35

55 0 0
                                    

Batasan ya akayi ba sai kawai ganin ta tayi a jikin Barrister ta ƙamƙame ta tana sakin kuka mai cike da damuwa da kuma farin ciki. Yayin da itama a nata ɓarin Barrister haka ne kuka ne na farin ciki take saukewa da kuma damuwar da take ciki ta ƴar ta. Ta manta da wata kunya ta ƴar fari wacce aka san Fulanin asali na da ita. Yayin da ƴan gidan suka tsaya suna kallan su kawai suke da mamaki da kuma ya akayi hakan ta kasance? Sajjad kuwa tashi yayi tsaye kawai ya naɗe hannunsa a ƙirjinsa yana kallon su, cike da so da ƙauna da kuma wani irin ratsatstsan farin ciki da ke ratsa shi ta ko ina. Tabbas yasan yana yiwa Nilah SO idan aka ce so ba wai son da aka sani ba, a'a sone dake shigar mutum batare da ya shirya yi masa hakan ba, so ne da zai iya basa rayuwar sa saboda ita ko da kuwa ita bata san shi. Ajiyar zuciya ya sauke yana cigaba da kallan su. Yayin da Abba ya taso daga inda yake ya zo kusa da shi saboda tunda suka fito daga mota yake kallan sa ganin yana ɗingisa ƙafar sa sannan kuma ta cikin takalmin ya ga kamar an sa abu an ɗaure ƙafar.

"Auta meke damun ƙafar taka?

"Ciwo naji".

"Muje a duba a ƙafar".

"Amma ita kuma fa?

Ɗan murmurshi Abba yayi.

Yace, "Tana nan mana, ba inda zata je. Muje yanzu zamu dawo kafin ayi magriba".

Ya kama hannun sa suka shiga mota, asibitin da baya da nisa da su suka je za'ayi masa treatment ɗin ciwon da ya ji.

Nilah kuwa ta shaƙi kukan ta gaji tayi lamo ajikin Mahaifiyar ta, tana sauke ajiyar zuciya ta lumshe idan ta. Yayin da Ummi da Mama suka cigaba da hiran su sai dai hiran na su sama sama yake domin kuwa Anty ta jima da lulawa duniyar tunani bata tare da su, tun farkon shigowar su take kallan sa tare da Nilah a kallo ɗaya kawai ta gane su dukan su suna matuƙar ƙaunar junan su,  ta tabbatar da ita ce wacce su Abdulmajid suke faɗa ganin tarin farin cikin da ta jima baya hango ba a idan ɗan nata, a yadda kuma ta ga yadda tarbiyyar yaran ta suke, ta tabbatar ta sami cikakkiyar tarbiyyar da ake so kowa ya kasance cikin ta, a yanzu kam bata da wani burin sake gani sama da farin cikin Aliyu duk da tasan shi Aliyu ba bazai taɓa farin ciki ba muddin be ga ɗan uwan sa yana farin ciki ba, zai iya yin komai domin ganin wannan farin cikin ya dawwama a fuskar sa bata da matsala da Aliyu baya da matsala shima, daman Sajjad ne kuma shima Alhamdulillah, yanzu me take jira kuma a duniya? Rayuwar ta ta rigada tayi nisa bata san zata ƙara adadin wannan shekarun ba haka. Ta manta cewa wasu suna share sama da shekaru goma a kwance kuma su tashi. Kallan ta ta kai wurin su Nilah dake kwance har yanzu a jikin Mahaifiyar ta bata tashi ba ita kuma Mahaifiyar ta ta cike da kulawa take shafa kan ta, kewan junan su take hangowa  daga gare su har yaushe suka kai basa tare da juna? A hankali taji jikin ta yana sauya, zuciyar ta dake mata zafi da zugi ta sauya launin bugawar da take yi, daman tasan daƙyar ne idan zuciyar ta ba zata buga ba saboda irin abubuwan da ta shaƙo da suka je Bauchi babu ranar da zata zo ta fice ba'a faɗa mata magana mai zafi ba, idan aka ga ita kadai ce babu irin abinda baza'a faɗa ba, kuma can ba wani san ta suke ba irin sosai ɗin nan ba, saboda ita ba ƴar Bauchi bace ƴar Kano ce dan haka ba'a cikin family ɗin su take ba shiyasa ma tsanar ta fi karfi.

Nilah da ta buɗe idan ta, domin ta ɗago ta kalli Mahaifiyar ta ce taga halin da Anty ke ciki, da yake tana kallon facing ɗin Anty ɗin ne, da wani irin sauri ta tsalleke Mama ta isa wurin ta tare da tare ta, tana ambaton zata faɗo, shine ya ja hankalin su suka tashi suka ƙara sa wurin ta, Daada na zuwa be wata wata kawai ya ɗaga ta cak yayi wurin mota da ita Baba ya ɗauko mukulli dan duka drivers ɗin basa nan, gaba ɗaya hankalin Daada  ya tashi ganin bata numfashi be ƙara sa wurin motar ba ya sauke ta a ƙasa a matsayin ya shiga danna mata ƙirji da sauri yayin da matan suka rufe shi gaba ɗayan su sun ruɗe. Nilah dake tsugunne a kusa da ita ya miƙawa hannunta ɗaya take murzawa da sauri, da sauri kuwa ta amsa ta shiga murzawa, har sai da suka samu taja dogon numfashi sannan aka sa ta a mota suka tafi asibitin dake kusa da su suka nufa wanda  su Sajjad suka je acan suka haɗu da su. Zo kaga tashin hankali a wurin Sajjad gam ya riƙe ta yace ba zai sake ta ba daƙyar aka samu ya sake ta aka shiga da ita.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now