38

64 2 0
                                    

Gidan yana nan kamar yarda suka san shi, sai wani canji da ya kuma samu na wasu abubuwan. An kuma ƙawata mashigar gidan da jeren wasu irin nau'in  fruits, sai flowers gwanin ban sha'awa, ga sanyi da duhu wajen, abin gwanin birgewa. Cike da fara'a Nilah take kallan wajen ƙwalla na cika a idan ta. Yayin da shi kuma Sajjad yaja gefe guda ta jingina da bisha yana kallon ta daga ita har yara yana jin wani irin farin ciki na ratsa shi. Yau ga Hauwa'u Nilah ya kawo masa idan yagan ta ko wanne irin farin ciki zai yi?

Yayin da Baba Garko kamar kullum yana wurin yana aikin tone ƙasa zai dasa wani abun, yaji hayaniyar yara sama-sama haka, sai ya tashi yana magana cikin fillanci yake tambayar waye  anan?

Jin maganar sa yasa ta maida kallan ta ga inda take jiyo maganar, zai sake magana idan ta ya shiga cikin nasa, kamilin dattijon mutum mai cike da haiba, ma'abocin murmurshi da sanyin hali, kamanin sa suna nan sai tsufa da ya ƙara na manyance da yayi. Haka shima a ɓangaren sa be manta da Nilah ba, duk da cewar ta canza sosai, tayi ƙiba ba Nilahr da ya sani bace amma hakan ba zai kasa gane taba.

Hawayen da bata sani ba ne suke tseren tsere a saman kuncin ta, yayin da ta kai duban ta ga Sajjad dake kallan su yarda kowa yayi surrender yana kallan kowa, lumshe mata ido yayi ya buɗe hakan yasa bata yi wata wata ba ta kwasa a guje tayi wajen sa, sai jin ta yayi a cikin jikin sa, hakan yasa hawayen da yake maƙalewa  suka zubo masa, ya manta da cewar ƙasa ce a hannun sa ya fara shafa kan ta yana magana cikin fillanci, babu abinda take yi sai ɗaga masa kai.

Jiddah ce uwar ƴan surutu taje wurin Sajjad.

Tace, "Wai meyasa Mammy take kuka?

Tsugunnawa yayi.

Yace, "Kukan daɗi take. Ta jima batagan shi ba ne shiyasa take kukan daɗi".

"To ko shi yasa ta kuka?

"Kukan murna ne fa".

"Dagaske kake?

Wannan yarinyar da shegen wayo take.

Yace, "Dagaske nake".

"To kuma idan zamu tafi zai samma mana wannan abubuwan?

"Idan ya baki ta ina zaki ci?

Wangale masa baki tayi tana nuna masa ta gefen haƙurin ta mana.

"Kuma ai haƙogin nawa ya faga fitowa". 

"Haka ne".

Ya faɗa yana maida kallan sa gare su, ganin sun yi cikin gida yana jan hannun ta yasa shi nufar su shima yana jan hannun Jiddah dan Maryam ta ja hannun Hauwa da kuma Abie sun shiga kasancewar ta kamar ƴar gida duk da har yanzu ba sa maraba da ita.

Kowa tsayawa yayi da abinda yake yi cike da mamaki suna kallan sa, yayin da shi kuwa Baba Garko wani irin sihirtaccen murmurshi ke fitowa daga fuskar sa cike da fara'a yake cewa.

"Yau Hauwa'u ta dawo tare da mijin ta. Ina kuke ku zo ku ga Hauwa'u ta dawo da mijin ta".

Babu wanda ya iya motsi a cikin su, sun ɗauka cewar Nilah ba zata taɓa dawowa ba sai gashi ta dawo abin sai kace wani irin almara haka shekara da shekaru fa kenan amma sai yau ta dawo? Ikon Allah ya fi ƙarfin sarki wasa, hakan ma dan ba su ji taya ne ta dawo ba.

Ɗakin Baba Garko suka nufa su dukan su, suna zama aka fara kawo musu abinci kowa ya fara shigowa yana lalle maraba, kafin lokacin sallah yayi suka fita shi da Sajjad a masallaci ya faɗa cewar jikar sa ta dawo, anan fa aka fara yi masa murna ana zuwa har gida ana ganin ta ana mata sannu da zuwa tare da kawo abubuwa iri-iri. Har yamma ana faman zarya, mutane har mamakin Baba Garko suke dan yarda yake farin ciki da dawowar ta abin ya wuce misali, ƙarin farin cikin sa kuma da yaji su Abie ƴaƴan su ne. Yamma lis sai ga Mahmud da matar sa da kuma ƴar sa mai sunan Nilah. Tunda suka zo Sajjad ya karbi yarinyar yake riƙe da ita, duk inda za su je da ita, haka suka zagaye garin nan suna tuno rayuwar su, har inda suka fara haɗuwa da ita sai da ya kai shi.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now