29

58 2 0
                                    

Washegari kasancewar basa nan yasa ta tashi da wuri ta shirya tsaf abinta ta gyara ko ina na gidan ta kuma duba jakarta sannan ta kwasa da lunch box ɗin su ta fita zuwa office ɗin, babu wanda ya fara zuwa sai masu aikin share-share kasancewar sune suke fara zuwa domin gyara office ɗin kafin ma'aikata su zo. Office ɗin ta, ta wuce taga mai shara na sharewa hakan yasa ta karɓa tace zata yi kada ya damu, tas kuwa ta share ta gyara haka ma office ɗin sa shima ta gyara ta kwashe kaf takardun wajen ta zuba a inda aka tanada domin su a daga gefen office ɗin, ba abinda ta bari akan table ɗin  landline sai pen stand shima a cikin drawer ta ɗauko shi haka ya bar birikan a barbaje  kuma wai a hakan kullum sai an gyara.Magana ta musu cewar ta gyara ya kawo mata freshener ta fesa ta saki curtains ta kunna ac. Ta nufi office ɗin ta, ajiyar da tayi taje ta ɗauko, ta nufi ƙofar da take da tabbacin ƙofa ce a wurin, tana shiga kuwa taga ɗan office ne ƙarami amma kuma ko ina akwai tv irin de gidan tvn nan ko inda ake duba CCTVs, wurin ta ƙare wa kallo kafin taga babu inda zata ajje tunda ba wani space ne a ɗakin ba, har zata juya sai kuma idea ta faɗo mata, a ƙasan table ɗin zata iya ajjewa tunda, haka kuwa ta yi ta bi ta jera su kaf a wurin, babu yarda za'ayi kace a wani abu a wajen, sannan tayi saurin ficewa.

*****

Daƙyar ta tashi da asuba yaje sallah, yana dawowa ta she su, sallah ya fara sa su sukayi sannan aka zo wanka.

Jiddah tace, "Nidai wugin Mammy zan je".

Ta faɗa tana wani cune baki.

"Naji, zaki je amma muje ku gaisa da Anty da Mama da kuma Ummi".

Abie yace, "Su waye ?

"Duka mamomi na ne".

"Kuma su dukan su".

"Ehh mana, kai ma sun zama Maman ka ko? Tunda kai kana jin magana ko?

"Ai ni ma ina ji".

Jiddah ta faɗa ganin zasu ware ta.

Abie yace, "Daddy bata jin magana fa, kullum sai Mammy ta mata faɗa lanal nan har dukan ta tayi".

"Ai kaima baka jin maganag".

"To naji kuyi haƙuri muje".

Ya faɗa yana jan hannun su, suka fita, duk da ba'ayi shiru ba sai da aka cigaba da yi, part ɗin Anty ya fara zuwa suna ɗakin Daada ya sani, hakan yasa su nufar parlourn na Daada lokacin gari har rana ta fara fitowa, suna zaune a parlour kamar yadda ya tsammata sai da aka amsa masa sallamar aka basu izinin shiga sannan suka shiga, a ƙasa ta zauna ganin haka yasa suma suka zauna a ƙasa, sai kalle-kallen su suke abin su, gidan yayi musu kyau sosai.

"Ina kwana Daada?

Daada beje ga amsawa ba, suka faɗa a tare.

"Ina kwana".

"Lafiya ƙalau Alhamdulillah sannun ku".

Ya gaida Anty, suma suka gaida ta, Daada kallan yaran yake, kallo kuma yaƙi ƙare wa na irin sune yaran da Anty ta bani labarin nan?

Anty tace, "Sune yaran?

"Ehh".

Ya faɗa kan sa a ƙasa.

Daada yace, "Ku zo, ko shi kaɗai kuka sani".

Sai da suka kalle shi, yace su je sannan suna je.

"Ya sunan ku?

Jiddah tace, "A makaganta ana cemin Hauwa'u Ahmad a gida kuma Jiddah shi kuma a makaganta Ahmad Ahmad a gida kuma Abie".

Ko ina mai surutu mai surutu ne baya canzawa, ba kuma zai canza ba, yayin da shi kuma Abie yayi shiru be ce komai ba, yaran ba ƙaramin burge Daada sukayi ba, haka itama Anty, hannun Abie ta ja ta zaunar a kusan ta.

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now