33

54 1 0
                                    

Yana jin su sukayi ta tsokanar sa amma be tanka musu ba, saboda yana san idan ta biyu, lamo tayi tana saurara shi kuma be san reni. Sai yamma aka sallame su suka koma gida, amma shi Sajjad ba gida ba ya koma wurin da aka kulle su ya nufa dake sun ji azaba sun faɗa wanda ya sani, da kuma duk wani abu da suka sani dangane da wannan harkar. Wanda ya sace ta a farko kuwa, Ogan su da ya sa su aikin a farko aka bashi ya kira aka ɗana masa tarko, a garin da yake suka sa aka kama shi da shi da sauran tawagar su. Ba shi ya dawo gida ba sai tara na dare, duk da haka be gama warkewa ba dauriya ce kawai yake yin ta, be zarce ko ina ba sai ɗakin da yake da tabbacin cewa tana nan.

Ɗakin duhu babu haske sai ɗan hasken dake shigowa ɗan kaɗan na bayan windown da take sai hasken system ɗin ta da take amfani da ita, ta ɗaura ta akan dressing mirror ita kuma tana zaune akan stool tana aikawa da Faisal saƙo, da wayar Al-ameen sukayi magana shine tayi connecting da WiFi ɗin gidan suke ƙara sa maganar su ta system. Kunna hasken da yayi ne yasa ta juyowa ta kalle shi, kallo ɗaya zaka masa ka gane ka baya da lafiya a kuma gajiye yake sosai.

Haɗa idan da sukayi ne yasa ta kauda kanta tana juyawa domin cigaba da abinda take yi. Jin ƙarar rufe ƙofa yasa ta ƙara juyowa sannan ta tashi ta sa hijabi akan kayan da ke jikin ta na bacci ta fito tabi bayan sa har ya kusa ƙofar fita.

"Nace ba".

Tayi saurin faɗa, yayin da shi kuma ya juyo yana lumshe ido, so yake kawai a yanzu ya kwanta. Batare da yayi magana ba ya tsaya yana kallon ta har ta ƙara so kusa da shi, hannu tasa ta taɓa goshin sa, tana cewa.

"Jikin ka da zafi".

"Kuma baka ci abinci ko ka ci?

Tayi masa maganar ɗaya bayan ɗaya tana kallan sa, shi kuma shiru yayi mata yana lumshe idan sa. Sam be kawo a ka ba zata kula da shi har haka, ko ba komai ya ji daɗ, sai ma wani irin ƙarin gwiwa da ya ji yana zuwar masa duk da ba kawo zai iya cin abinci a yanzu ba, wanka kawai yake da baƙutar yi amma ba zai iya gujewa tayin ta ba duk da yana jin haushin ta.

"Uhmm?

Ta faɗa cikin alamar tambaya.

"Ka ci ne?

Girgiza mata kai yayi.

"To muje ka ci".

Ta faɗa tana jan sa, shi kuma ya bita yana ƙare mata kallo. Taja masa kujera ya zauna sannan ta shiga kitchen shayin da suka sha ɗazu ta ɗiba ƙofi ɗaya ta ƙara tafasa masa shi ta kawo masa. Shayin ya fara sha kafin ta zuba masa abincin, kaɗan kuwa ta zuba masa dan tasan ba lalle ya wani ci da yawa ba, ta nemi waje ta zauna tana kallan sa, yana cin abincin yana shishitu na ginger dake cikin shayin, duk da haka be cinye ba abincin amma ya shanye shayin tas.

"A ƙaro ma?

Girgiza mata kai yayi, yana tashi ya so yace ya gode amma kuma ba zai faɗa itama ta fara jin babu daɗi. Ita kuwa ko a jikin ta, tana zaune da sauri ta riƙe hannun sa.

Tace, "Maganin ka a wurin Ya Aliyu".

'Iyayi' ya faɗa a zuciyar sa. Ɗaga mata kai kawai yayi.

"Dan Allah ka sha".

Ɗaga mata kai ya kuma yi sannan ya fice, ita kuma ta kwashe kayan ta kai kitchen sannan ta koma ɗaki bayan ta kashe komai, duk da bata sani ba ko idan mai gidan ya fito zai yi hakan.

Washegari da safe shi kaɗai ya tafi wajen meeting suka je suka tsaida matsaya ɗaya akan aikin ta baro musu batare da tasan wanne irin aiki ne ta gingumo ba wai ita gwana. Sun tsaya akan cewar za su je har inda yake ya kuma yarda da hakan. Suna fitowa daga meeting ɗin ya koma gida ba su wani ɗau lokaci ba suka juya babu yarda Al-ameen be yi da shi ba akan su tsaya su kwana amma yace shi be san zance ba, aka kai su airport suka koma. Daga ita har shi babu wani mai yiwa ɗan uwan sa magana har suka iso, ita bata ce da shi komai ba, shima kuma be ce da ita komai ba, yana jira ta fara masa magana yayin da ita kuma ta rasa me zata ce da shi.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now