayi zaune tana cigaba da kallan sa.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now