41

68 1 0
                                    

Da daddare yana zaune kawai shi  kaɗai yayi shiru, yana tunanin Anty, shigowar Aliyu yasa shi sauke tagumin yana kallan sa. Girgiza kan sa kawai Aliyu yayi  tare da zuwa inda yake.

Yace, "Tunanin ba zai ƙare ba?

"Yaya Aliyu taya kake tunanin tunani zai ƙare?

"Ba zai ƙare ba, amma Sajjad zai ragu".

Kallan sa yayi sai yaji wani irin tausayin su na kama shi, yanzu shikenan babu Anty fa. Ƙwalla da ta cika idan sa ne ta zubo yasa hannu ya share.

Yace, "Yaya Aliyu. Har yanzu banji Anty ta tafi, har yanzu na kasa yarda da barin Anty a rayuwar mu".

Rungumo shi Aliyu yayi yana bubbuga bayan sa, cike da kulawa, bece masa komai ba, duk da shi nasa da sauƙi sosai idan aka haɗa da nashi zafin dake cikin zuciyarsa, zuciyar sa wani irin zafi da raɗaɗi take masa, shi nasa yana da wacce take san sa, shi kuma fa?

Kamar Sajjad yasan tunanin da yake ya zame kan sa yana goge hawayen sa.

Yace, "Yaya Aliyu kasan me?

Girgiza masa kai yayi.

Yace, "Ashe Zainab na san ka daman ?

Ɗan murmurshi kawai yayi.

Yace, "Waya faɗa maka?

"Ita ce mana..."

"Ita de..."

Aliyu ya tari numfashin sa murmurshi na san ƙwace masa, kumbura fuska yayi yana ƙokarin tashi.

Yace, "Na fasa faɗa maka".

Kamo hannun sa yayi.

Yace, "Yi haƙuri zauna".

Komawa yayi ya zauna yaƙi kallan sa.

Yace, "to faɗa min".

Kamo fuskar Aliyu yayi da duka hannun sa.

Yace, "Ashe tayi ne saboda irin tarin san ka da take yi ɗan Yayana Yaya Aliyu".

Ya faɗa yana kama kuncin sa, kamar irin yadda ake yiwa yaran nan. Da gudu ya tashi ya fice, rasa me zai yi yayi kafin ya girgiza kan sa kawai yana sakin murmurshi.

"Ba zai taɓa canzawa ba".

Ya faɗa yana ƙoƙarin tashi yaga kiran  Unaisa, ɗagawa yayi kafin yayi magana.

Tace, "Allah yayi na sauka lafiya".

"Masha Allah. me muka samu".

Ya faɗa cike da zumuɗin me aka samu.

"Namiji ne".

Ta faɗa, dan taji wanne irin expression zai yi sai dai yarda taji yayi ɗin yasa ta bata mamaki kenan su duk wanda aka haifa suna maraba da shi? Su wannan wanne irin family ne haka?

Tace, "da mace".

"Twins ne?

"Eh".

Ji tayi ya kashe wayar gaba ɗayan ta, be nufi cikin gida ba ya fita daga gidan, shopping yaje ya haɗo musu kamar wanda za su buɗe ƙaramin shigo. Yaje ya ga yaran banda murna babu abinda yake ya ɗauke su yana ta kallan su, wasu daga ƴan uwan ta sun ɗauka shine Baban yaran nan, hotuna kam sun sha hotuna kamar kamar me, daƙyar ya haƙura ya ajje su ya tafi gida lokacin shaɗaya na dare yayi, a parkourn Sajjad ya same su, yana shigowa duk suka zuba musu ido. Wurin Al-ameen yaje ya zauna.

"Wannan dariyar fa?

"Unaisa ce fa ta haihu".

Da mamaki ya juyo yana kallan sa, kafin yace.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now