31

55 1 0
                                    

Ɗakin da take ciki ta ƙare wa kallo, babban ɗaki ba kuma ɗakin ne na ya ku bayi ba, ɗaki ne babba wanda aka kashewa kuɗi tun daga ceiling ɗin ta gane hakan, ga kuma inda take a kwance shima wani irin haɗaɗɗan katafaran gado ne mai take kai sai dai kuma ko ledar dake kan gadon ba'a cire ba alamu na saban ɗaki ne inda aka sata. Idan ta ne ya sauka akan agogon dake ɗakin wanda ya nuna mata bakwai saura minti goma. Tunowa tayi a lokacin da ta duba wayar ta bayan ta wanke fuskar ta ta fito daga office ɗin aka ɗauke nepa shine ta tsaya domin ɗauko wayar ta, ta haska taga goma da minti sha biyar daga nan bata san me ya faru ba kuma sai yanzu shine zata ga  har lokaci yayi haka?

Yunƙurawa tayi ta tashi domin shiga toilet, taji kan ta yayi wani irin ciwon juya ta ɗiban ta, daƙyar ta samu ta lallaɓa tana bin bango daƙyar ta nufi inda take da tabbacin toilet ne, sai dai ga mamakin ta ba toilet ɗin bane, parlourn ne ƙarami wanda yaji kayan ado, babu wani takarce da yawa gwanin ban sha'awa, ƙaramar ƙofar da ta gani guda biyu a parlourn nan ta nufa  ta buɗe ɗayar taga bene ne wanda zai sadaka da ƙasa, hakan ya nuna mata  kenan a sama take, sai ta rufe ta buɗe ɗayar anan taga toilet ɗin, ta shiga tayi abinda zata yi ta fito a daddafe ta kuma komawa ɗakin, ɗankwalin ta ta cire ta shimfiɗa ta tada sallah. Tana idarwa ko addu'a baya gama ba kawai ta kwanta ta koma bacci saboda ciwon da kan ta yake mata ga kuma juwa dake ɗiban ta.

Ƙafar da aka take mata yasa sakin ƙara mai nuni da cewar taji zafi da kuma firgicin mai bacci na tsoro, kulle idan ta tayi gam tana jin zabar da ƙafarta ke mata batare da ta kalli  wanda ke mata wannan muguntar ba.

"Ya isa haka".

Taji an faɗa, ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta ja ƙafarta ta jingina da jikin gadon tana sauke numfashi.

"Ke!

Tana nishi ta buɗe idan ta, ta sauke shi fes akan wanda tagan shi yana waya da yaren ta.

"Sunana Bashari, ko kin san ko baki sanni ba bashi ne damuwa ta ba, damuwata dake shine, shirina da kike tarwatsawa".

Ɗan murmurshin takaici tayi.

Tace, "Shirin ku zaka ce na shirin ka kai ɗaya ba".

"Hakan ya min daɗi tunda kin san ba ni ɗaya bane".

"Me ye dalilin ka na kawo ni nan".

"Ina so naji, meye alaƙar ki da wannan companyn da kike ƙoƙarin salwartar da rayuwar ki saboda shi?

"Idan kaji alaƙa ta dashi me zaka yi? Me zaka iya? Kana da abinda zaka yi ne? Ko gargaɗina zakayi?

Shiru tayi tana tsare shi da ido yayin da shima ya zuba mata idon yana kallon ta.

"Ke kina tunanin zaki koma ne?

"Ko ban koma ba ina da wanda zai cigaba daga inda na tsaya".

Tas! Ya wanke da mari, rufe idan ta tayi ta buɗe a kan sa.

Tace, "Ba mari ba, ko kashe ni zaka yi sai dai kashe amma sai na faɗa".

"Faɗa min shi waye?

"Ohh! Marin da ka min kenan dan na faɗa maka waye shi? To ai da kashe ni kayi da sai yafi mana sauƙi. Kaga baka wahalar da ni ba, ba kuma ka wahalar da kan ka ba".

Kallan samudan dake tsaye a kan sa yayi alamar ya cigaba. Shi kuma tashi ya ƙara falla wani marin, yayin da basamudan ya cigaba da take mata ƙafa. Marin da yayi mata shi kuma yayi sanadiyar da yasa kan ta ya bugu da jikin gadon, bata ɗago ba ya kuma gwara kan ta a jikin gadon, azaba biyu ce take sha, ga ƙuma kai ga kuma taka mata ƙafa da ake yi, sai da suka sumar da ita sannan suka haƙura. Amma duk da hakan sai da suka kawo ruwa mai sanyin gaske suka sheƙa mata. Sannan suka tafi suka bar ta tana karkarwa.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now