36

53 0 0
                                    

Bayan sun gaisa, kowa yaja bakin sa yayi shiru yayin da, Nilah take so ta tambaye ta amma ta kasa. Kawai yarinyar take bi da kallo tana jin tausayin ta, babu wannan kazar kazar ɗin na yara a tare da ita.

"Dan Allah...."

Ta fara faɗa sai kuma tayi shiru. Kallan ta Zainab tayi alamar tana ji sai kuma kawai tayi ɗan murmurshi.

Tace, "Ai bansan ya zaki ɗauki maganar ba".

Sai tayi shiru sannan ta sake cewa.

"Meya sa Sajjad ke maki abinda yake yi? Bayan nasan hakan ba halin sa bane ba ?

Ɗan murmurshi Zainab tayi.

Tace, "Meyasa kike san ji?

"Saboda bana san abinda yake maki".

"Idan kinji me zaki yi akai?

"Na gyara tsakanin ku".

"Ba zaki iya ba".

"Me yasa kike tunanin ba zan iya ba?

"Bansan meke tsakanin ku da shi ba, amma tabbas nasan ba zaki taɓa iya gyarawa ba. Ya min tsanar da ba zata taɓa gogewa a cikin kwanyar kan sa ba. Koda kuwa yayi loosing memory ne ya dawo hakan ba zai taɓa faruwa ba".

"Amma idan hakan ta faru fa?

Shiru Zainab tayi.

Tace, "Kinga mu bar wannan maganar, ki faɗa min dalilin da yasa ya maki wannan tsanar".

Idan ta da ya ciko da hawaye tasa hannu ta goge.

Tace, "Sa Farko sunana Zainab, mu ƴan kafacen ne, amma muna zaune a cikin garin Kaduna. Mahaifinmu ya rasu ya bar mana dukiya, baya da ɗan uwan da suke uwa ɗaya dashi sai ƴan uba, Yayan Baban mu kuma yace ba zai riƙe mu ba sai dai idan Maman ta aure shi, babu yadda ta iya ta aure shi, muke zaune a cikin gidan mu, har mukayi University. Haɗuwa ta da Aliyu sai ta sauya min rayuwa ta gaba ɗaya ina da burin yin karatu da yawa amma dana haɗu da shi sai komai ya sauya. Ba iya shi kawai yake so na ba, hatta ƴan uwan sa da Iyayen su suna sona anan na gane wata Soyayya. Sajjad duk ya fi su sona, duk da cewar yana bani labarin ya canzawar sa da yayi na  dena magana da wasu abubuwan amma ni bangani ba. Koda auren mu ya tashi babu irin mugayen da ba'ayi ba akan Mahaifin su da kuma ita kan ta Antyn, Uncle Sagir yana ɗaya daga cikin wanda baya so, ɗaya daga cikin Ƙannan Babana, haka de aka yi auren, ta shigewae dangin Mahaifiyata.  Bayan auren mu duk sati saki gan shi yaje Abuja dan kawai mu gaisa, ya girmeni amma yana bani matsayina na Matar yayan sa, bama shi kawai ba har su Yusuf da Hafiz duka suna bani wannan girman da kuma matsayin, ba kuma ga ni kawai ba dukkan gidan haka ake. Akwana a tashi muka dawo hutun Sallah anan Kawuna Uncle Sagir ya fara bibiyata akan yana neman wani abu daga gareni, na ruguza ahalin su, wanda naƙi yarda, maimakon nayi sati biyun da zan yi sai nayi sati ɗaya na koma gidan su na ƙara sa ɗayan, muka koma. Duk da hakan sai da ya cigaba da bibiya ta, ya ce kuma idan na sanar da Aliyu sai ya illata shi, kuma a lokacin Aliyu sunyi Accident shi da Al-ameen wanda yace shine dalilin yin accident ɗin nasu, Allah ya rufa asiri basu ji mugun rauni ba. Nayi shiru bansanar da kowa ba. Har Allah ya azurtani da samun ciki, kar ki so kiga irin murnar da  dukan su sukayi, tsakanin Sajjad da Al-ameen bansan waya fi wani zumuɗin ganin yaron ba, kasancewar ita Matar Al-ameen bata samu ba, duk da kuwa tare akayi bikin mu. Lokacin haihuwa na yayi muka dawo gidan su da zama, a lokacin kuma yace muddin ban yi abinda ya sani ba, sai ya illata mu, mu dukan mu. Tsoron hakan da naji yasa na yanke shawarar rabuwa da shi, bangama tunani na ba na fara labour, aka akai ni asibiti, na haifi yaron, ina tashi daga bacci aka ce min ya rasu, a lokacin babu kowa a ɗakin sa Aliyu. Irin mugayen kalaman da na jefe shi da su be sa ya sake ni ba, sai da nace ya sake ni. Ashe Sajjad yaji dukkan abinda nace ga ɗan uwan sa, tun daga nan ya tsane ni.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now