45

70 0 0
                                    

Inda aka kai shi babu abinda ake masa sai ganar da shi a azaba domin sun ce ba za su kai shi kotu ba, tunda ya sanar da su halin da shi kan sa Alƙalin ya shiga bima'ana ya siye shi. Hakan yasa suka kulle shi a cikin wani ɗakin mai bala'in sanyi suka ganar da shi azaba, yayin da Yahaya Sabo ya gane Allah ɗaya ne, ya kuma tabbatar da babu wani Sarki sai shi. Sai a yanzu yayi nadamar rayuwar sa, yanzu ne ya gane kuskuren sa, yake so a bar shi ya gyara kafin lokacin mutuwar sa ya ƙara sa. Tunda yasan da Azahar zai mutu shine lokacin da suka kawo masa ziyara. Tashin farkon da suka gama jibgar sa, babba daga cikin su ya sami kujera kusa da shi ya za ya zauna, sannan ya kama hannun sa guda ɗaya ya sami yatsun sa biyu yana kallan sa, ganin kallan da yake masa yasa shi cewa. "rufe idan ka". Idan nasa ya rufe ruf jikin sa yana ƙyarma dan ya tsoro ta da su sosai. Kallan na gefen sa yayi aka miƙo masa wani abu, gif yasa ya yanke hannun, wata irin azaba yaji da yasa buɗe idan sa yana kwarma wani irin uban ihu ya kasa ƙwace hannun sa yana kallan ɗan yatsan sa a ƙasa. Ihu kawai na azaba da raɗaɗi yake ji sosai, faɗar irin zafin da yake ji ba ba zai faɗu ba.

"Tambayar ka zan yi. Idan baka amsa ba min kuma zan yanke maka duka yatsun ne".

Ya faɗa yana ƙara kama ɗan yatsan nasa na biyu da ya riƙe.

"Zan faɗa".

Ya faɗa hawaye shaɓe shaɓe yana ɗaga kai.

"Waye ka sa aiki".

"Wani ne".

"Nasan wanin ne ai. Waye shi? A'ina yake?

"Sunansa Usman, sun yi karatu tare da Sajjad acan ƙasar waje, yace min yana so ya ɗau fansa ne akan sa, saboda Sajjad ya raba shi da budurwar sa, wata ƴar Mumbai India, ni bansan ya akayi ba, shine Jibrin ya haɗa mu da shi, shi kuma Jibrin ɗin yana yiwa su Sagiru aiki shine muka sa shi domin ya kashe Sajjad ɗin kawai kowa ma ya huta".

"Me yasa kake so ka kashe Sajjad".

"Saboda shine kowa a familyn su yake so, sukan sadaukar da farin cikin su saboda shi. Saboda shi ne Mahaifin su ya tafi prison badan shi ba, babu yarda za'ayi wannan mutumin yaje shi. Da tura ɗan sa Taraba da binciken da ɗan sa ya fara akan asibitin Mahaifin nasa, shine kuma wanda ya auri matar da yaro na yake so, ya aura saboda kuɗin Mahaifinta".

Shiru yayi yana ganin yadda ake masa treatment ɗin hannun sa, kamar ba mutum suke gyarawa.

"Ina sauraro".

Dawo da kan sa yayi kam Ogan nasu.

Yace, "Shine dalilina bama ni ɗaya ba har su Dr. Ismail, kowa burin sa be wuce suka ga wannan ahalin a cikin kangin wahala ba. Idan aka kashe Sajjad  tabbas ko shakku bana yi sai sun shiga halin mutuwa kamar de yadda..."

Sai yaji shiru ya kasa ƙarasawa.

"Yarda ka kashe masu Mahaifiya ko?

Jinjina kai kawai yayi.

Yace, "Duk wani tunani da zakuyi na wuce inda kuke zato".

Murmurshi sojan yayi.

Yace,"Haka muma duk inda kake tunanin mun wuce inda kake zato".

Shiru yayi.

Yace, "Ka nuna nadama, dana sani ƙarara a fuskar ka. Kana so a bar ka ka huta ko? Kana so a barka ka gyara kuskuren ka ko? Alhali kuma a zuciyar ka ba haka bane ba".

Kallan shi Yahaya Sabo yayi kawai, dan be san lokacin mutuwar sa ya kusa ba kenan kome?

"Ga ruwa kasha idan baka san ka mutu saboda abinda aka zuba maka a jiya".

Da sauri ya karɓa ya kafa kai ya kashe tas daman ƙishin ruwan yake ji, duk da hakan ma be ishe shi ba.

"Me kuma kake so kafin ka mutu?

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now