4

94 1 0
                                    

Washegari suka je asibitin dake ƙauyen sai dai kuma aka ce sai dai su je Gassol su kai report ɗin nasu shima wani Nurse ne ya faɗa musu bayan ya karanta ya gani, dolen su suka je suka kai sannan suka dawo to daman babu nisa kuma da suka je ba'a wani ja musu aji ba aka karɓa. Koda suka koma aiki suka fara yi, asibitin ba wani babba bane Labour room ne sai ɗaki biyu babu ma offices ɗin Likita kawai wuri ne ƙatan gaske sai benches da aka saboda marasa lafiyan sai kuma table da kujera da aka sa kowacce kusurwa, sai ɗakunan ɗaya Labour room ɗaya kuma na maza ɗayan na mata inda ake kwantar da su sai toilet shima daga waje yake asibitin kuma ba'a zagaye yake ba. Sannan maganin da suka duba duk yayi expire hakan yasa ake rubuta musu suje su siya, koda suka duba Labour room ɗin ma babu wani abun azirki a ciki. Sajjad ne da baya yin shiru bayan sun dawo sun zauna ya kalli Nurse ɗin da ya ce musu Gassol za su je.

Yace, "Wai kai meye sunan ka?"

Murmurshi mutumin yayi.

Yace, "Habib".

"Kaima anan kake?"

"A'a daga Gassol aka turo ni aiki anan".

"Kuma kai ɗaya kake zuwa? Ko kai ɗaya aka turo?

"Ai dake ƙauye ne mutane basu cika zuwa ba, a cewar su yayi ƙauye da yawa shiyasa".

Jinjina kai kawai yayi.

Mahmud yace, "Ka jima kana aiki anan?

"Ehh dan zan kai shekara gaskiya".

"Amma ya naga duk asibitin wani iri haka?

Murmurshi yayi.

Yace, "To kunsan halin da ƙasar ta mu ai ba sai na faɗa ba".

"Bakayi complain ba?

Sajjad ya faɗa.

Wani murmurshin takaici yayi.

Yace, "Ahmad ko?

Jinjina masa kai Sajjad yayi.

Yace, "Complain ba ɗaya ba ba biyu ba duka nayi amma a banza yake tafiya na takaice maka har gidan Radio naje amma a banza".

"Kuma babu abinda akayi akai?

"Kamar yadda ka gani".

Jinjina kai kawai yayi be ƙara magana ba sai ƙare wa asibitin kallo kawai yake, kafin ya tashi ya fita ya sami can wajen bishiya ya tsaya. Zai kira Abba kenan kiran Aliyu ya shigo.

"Yaya Aliyuuuuna".

"Ka tashi lafiya?

"Alhamdulillah ya aikin?"

"Alhamdulillah, hope komai lafiya? Kunje kun kai report ɗin? Ya asibitin? Ya aikin ?"

"Yaya Aliyu kawai de ka bari, kai ka ga asibitin? Babu magani bare kuma a samu wani drip da sauran kayan aiki".

"A asibitin?

"Wallahi kuwa, kuma idan kasan mutum ɗaya ne tak yake zuwa".

"Allah ya kyauta".

"Amin, ina tunanin samar da Abba kasan yana da mutane ko ina to na tabbatar idan na sanar da shi komai zai zo da sauƙi ko?

"Bazan ce maka a'a sai dai nayi maka fatan Nasara na bika da addu'ar dacewa".

"Nagode".

"You are always welcome".

"Hmmm".

"Faɗi abinda kaka so ka faɗa straight to the point nasan da magana".

Sosai ƙeya ya fara yi kafin yace.

"Kasan me Yaya Aliyu? Be jira amsar ba ya cigaba, "Jiya ne dana fita na kasa komawa gida shine naga wata yarinya".

A SOYAYYAR MUWhere stories live. Discover now